17/05/2026
Mahaifin wani Mulhidi ya rasu. Abokinsa Musulmi ya je masa gaisuwa, sai ya ce:
Abin da yanayi "Nature" ya karba nasa ne, abin da ya bayar ma nasa ne, komai yana faruwa ne a bisa tsautsayi.
Haƙurinka ba shi da wani amfani, haka, babu wata fa'ida wajen nuna damuwarka. Kar k yi tsammanin komai daga kowa.
Mamaci ko rayayye ba shi d wata ƙima. Ɗan Adam ba wani abu bane face "Sinadarin Kimiya" kamar yadda Mulhidi Stephen y faɗa. Duk gaba ɗayanmu mun zo daga babu ne, kuma zamu koma zuwa ga babu.
Dawwama ta mai ƙarfi ce kaɗai. Da mahaifinka ba rarrauna bane tabbas da bai mutu kamar yadda Birrai suke mutuwa ba.
Yanayi ya jiƙan mahaifinka abokina.
Ka karantawa Mahaifinka wasu shafuka daga cikin littafin "The Origin of Species" na Charles Darwin wataƙila yanayi ya sake halittarsa a karo na biyu..
in akamaka irin wannan ta'aziyar yazakaji