10/03/2021
[3/10, 4:51 PM] Abubakar Ango: Assalamu alaikum (Bayani akan muhimmancin Ranar 27th na wannan Watan da muke Ciki Wanda Shiek Mallam Umar Sanda ya Rubuta on the 27th March 1986)
FARIN CIKIN ZAGAYOWAR RANAR MANZANCIN ANNABINMU SALLALLAHU ALAIHI WA ALA ALIHI WA SALLAMA .
Asalin Al amarin dai wato asalin muhimmancin "Saba'a wa ishirin" ga Rajab , shine Ranar Litinin , 27th ga Wannan wata Rajab, a Shekara ta 610 AD Bayan hahuwar Annabi Isa bn Maryam (Alaihis Salam) a wannan Rana ce Babban Mala'ika Jibrilu, alaihisSalam, ya sauko duniyar nan da SAKO NA FARKO daga Mahaliccinmu Sarki Allah Tabaraka wa Ta'ala, zuwa ga fiyayyen Halittarsa, Shugaban Annabawa, Sallallahu Alaihi wa Sallama wa Alaihim. wato a wannan Rana ce, 27 ga Wannan wata na Rajab, aka tabbatar wa Shugaban halitta, Sayyidina Muhammadur-Rasulillahi, Sallallahu Alaihi wa Sallama da cewa shine Cikamakin Annabawa Wanda sakonsa ya game kowace kabila, mutane da Aljannu na wannan duniya, da Mala'iku da sauran halitta na can wadansu duniyoyin dake can-can Sama. A wannan Rana ce Allah ya cika alkawarinsa da Ya yi na cewa zai bayyanar da Wannan Annabi don ya Zama Mabuwayiyar Rahama ga halitta na kasa da na Sammai duka. Annabin da Babu wani Annabi bayansa - Sallallahu Alaihi wa Sallama. Wannan Rana 27 ga Watan Rajab, Rana ce Mai Girman ga Mala'iku da mutane musulmi da Aljannu musulmi..
IBADA DAREN MI'IRAJ DA RANARSA:
Anaso a azumci wannan rana, a sada zumunci. A Kara kyautata wa iyali da makwabta. Mata su Kara biyayya ga mazajensu. A gaida Malaman Sunna. A Kara biyayya ga magabata. Agaida marasa lafiya na gida dana asibiti, akai musu abin marmari.Ana son agajin mabukata da marasa galihu a wannan Rana mai albarka. A nisanci aikin banza da shashanci,da duk aikin sabo da zunubi ,da nisantar duk abin assha.Anaso a karanta Alkur'ani Kamar Suratul Isra'i da Suratul Alaqi (ikra'a) da Wannajami, da Salati ga Annabi musanman a wannan Rana ta farin ciki.
An ruwaito Hadisi daga Annabi Yace, "Ya kyautu Kan kowane jama'arka gida su yanka rago a Watan Rajab, su Kuma Yi Layya a Watan Zul Hajji."
Page 1 of 2
[3/10, 4:56 PM] Abubakar Ango: SALLAR DAREN MI'IRAJI
Ana so Ayi SALATI LAILTIL MI'IRAJI Wanda Annabi Yace Ayi. Ga sifarta: Raka'a goma Sha biyu, Fatiha da surar da kake so, Sallama ko wace Raka'a biyu. In ka gama ka karanta Albaqiyatul Swalihatu 100, Istigfari 100, Salati Alan Nabiyyi 100 . Sai kayi addu'a don kanka da Malamanka da ' ya' yanka da matanka, da ' yan uwanka da makwabtanka da jama' ar musulmi duka sa annan kasa baki daya . Kayi kyakkyawan addu'a ga Shugaban kasa da mataimakansa, sarakuna da sauransu wato ka roki Allah Ta ala ya Kara salaha da adalci da karimci ga Shugaban kasa da mataimakansa. Ka daure kayi azumin wannan Rana Mai albarka, watau 27 ga Rajab.
ALHAMDULILLAHI , THIS YEAR 27TH RAJAB ZAI K**A ON THURSDAY 11/3/2021 Saboda haka Sallar Daren MI'IRAJI za Ayi tane ranar Wednesday at night bayan Isha' I before Dawn sai atashi da azumin Yaumil Risalati on Thursday . Insha Allah .
Anaso Ayi Sallar nafila 4 rak'as a ranar MI'IRAJI ) Yaumur Risalati. In each rak' a you recite Fatiha once, falaqi 1, Nasi 1, Suratul Qadri 3x, and Suratul Ikhlas 50. Bayan kayi Sallama kayi a lot of Salaat alan Nabiyy da addu'o'in masu yawa. ALHAMDU LILLAHI.