21/02/2026
QUR'ANI: Ubangiji Subhanahu wata'ala yana Bamu labari acikin Suratul Waqi'ah alokacinda idan Mutum ya zo gargara Na Mutuwa Ran shi yazo makoshinsa ana dab da azare shi...
"Toh, idan ya Kasance Mai mutuwar yana daga cikin Makusantan Allah ne watau Salihan Bayi Masu Taqawa"
"Toh, Sai ace dace lale maraba kai kam ka huta babu sauran wuya sai hutu, ga kyakkyawan abinci Na jiranka da Kuma Aljannar Ni'ima duka gareka"
"Kuma amma idan yakasance daga ma'abota dama ne watau mutanen kirki "
"Sai ace Masa aminci ya tabbata agareka, kana daga cikin 'yan aljannah"
Allahu Akbar, daga nan sai mutum yaji wani irin dadi da bai taba jin irinsa ba, aduniya koda ko yafi kowa shan wahala aduniya.
Sai Allah yace:-
"Kuma amma idan Mai mutuwar yakasance daga cikin Masu karyata batun Allah ne (Al-kur'ani) Kuma yakasance daga cikin batattu"
Ko munafikai, ko azzalumai masu zalintar kansu da kansu da sabawa Allah.
"To, Sai a tareshi da wata liyafa ta ruwan zafi, da konuwa daga wutar jahim Mai Zafi"
Domin Ayi masa albishir da azaba da azabtarwa da Zai riska agaba, bayan an zare ranshi.
Subhanallah, awannan lokacin Sai Mutum Yashiga wani irin tashin hankali da bai taba shiga irin sa ba aduniya, ko da ko yafi kowa jindadi.
Sai ace Masa "lalle wannan ita ce gaskiya ta haqiqa"
wanda ake ta baka labarin ta, ake fadamaka ita cewa za ta zo, to amma Sai ka ki, ka kauda Kai, ka ki yarda, ka ki gaskatawa Ka ki aiki.
Ka bi son zuciyar ka da abunda shedan yake Qawatama ka, har Sai da Mutuwa gata ta zo gabanka ga shi ta riske ka?
Kaicon ka!
Allah yace"
Saboda haka (kai musulmi) Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mai karamci.
Suratul Waqi'ah.
Watau shi yasa aka ce duk mai Karanta suratul Waqi'ah to Zai samu Arziki Duniya Da Lahira, ma'ana ita kanta Karanta suratul da lura da ma'anoninta Zai sa ka manta da Duniya ka fuskanci Lahira, Kuma Ka kara Taqawa (storon Allah Arayuwar ka ta Duniya).
Surar da take biye da ita watau suratul Hadid, suna da alaka da Juna.
musamman fadin Allahu (SWT) inda yake cewa" Dukkan halittun da suke a sammai da Kasa Su tsarkake sunan Ubangiji Allah"...
Shi yasa malamai s**a ce babu abinda yakai ambaton Allah (zikiri) lada.
Annabi SAW yace Daga cikin kalmominda Allah yake So, shine mutum yace " Subhanallahi, Wabihamdihi, Subhanallahil azeem, la ilaha illah, lahaula wala quwwata illa billah.
WALLAHU TA'ALA search
🤲Ya Allah muna Rokonka ka Bamu daga Falalarka aduniya da Kuma lahira, Kasa mu gama da Duniya lafiya, ibadunmu da Addu'o'in Allah ka karbamana, iyayenmu Da Malamanmu Da zuri'ar mu Baki daya Kasa Aljannace Makomarmu🤲
✍️ Yunusa Magaji Gombe