16/01/2023
*SIYASAR ƘASATA!*
*Dararrafe Writers Association*
'Duk abin da mutum ya shuka shi zai girba.' Na jima ina jin wannan azancin maganar, amma ban taɓa gaskata hakan ba sai da Ubangiji Ya tarfa wa garinmu nono, ta hanyar kawar da duhun zalincin da aka gadar wa wannan al'umma tamu. Wanda hakan ya yi sanadiyar ruruwar wutar gaba da faɗace-faɗace tsakanin al'ummar da ta kafu bisa kyakkyawan tarihi da fahimtar juna, tamkar dai salon maganar nan da ke cewa, 'tsintsiya maɗaurinki ɗaya.'
Na numfasa tare da sakin ajiyar zuciya, duk yadda na so na hana zuciyata hakaito mini ɓarnar da na tafka a baya, abin ya gagari kundila. Babu shakka sharri ɗan aike ne, matuƙar ka aika shi, to kada ka rufe ƙofa zai dawo gare ka. Domin duk nisan gari akwai na gabansa.
***
"Nakaka ikon Allah! Nakaka gagara badau, ka gagari duk wani shege. Ka san fa zaɓe saura 'yan makonni, babu shakka na yaba maka da kai da yaranka, aikinku ya yi kyau matuƙa. Duk inda abokan adawarmu s**a je ba a kwashewa ta arziki, sai an yi hargitsin da ya haifar da zubar kayuwan mutane. To sai dai ka san mutane fa har yanzu suna nuna ƙauna gare su, don haka nake so mu sake wata ɗamarar, yanzu ne za a fara yaƙin. Ranar zaɓen nan akwai akwatunan da nake a sato su, idan ba za su satu ba, to a hargitsa wajen a ƙona su."
Sautin muryar shugaban jam'iyya mai mulki ke nan watau Hon. Halliru Isa, lokacin da yake tsara mini irin ta'addancin da za mu aikata don biyan buƙatarsu.
Dariya na saki tamkar mahaukaci tare da cewa, "An gama oga! Sai dai fa har yanzu ba mu ga sauyi ba, yarana ƙorafi suke yi mini kayan aiki ya yi kaɗan."
"Haba Nakaka kada damu, ku kwantar da hankalinku indai kayan aiki ne a wannan karon ba ku da matsala. Mun yi magana da mai girma Gwamna, ya ce duk abin da kuke buƙata ku sanar da ni kawai. Yanzu ma fara riƙe wannan." Ya sa hannu cikin aljihun babbar rigarsa ya zaro dami guda na 'yan dubu ɗai-ɗai ya miƙo mini.
Zaɓe ya rage saura mako biyu, mahaifina yana kwance babu lafiya tsawon shekaru bakwai, yana fama da ciwon siga da hawan jini. An yi magani har an gaji, babban yayanmu ya nemi taimakon shugaban gundumar tamu game da rashin lafiyar mahaifin namu, amma bai saurare shi ba kasancewar shi yayan nawa da mahaifina ba sa goyon bayan gwamnati mai ci. Ni kuma harkar gabana nake ban cika zuwa gida ba bare na san wainar da ake toyawa, ashe jikin ya yi tsanani matuƙa.
Zaɓe ya rage saura kwana biyu, mahaifina ya sa aka kira ni, yana kwance da kyar sautin muryarsa yake fita, ya fara mini wasiyya k**ar haka, "Usman don Allah ka bar wannan harka ta ƙuruciya, girma ya fara k**a ka. Ba zan hana ka yin siyasa ba, domin ita siyasa halak ce kuma hanya ce da mutum zai amfanar da kansa ya amfanar da al'ummarsa. Sai dai abin kaico shi ne yadda aka yi rashin dace, kake bin gurɓatacciyar siyasa. Wacce ba za ta amfana maka komai ba, sai dai ta kai ka ga kogin nadama. Siyasa ba gaba ba ce, ba kuma hanya ba ce ta ko a mutu ko a yi rai ba. Shi mulki a hannun Allah yake, yana bayar da shi ga wanda ya so, haka nan Ya karɓe daga wajen wanda Ya so. Alfarmar da za ka yi mini ke nan ka bar duk wannan shashancin, ka yi koyi da 'yan uwanka. Allah Ya yi muku albarka gabaɗaya."
Tari ne ya sarƙe shi, alatilas ya gimtse maganar. Tarin kuma ya ci gaba da tsananta, nan dai na bar shi tare babban yayanmu na fice abina. Ko a jikina wai an yakushi kakkausa.
