Fassarar Al-qur'ani da Hausa

Fassarar Al-qur'ani da Hausa Fassarar Al-Qur'ani Da Hausa Bisa fahimtar Sahabban Annabi Muhammad SAW.

Ga Wani Sirrin Salatin Annabi (s.a.w) ko za ka gwada?''''Annabi S.a.w yace wanda duk yamini Salati (100) Bayan Sallar as...
08/05/2026

Ga Wani Sirrin Salatin Annabi (s.a.w) ko za ka gwada?
'
'
'
'
Annabi S.a.w yace wanda duk yamini Salati (100) Bayan Sallar asuba kafin yayi magana, Allah Zai biyamasa bukata Dari (100) Zai gaggauta Masa talatin (30) aduniya, Zai ajiye Masa saba'in (70) Sai Ranar tashin kiyama.

haka a bayan Sallar magrib ma akeyi.

Sai Sahabbai s**a ce to ya ya ake Maka salatin a Nan?

Sai Annabi S.a.w ya Karanta ayar "Innallaha Wa mala'ikatahu yusalluna Alan nabiy yaa ayyu hallazina amanu Sallu alaihi Wa sallimu taslima"

Sai yace ga abinda za Ku Karanta " ALLAHUMMA SALLI ALAIHI" Sau (100)

Amma Sai Mutum ya Karanta ayar tukunna kafin ya dora da Cewa "Allahumma Salli alaihi" Sau (100) Insha Allahu bukatunsa za su biya Kuma za a ajiye Masa a inda yafi ko ina daraja ranar tashin kiyama.

Ana yin Salatin A duk bayan sallar asuba da magrib kafin kayi magana.

Wallahu Ta'ala A'alam.

Allah yasa mudace, ya Allah kasa Aljannace Makomarmu da mu da iyayenmu Da Malamanmu Da iyalanmu da 'yan uwanmu da zuri'ar mu Baki daya ya Allah 🤲

✍️ Yunusa Magaji (Gombe)

Al-kur'ani Dadi, ya Allah Kasa Al-kur'ani ya zamo hujja ne garemu ba akan mu ba
11/04/2026

Al-kur'ani Dadi, ya Allah Kasa Al-kur'ani ya zamo hujja ne garemu ba akan mu ba

JANHANKALI: ka yi dubi  izuwaga halittun Allah Mai tsarki da daukaka musamman halittar Mutum Mai cike da abin Mamaki, Wa...
05/04/2026

JANHANKALI: ka yi dubi izuwaga halittun Allah Mai tsarki da daukaka musamman halittar Mutum Mai cike da abin Mamaki, Wadda aka soma ta da gudan jini, har ta Kai abinda Allah ya so ta Kai, ta zamo cikakkiyar halitta Mai karfi da hankali, da ga bisani Kuma, Allah zai Sa ta koma turbaya, kafin a tashe ta domin ayi Mata Hisabi.

Fadin Allahu SWT "Lalle Kuma Zuwaga Ubangijin ka makoma take"

Allahu Akbar, Yan uwa Ya kamata ace muna fadakuwa da abinda ake bamu labarinshi na daga Al-kur'ani Mai girma, Kowa ya gyara niyyarsa ya kuma gyara alakarsa da Allah, domin akwai mutuwa gaba garemu Kowa sai mutu Kuma Kowa Sai anyi masa hisabi.

surah Al-alaq aya ta Takwas (8).

Allah kasa muyi kyakkyawan Karshe, Allah ka Gafartamana zunuban mu ka kankare mana Laifukanmu Kasa Aljannace Makomarmu da mu da iyayenmu Da Malamanmu Da zuri'ar mu Baki daya 🤲

✍️ Yunusa Magaji (Gombe)

QUR'ANI: Ubangiji Subhanahu wata'ala yana Bamu labari acikin Suratul Waqi'ah alokacinda idan Mutum ya zo gargara Na Mutu...
21/02/2026

QUR'ANI: Ubangiji Subhanahu wata'ala yana Bamu labari acikin Suratul Waqi'ah alokacinda idan Mutum ya zo gargara Na Mutuwa Ran shi yazo makoshinsa ana dab da azare shi...

