13/06/2026
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Muna miƙa saƙon taya murna ga malamammu masu daraja na Mai Lamai Academy Islamiyyah:
🎓 Malam Muhammad Saminu Hussaini wanda ya kammala karatun digiri na farko a fannin Computer Science.
🎓 Malama Khadija Alhassan Abdullahi wadda ta kammala karatun digiri na farko a fannin Microbiology.
Muna taya ku murna bisa wannan babban nasara. Muna roƙon Allah (SWT) Ya sanya ilimin da kuka samu ya zama mai amfani gare ku da al'umma baki ɗaya. Allah Ya ƙara muku basira da hikima, Ya buɗe muku ƙofofin alkhairi da arziki mai albarka, Ya ba ku nasara a dukkan al'amuranku na gaba.
Allah Ya sanya wannan nasara ta zama mafarin ɗaukaka da cigaba a rayuwarku. Ameen Ya Rabbal-'Alamin. 🤲
🌹 Taya murna da kammala karatun First Degree. 🌹
Daga: Mai Lamai Academy Islamiyyah.