15/08/2023
*DAGA CIKIN FALALAR ZIKIRI*
Daga Abu Hurairah (Allah Ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:
*" Wallahi ! In furta: (zikirin ) SUBHANALLAHI, WALHAMDULILLAH, WA LAA ILAAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR; shi ya fi soyuwa a gare ni sama da abinda rana take ɓullowa a kansa."*
_Imamu Muslim_