"Toh, idan ya Kasance Mai mutuwar yana daga cikin Makusantan Allah ne watau Salihan Bayi Masu Taqawa"

"Toh, Sai ace dace lale maraba kai kam ka huta babu sauran wuya sai hutu, ga kyakkyawan abinci Na jiranka da Kuma Aljannar Ni'ima duka gareka"

"Kuma amma idan yakasance daga ma'abota dama ne watau mutanen kirki "

"Sai ace Masa aminci ya tabbata agareka, kana daga cikin 'yan aljannah"

Allahu Akbar, daga nan sai mutum yaji wani irin dadi da bai taba jin irinsa ba, aduniya koda ko yafi kowa shan wahala aduniya.

Sai Allah yace:-

"Kuma amma idan Mai mutuwar yakasance daga cikin Masu karyata batun Allah ne (Al-kur'ani) Kuma yakasance daga cikin batattu"

Ko munafikai, ko azzalumai masu zalintar kansu da kansu da sabawa Allah.

"To, Sai a tareshi da wata liyafa ta ruwan zafi, da konuwa daga wutar jahim Mai Zafi"

Domin Ayi masa albishir da azaba da azabtarwa da Zai riska agaba, bayan an zare ranshi.

Subhanallah, awannan lokacin Sai Mutum Yashiga wani irin tashin hankali da bai taba shiga irin sa ba aduniya, ko da ko yafi kowa jindadi.

Sai ace Masa "lalle wannan ita ce gaskiya ta haqiqa"

wanda ake ta baka labarin ta, ake fadamaka ita cewa za ta zo, to amma Sai ka ki, ka kauda Kai, ka ki yarda, ka ki gaskatawa Ka ki aiki.

Ka bi son zuciyar ka da abunda shedan yake Qawatama ka, har Sai da Mutuwa gata ta zo gabanka ga shi ta riske ka?

Kaicon ka!

Allah yace"
Saboda haka (kai musulmi) Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mai karamci.

Suratul Waqi'ah.

Watau shi yasa aka ce duk mai Karanta suratul Waqi'ah to Zai samu Arziki Duniya Da Lahira, ma'ana ita kanta Karanta suratul da lura da ma'anoninta Zai sa ka manta da Duniya ka fuskanci Lahira, Kuma Ka kara Taqawa (storon Allah Arayuwar ka ta Duniya).

Surar da take biye da ita watau suratul Hadid, suna da alaka da Juna.

musamman fadin Allahu (SWT) inda yake cewa" Dukkan halittun da suke a sammai da Kasa Su tsarkake sunan Ubangiji Allah"...

Shi yasa malamai s**a ce babu abinda yakai ambaton Allah (zikiri) lada.

Annabi SAW yace Daga cikin kalmominda Allah yake So, shine mutum yace " Subhanallahi, Wabihamdihi, Subhanallahil azeem, la ilaha illah, lahaula wala quwwata illa billah.

WALLAHU TA'ALA search

🤲Ya Allah muna Rokonka ka Bamu daga Falalarka aduniya da Kuma lahira, Kasa mu gama da Duniya lafiya, ibadunmu da Addu'o'in Allah ka karbamana, iyayenmu Da Malamanmu Da zuri'ar mu Baki daya Kasa Aljannace Makomarmu🤲

✍️ Yunusa Magaji Gombe

🤲Addu'ar da akeyi idan Mai Azumi ya zo yin Buda Baki🤲Za Kace " (Godiya ta Tabbata ga Allah) Kishin Ruwa ya tafi, an yayy...
18/02/2026

🤲Addu'ar da akeyi idan Mai Azumi ya zo yin Buda Baki🤲

Za Kace " (Godiya ta Tabbata ga Allah) Kishin Ruwa ya tafi, an yayyafawa jijiyoyi Ruwa, kuma lada ya Tabbata in Allah ya so"

Ma'ana ina buri da Kuma fata wan nan azumi da nayi Ubangiji Allah ya karbamini ya bani ladansa.

