Arewa Student's Orientation Forum Bauchi State Chapter

Arewa Student's Orientation Forum Bauchi State Chapter Domin fadakarwa da ilmintar da dalibai dakuma wayar musu da kai akan karatunsu daga kowanne mataki

19/05/2026

AN FARA UPLOADING ƊIN O'LEVEL RESULTS A PORTAL ƊIN JAMB

O'Level Results Upload: na nufin ɗora sakamakon jarrabawar kammala karatun sakandire (NECO, WAEC, NBAIS, Ko NABTEB) a shafin hukumar JAMB, domin cika sharaɗin samun gurbin karatu, a kowacce daga cikin manyan makarantun ƙasar nan.

• YANZU JAMB TA BUƊE UPLOADING - ME HAKAN YAKE NUFI ?

Hakan yana nufin, dukkannin ɗaliban da s**a yi rijistar JAMB UTME 2026 ba tare da ɗora sakamakon jarrabawarsu ba (Awaiting Result) zasu iya halartar JAMB CBT Centre mafi kusa da su, ɗauke da sakamakon jarrabawar O'Level - tare da Slip ɗin JAMB, domin Uploading.

• NAWA CBT CENTRES SUKE KARƁA DOMIN UPLOADING ƊIN O'LEVEL ?

Mafi yawan Accredited JAMB CBT Centres suna karɓar Naira Dubu Ɗaya (1,000) ne domin yin Uploading.

• SAKAMAKON JARRABAWARMU BAI FITO BA (KO BAMU RUBUTA BA MA) TUKUNNA - TOH YA MATSAYINMU WAJEN YIN UPLOADING ?

Babu wata matsala, kuma wannan ba abin ɗaga hankali bane, zaku iya zuwa CBT Centre ku yi uploading ɗin - a duk lokacin da sakamakonku ya futo, domin ba a rufewa kwata-kwata, har zuwa kammala kakar admission.

• TOH IDAN ZAMU YI UPLOADING, DOLE SAI MUNJE CBT CENTRE ƊIN ?, KO ZAMU IYA TURA RESULTS ƊINMU AYI MANA ?

Dolene ku halarci JAMB CBT Centres a lokacin da za a yi muku uploading, domin a sabon tsarin da hukumar JAMB ta kawo wajibine ɗalibi yayi thumprint (biometric verification) kafin uploading ɗinsa na o'level ya hau.

• SHAWARARMU GAREKU:

Kada kuyi gaggawar yin uploading ɗin, har sai makarantun da kuke nema sun fitar da Cut-Off Mark (tunda ba a rufewa kwata-kwata), saboda a shekarun baya an sha samun matsalolin saukar results ɗin da ɗalibai s**a yi uploading da wurwuri - saboda gyaren-gyaren da JAMB ta dinga bijirowa da su.

Amma yin uploading a lokacin da makarantun da kuke nema s**a fitar da Cut-Off Mark - zai bawa sakamakon o'level ɗinku tsaro (tunda ba za a daɗeba zaku samu Admissions).

FATAN KUN AMFANA DA BAYANAN...

RUBUTAWA: Miftahu Ahmad Panda

WhatsApp - 08121124840

Address

No. B3 Aminu Street Junction, Wunti Street Bauchi
Bauchi
BAUCHISTATE,

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Student's Orientation Forum Bauchi State Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Arewa Student's Orientation Forum Bauchi State Chapter:

Share