Ranar da za a fita zaɓe da Asubar fari, wayata ta shiga ruri, na ɗauka na ga lambar yayanmu ce, karawa na yi a kunne bayan na latsa maɓallin amsa kira, kafin na yi magana ya ce, "Usman mai afkuwa ta afku, Malam wa'adi ya yi. Idan za ka hankaltu sai ka hankaltu, muna jiran ka ka zo a yi masa sutura." Ya kashe wayar.
Nan take na kira Hon. Halliru na faɗa masa, cewa ya yi, "Allah Ya jiƙan sa, to ya ya maganar aikin da muka ba ka? Ina fatan dai za ka fito ko?"
"E, amma zan fara zuwa gida a yi jana'izar mahaifina tukunna."
"Ban amince ba, ka san fa yadda harkar nan take, ko yaya aka samu akasi lissafi ne zai canja, kawai ka yi masa addu'a, ba sai ka je ba."
Ai kuwa hakan aka yi, wannan gurguwar shawara ita na hau kai na yi ɗerere. Na fita na tara yarana, na rarraba su zuwa duk wata rumfar zaɓe da na san gwamnati mai ci ba ta da goyon baya a wajen, na yi musu huɗubar cewa da zarar sun ga alamun wankin hula zai kai mu dare, to su aikata ɗayan biyun nan, ko dai su tayar da rikici su tarwatsa masu zaɓen, ko kuma su sace akwatin zaɓen. Ni kuma na riƙe wata babbar mazaɓa, wacce ta kasance mafi maiƙo, watau tana da yawan al'umma. Ita mazaɓar indai ɗan takara ya samu ƙuri'u sama da rabi, to ana sa rai shi zai lashe zaɓen. Ba jimawa jami'an zaɓe da ma'aikatan tsaro s**a hallara a dukkan rumfunan kaɗa ƙuri'a, aka fara zaɓe lafiya ƙalau.
Sau uku babban yayanmu yana yi mini waya ina ce masa gani nan tafe, daga ƙarshe dai ya gaji ya daina.
Rana ta take sosai, alamomin faɗuwar gwamnati mai ci sun bayyana ƙarara, domin al'ummar gari sun fara murna da farinciki, wasu na faɗin ai In Sha Allah bana wahalar mu ta yanke, sauyi ya tabbata. Nan take wayata ta fara ruri, shugaban jam'iyya ne ya kira ni, cikin kakkausan harshe ya rufe ni da faɗa, yana cewa, wane irin mummunan labari suke ji, lallai na yi abin da ya dace cikin mintuna goma. Nan da nan na shiga kiran wayoyin yarana, cikin mutum goma da na kira biyu na samu, su ka shaida mini cewa ai matasa sun kasa sun tsare, duk wanda ya yi yunƙurin kawo cikas, riƙe shi suke yi su kai shi wani waje su ɗaure.
Ina tsaye ina tunanin yadda zan ɓullo wa lamarin, kwatsam sai ga babban yarona yana haki, ban tsaya sauraren mai zai faɗa mini ba, na kutsa kai cikin tashar zaɓen da nake sa-ido wacce ta kasance makarantar firamare, cikin ƙarfin hali na suri akwatuna biyu maƙare da ƙuri'u, na ara ana kare, sai ihun tara-tara. Daidai fita daga ƙofar makarantar wasu matasa s**a yo kaina, guda daga cikinsu ya ya sauke mini wani katako a kai, ban san lokacin da na zube ƙasa ba. Ban sake sanin a wace duniya nake ba sai farkawa na yi da tsintar kaina a asibiti. Duk jikina ciwuka ne na duka da mak**ai, bayan na ɗan samu sauƙi aka sauya mini muhalli, daga asibiti zuwa ofishin 'yansanda. Aka tuhume ni da laifin tayar da rikici da satar akwanin zaɓe. Dangina ba wanda ya zo, da ma ban sa rai da zuwansu ba. Alƙali ya yanke mini hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru ashirin da biyar.
Babu shakka hakkin mahaifina ne yake bibiya ta. Ya Allah ka jiƙan malam, ni kuma ka yafe mini. Ya Ubangiji ka ƙara shiryar da mu tafarki madaidaici. Ya mai ba da mulki ga wanda ya so, ka zaɓa mana shugaba mai adalci da tausayi, amin summa amin.
Ƙarshe!