Sai Ka Ce"
Ya Allah Ina Rokonka da Rahamarka da ta yalwaci komai da Ka gafartamini "

Ba lefi Idan kana da wasu bukatun Ka Roki Allah ya biya maka.

Sa an nan an fi so afara Buda Baki da Dibino ko wani abu na Dan ice.

Wallahu Ta'ala A'alam.

✍️ Yunusa Magaji Gombe

Suraul Munafiqun/ Qissar Musa Samiri Allah yace "Idan munafukai S**a Zo maka, Sai S**e mun Shaida Kai Manzon Allah ne (A...
09/12/2025

Suraul Munafiqun/ Qissar Musa Samiri

Allah yace "Idan munafukai S**a Zo maka, Sai S**e mun Shaida Kai Manzon Allah ne (Amma a zuciyar su Karya Suke)

Kuma Allah yasani cewa Kai Manzonsa Ne (ya Muhammad S.a.w)

Kuma Allah yasani lalle munafiki haqiqa Makarkaci ne"

SHI MUSA SAMIRI Uwar shi ta Sami cikinsa Ne a layi, Sai Mutanen Garinta S**a Koreta Ta Shiga Dashi acan Ta haifi Musa Samiri, Sai Ta Mutu ga Kuma Jariri shi kadai

Sai Allah Ya Aiko Mala'ika jibril ya Dauki Yaron.

Saboda jarrabawa Mala'ika jibril shi ya reni Musa Samiri Duk da cewa Munafiki ne.

Idan Annabi Musa da Haruna S**ayi wa'azi, Sai Musa Samiri yazo ya ringa Rusa Abinda S**a Gina Azukatan Banu Isra'il.

Ya Gunkin saniya yace Itace Abin Bauta Allah.

Ya kera saniyar Ne Daga Kasar Da Godiyar Mala'ika jibril (A.s) ta Taka, Alokacin da fir'auna ya biyo Annabi Musa (A.s) Zai kashe shi

Toh, Musa Samiri yaga godiyar Mala'ika jibril ta Wuce Kan Ruwan Teku, duk inda godiyar ta Taka Sai yaga koren ciyawa ya fito agun

To anan ya fahimci Akwai Rayuwa a inda godiyar Mala'ika jibril take Taka, Sai Ya Kwashi Kasar Wajen ya boye.

To a Sanda Yake kera Dan marakin Nan, Sai Ya gwama kasar wajen da gwala gwalai da ya Harhada agunsu don kera Dan maraqi.

Da ya kera Sai ga saniyar Tana kuka irin Na Sauran shanu Masu Rai.

Da S**a ga haka shi kenan Sai s**a Ce Lalle Tunda wan Nan mutumin Ya kera wan Nan, to, sa Zata Iya zamowa Saniyar ita ce Allah, shikena Nan sai S**a Bata Suna Bautamata

Annabi Musa (A.s) ya sha Wahala dasu matuqa akan Bautar Dan Maraki, Shida Dan uwansa Harun (A.s)

Atakaice shi Musa Samiri munafiki ne, Yana Rusa Aikin annabawan Allah ne, Kuma Yana Hana Al-ummar Allah Fahimtar gaskiya

shi Asalin Munafiki, shine Zindiqi/Makarkaci, Wanda asalin su, Su masu Bautar Wuta ne, suna Yiwa Allah Shirka, Kuma suna Buga Ganguna Suna Rawa da sashin Junan su.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Ya Allah ka jaddada Imani Azukatan mu.

