05/04/2024
Idan wani yace ma ka rayuwar nan tana da sauki bai faɗa ma ka gaskiya ba, gaskiya ita ce "rayuwa aba ce mai wahala" kai da ka zo duniya don jarrabawa ka san abu mai wahala ka zo yi. Labari mai daɗi shine duk wahalar tan za ka iya ɗauka saboda Allah ba ya ɗorawa bawa abunda ba zai iya ba, daɗi kan daɗi kuma shine matukar ka sha wahalar bisa gaskiya da yiwa Allah ɗa'a za ka samu rabo mai girma bayan ka bar duniya, abun tsoro kuma shine idan ka yi ganganci ka sha wahalar duniya ta fuskar saɓon Allah za ka tarar da wahalar da ta fi wannan bayan ka bar duniya.
Copied