Karipagt

Karipagt Abba AJI

19/07/2023
19/07/2023

Yan nageria da fatan an samu cigaba da saukin rayuwa akan gwannatina👋👋👋

26/06/2022
13/04/2022

YAU SHEKARA 15 DA KASHE SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM KANO

Takaitaccen Tarihinsa

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, ranar 12 ga watan February 1960.

Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a Wurin mijin Yayarsa, Mallam
Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza,
kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano.

Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai s**a zauna a makarantar Malam Abdullahi, Wanda
asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980.

Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen
kasar Misra a cibiyar yada Al ' Adun Rude Misra, Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru
na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu.

Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da Daddare Bayan Sallar Isha' in, waccan kuma ta koyo harshen
larabcin da yamma.

Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983.

Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.
A shekara ta 1989,ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta
Ilimin Tafsir wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.

Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar
Kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan.

Yana dawowa gida baiyi wata -wata ba yakama wa'azi,yakuma kafa cibiya maisuna USMAN BIN AFFAN. Cikin shekara ta 1995 wannan cibiyar ta shahara, kuma tazama wacce take cin gashinkanta, yana koyar dayawa karatun addini, duk watan Ramadhan yakanyi a garin Maduguri.

Har ila yau shine shugaban asusun wannan cibiya ta Usman Bin Affan. Yawakilci Najeriya a gasus**an kur'any alokuta daban -daban, yana Cikin kwamitin malamai na jihar Zamfara da Bauchi.

Sannan kuma, kafin Rasuwarsa,ya yi kokari wajen kammala karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (Phd), a Jami ' ar usman dan Fodiyo da take Sokoto.

Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,
Sheikh Abdul-Aziz Ali al- Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar dandago,wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa.

Akwai kuma Jibrin Abubakar Sheikh Limamin Masallacin Juma'a BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.

Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt.

Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, ARB'UNA
Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus salaatun Nabiiy.

Sannan kuma yana gudanar da karatuttuka a gidajen rediyo, da talabijin daban -daban. Kamar su rediyo, Kaduna, Bauchi ARTV Kano, DITV, Kaduna NTA, Borno, OITV Damaturu, NTA Yola.

Wasu daga cikin daliban Malam sun hada da Malam Rabi 'u Umar R /lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Mallam Abdullah Usman da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani Da Malam Yunus Ali Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da malam anas Muhammad Madabo.

Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (SHIEK JA'AFAR ISLAMIC DOCUMENTATION CENTRE ).

Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428
(13/04/2007) kimanin karfe 5:30 na asubah. Alokacin yana jagorantar sallar asubah a babban masallacin jaumma'ar dake anguwar Dorayi. Wasune wadanda har yau din nan ba a gano su ba. Da makamai s**a shigo har Cikin masallacin s**a harbe shi. Sun same shine a kirjinsa da kuma wurin cibiyar Sa.
Anyi hanzarinwucewa dashi babban asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma kafin likitoci su zo gare shi ya bar duniya.

Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan s**a halarci jana'izarsa, kuma
an binne shi ne a makabartar Dorayi.

Allah ya jikan sa, ya gafarta masa, ya yi masa tagomashi da gidan aljanna.
Amin.

Mukuma idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.

Akoma
13/04/2022

Akoma

Asalamuaikum maza da mata Munagayatarku dorin auren na Ibrahim AISAMI sulloma ranar asabar daidai kofar gidamu nan bakin...
02/03/2022

Asalamuaikum maza da mata
Munagayatarku dorin auren na Ibrahim AISAMI sulloma ranar asabar daidai kofar gidamu nan bakin kasuwar damasak 2022.03.05

04/02/2022

ALAMOMI 10 GA WANDA DUNIYA TA AURE SHI

1. Idan ya zamto baka jiran sallah saidai sallah ta jiraka.

2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur'anin ka ba (wai bakada lokaci).

3. Idan ya zamto kafi damuwa daka burge mutane koda zaka sabawa ubangijinka.

4. Idan ya zamto kullum tunaninka yaddazakayi ka tara dukiya da kudi bakada lokacin tunanin hisabi.

5. Idan ya zamto baka karbar nasiha.

6. Idan ya zamto babu rayuwar da take birgeka sai rayuwar mawaka da 'yan kwallo da makada.

7. Idan ya zamto bakada lokacin sauraron wa'azi ko karatun al-qur'ani.

8. Idan ya zamto kana jinkirta aikin alkheri sai watarana.

9. Idan ya zamto bakada lokacin neman ilmin
addininka sai dai na neman duniya (boko).

10. Idan ya zamto ka karanta wannan sakon ba tare da kayi Share dinsa ba don 'Yan'Uwa su Amfana, kuma bai Qareka da komae ba.

Allah (swt) Ya Yafe mana zunuban mu manya da qanana Ameen Summa Ameen.

Dan Qaunaku da Allah kuyi share da Inviting Domin Bunkasa wannan group me Albarka, Saboda yaÉ—a musulunci.

To Allah yashimu
03/02/2022

To Allah yashimu

01/02/2022

Sanda zumunta yana wajaba
Yanketa Kuma yana haramta
Allah madaukaki yace kuba
Dan uwa hankinsa da miskini da matafiya
Kada kuyi almubazaranci
Suratul israi

Qala taalaa wat tadul laha ladhiy tassaa aluna bihi walarhama an

09/11/2019

ASSALAMU

Address

Mobbar
Lagos
ALBB

Telephone

+2347089556875

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karipagt posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share