ka Rabamuda munafirci da aikin Riya, Kasa Aljannace Makomarmu da iyayenmu Baki daya

CETON MA AIKI S.A.W: Wata rana Aranar Tashin Alqiyama Tsanani Yayi Tsanani Ana Bukatar Ceto Kaga Da Da Ubansa, Miji Da M...
03/09/2025

CETON MA AIKI S.A.W: Wata rana Aranar Tashin Alqiyama Tsanani Yayi Tsanani Ana Bukatar Ceto Kaga Da Da Ubansa, Miji Da Matarsa, Suna Gudun Junansu, Hatta Manzanni Da Annabawan Allah Babu Abinda suke Cewa Sai Rabbi Sallim-Sallim

Kwanyar Kai Tana Tafarfasa Saboda Tsananin zafin Rana, Mutane Suna Magagi kamar Wanda S**a sha abun Maye Amma Basu sha kome ba Tsananin Azabar Allah ce Ta maida su Haka.

Sai Mutane Suje gun Annabi Nuhu (A.s) S**e Ya Nuhu Ka Rokamana Allah Ceto, Yace Ba Ceto Inada Laifi awajen Allah, nayi Addu'ar Dhufana Duniya ta Halaka, Sai Dai kuje Gun Adam (A.s).

Sai Muje Gun Adam (A.s) Muce Ya Adam Ka Rokamana Allah Ceto, Se Yace Ba Ceto Inada Laifi awajen Allah Naci Dan Bishiyan Da Allah Ya hanani Naci, Sede kuje Gun Musa (A.s)

Sai Muje Gun Annabi Musa (A.s) Muce Ya Musa ka karokamana Allah Ceto, Sai Annabi Musa yace Ba Ceto Inada Laifi awajen Allah Na Kashe wani Bakibde, Se de Kuje Gun Isah (A.s).

Sai Muje Gun Annabi Isa (A.s) Muce Ya Isah Ka Rokamana Allah Ceto, Sai Yace Inada Babban Laifi Ni da aka yimini Bauta Aduniya, Wannan Aiki Sai Dai Kuje Wajen Muhammadu (SAW)

Sai Muje Gun Annabi Muhammadu SAW, Muce Ya Rasulullahi Ka Rokamana Allah Ceto, Sai Yace Ni ne Da Ita, Ni ne Da Ita, ko zo Zan Baku S.A.W

Sai Annabi Muhammadu SAW yaje Gun Allah yayi Sujjada Yata Yabo da Kirariwa Allahu SWT, Sai Ubangijin Al-arshi Yace Mai Nene? Sai Annabi Muhammadu SAW yace Ya Allah Nayi Alkawari Aduniya Duk Mai Kaunarka da Kuma Mai Biyayya agareni Zan Cece Sa, Sai Allah Yace Jika Ambaka S.A.W

Sai Manzon Allah Ya Zo Ya cece Duk Nashi Da Masoyinsa Izuwa Aljanna S.A.W

Wannan shine Matsayin Manzon Allah kenan Ceto Na Farko Allah ya kalli bayi ayi musu hisabi Hatta Annabawa da Manzannin Suna Cin Albarkacin Annabi Muhammadu S.A.W.

Ceto Na Biyu Annabi Muhammadu SAW ya ceci Al-ummarsa Duk Wanda Yayi Imani da Allah Da Annabi Muhammadu SAW.

Kafin Kuma Ceton Sauran Annabawa da mursalai da Shahidai Da Sauran Manyan Bayin Allah ya biyo Baya.

Kuma Wanda Allah Ya Kaddara zasu iya Cetonsa Kadai Za su Ceta, Ba Kowa da Kowa ba, Kamar Ceton Manzon Allah SAW .

ALLAHU AKBAR
Ya Allah Ka Samu Aceton Annabi Muhammadu SAW 🤲

Wallahu a'alam.

✍️Naku
Yunusa Magaji Bala Gombe

KISSA: Wata Rana Mala'ika Jibril Yazo Ya Samu Manzon Allah SAW Yace: Kana So Ka Rayu Manzo Wanda yake Cikin Daula Jin Da...
01/09/2025

KISSA: Wata Rana Mala'ika Jibril Yazo Ya Samu Manzon Allah SAW Yace: Kana So Ka Rayu Manzo Wanda yake Cikin Daula Jin Daɗi Da Dukiya Ko Kuwa, Ka Rayu Yau Akwai Gobe BaBu? Sai Manzon Allah SAW Yace: A'a Nafison Na Rayu Yau Inadashi Sai Nagodewa Allah Gobe Kuma BaBu Sai Na Tuna Allah Nakoma Gareshi (S.A.W)

Annabi Muhammadu Kenan, Yafi Kowa Matsayi Da kankan dakai Hatta Ga Annabawa Da Manzannin Allah (S.A.W).

Watara Manzon Allah SAW Bayan Gari yawaye Sai yacewa: Sahabbansa Jiya Ina Sallah da Dare Sai Wani Ifiritu Minal Jinni ya zo mini, Ma'ana Shedanin Aljani Yazo Don ya Bata mini Sallah Sai Allah ya Taimakeni Na Damke shi da hannuna Haka, Naso Na Daure A Nan Masallaci Hatta Yaran Garin Madina Se Sun ganshi, Sai Na Tuna Da Addu'ar 'Dan uwana Annabi Sulaiman (A.s) Sai Na Sake shi Ya Tafi.

ALLAHU AKBAR
Tawabu'un Manzon Allah SAW kenan Babu Hassada ko Gilli Azuciyar Sa (S.A.W)

🤲Ya Allah kabamu Albarkacin Sa 🤲

Kasadamu Da cetonsa Aranar Gobe Alqiyama.

Wallahu a'alam.

✍️Naku
Yunusa Magaji Bala Gombe

ABUBUWA GUDA (11) DA IDAN KAYI RANAR JUMMA'A ALLAH ZAI GAFARTAMAKAManzon Allah SAW Ya lissafa Wasu Abubuwa da Idan Mutum...
29/08/2025

ABUBUWA GUDA (11) DA IDAN KAYI RANAR JUMMA'A ALLAH ZAI GAFARTAMAKA

Manzon Allah SAW Ya lissafa Wasu Abubuwa da Idan Mutum yayi Su a Ranar Jumma'a Za'a Gafartama Sa Zunuban Sa, Daga Jumma'a zuwa Wata Jumma'a.
*1- Kayi Wanka, 2- Ka Sanya kaya me Kyau, 3- Kayi Tsarki, 4- Ka goge Baki, 5- ka Shafa Mai, 6- ka fesa Turare, 7- ka fito Masallaci a sa'ar farko, 8- ka tafi a naste, 9- kada Ka bubbuge kafadun mutane Don zaka Shiga Masallaci, 10- idan ka Shiga Masallaci Kayi Raka'o'i Guda Biyu, 11- ka zauna ka Saurari Khudubar liman Ba Tareda Kayi magana ba*

Manzon Allah SAW Yace " Akwai wata Sa'a Ranar Jumma'ah Da idan Ka Roki Allah Alla Zai Amsamaka"

Wasu malamai S**a ce: A lokacin Khudubar Jumma'ah sa'ar Take

Wasu S**a ce: Bayan Sallar La'asar sa'ar Take

Duk Dai Ko wani Lokacine ma Ana So duk bayan Sa'a kayi addu'a

Domin ARanar Jumma'ah dai Sa'ar take, Sai Ka Raye Ranar da Addu'o'in ka baki daya zaka dace

Jumma'ah Idi ce Ta Musulmai Baki daya Yana Daga Cikin Ladduban Ranar Jumma'ah

Ana So Mutum Ya Yawaita Salatin Manzon Allah SAW

Ana So Mutum Ya Karanta Suratul Lahfi.

Ana So Mutum Ya Yawaita Zikiri (SUBHANALLAHI WALHAMDULILLAH, LA'ILAHA ILLAH ALLAHU AKBAR)

Ana So Mutum Ya Sada Zumunci, Ziyarce Ziyarce Na Yan Uwa da Abokai

Ana So Mutum Ya Yawaita Sallama A Tsakankanin Mutane

Ana So Mutum ya yi Sadaka Ko Kyauta.

Ana So Mutum Ya aikata Alkairi Ya Nisanci Sharri
Bakinka ya furta Gaskiya, Sai Ambaton Allah,

Banda Zagi, Zalinci, Karya, Alfasha, Dasauransu.

WALLAHU A'ALAM.

✍️Naku
Yunusa Magaji Bala Gombe

TARIHIN ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)Kashi Na Takwas (8)Bayan Gwagwarmayar Annabi SAW Da Sahabbai Don Ganin Musulunci Ya Kafu...
25/08/2025

TARIHIN ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)
Kashi Na Takwas (8)

Bayan Gwagwarmayar Annabi SAW Da Sahabbai Don Ganin Musulunci Ya Kafu Ya Tsaya Da Kafafuwansa

Hakika Manzon Allah Ya Samu Nasarar yin Hakan, domin Kuwa Musulunci Sai da ya Shiga Ko ina da Ina acikin Nahiyar Duniya Baki Daya Bayan Wafatin Annabi SAW.

Manzon Allah SAW Ya Rasu Yana da Shekaru sittin da Uku (63).

Kuma an Bunne shi ne Agarin madina, wanda itace Garin da yayi hijira zuwa gareta daga Makka, kuma wanda a yanzu masu Aikin Hajji suke ziyartan ta Don Ziyaran kabarin Annabi SAW.

Kuma 'ya'yan Manzon Allah SAW guda bakwai ne (7) hudu daga ciki mata ne, Sune Fatima, Zainab,RuQayya,Ummu kulsum.

Da Kuma 'yaya Uku Maza, Sune AlQasim, Abdullahi, Ibrahim.

Duka 'ya'yan Manzon Allah SAW Wadda ta haifesu itace Ummuna Khadija (R.a) Sai De Ibrahim shi kadai, wanda Mahaifiyar sa itace Mariyatul Qibtiyya asalinta 'yar Misira ne.

Dukkan 'ya'yan Manzon Allah SAW Sun Rasu Suna Kanana, kuma Mun kawo muku Tarihin 'ya'yan sa da Matan sa duka adarasin Mu Na Baya, S.A.W.

Manzon Allah SAW yakasance Mai Gaskiya ne acikin Maganar sa, Kuma Adali, Mai Amana ne Shi, yana Ciyar da Fakirai, da Talakawa, da Marayu, yakasance Hatta akan akan Dabbobi shi Mai Tausayi ne, S.A.W.

Wan nan Shine Tarihin Annabi SAW Atakaice.

WALLAHU A'ALAM.

Akwai yakukuwansa wanda muka ta kawo muku su adarasi darasi Na Baya, kuma zamucigaba da kawo muku wasu yakukuwan nasa SAW, Da Rayuwar Sa Daki Daki Adarasi Masu Zuwa, Insha Allah.

Adarasin Mu na Gaba Zamu kawo muku Tarihin Annabi Nuhu (A.s).

🤲Ya Allah Kasa Muyi koyi da Dabi'un Sa, Ya Allah Kasa Mu kaunacesa Fiyeda kanmu da Dukikoyin Mu, ya Allah kasamu acetonsa S.A.W🤲

✍️NAKU
YUNUSA MAGAJI BALA GOMBE

Address

Jekadafari Layin Mele Street
Gombe Aba

Telephone

+2348168311092

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fassarar Al-qur'ani da Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Fassarar Al-qur'ani da Hausa:

Share