03/11/2020
Alkusady and 29 others.
LIMAMI BARAWO!
A watan Ramadan,wasu mutane s**a gayyaci wani limami shan ruwa a gidansu,sabida girmama shi da suke yi,a gurin da limamin ya zauna zai ci abinci,matar gidan ta manta da kudin ta a gurin,
Bayan liman ya gama cin abinci yayi sallama ya tafi,sai ta duba,amma sai bata ga kudin ba,kuma bata da yara,kuma babu Wanda ya shigo gidan sai wannan liman din.
Sai ta fada wa mijinta,tace yaje ya sameshi,Dan ya karbo mata kudin ta.
Sai yace mata bai kamata a kunyata shi ba,ko a zubar masa da mutunci,sabida yana da kima a idon mutane.
Amma s**a yanke shawarar su dena bin sa sallah,kuma su yanke duk wata alaqa dashi,haka ko s**a yi.
Ana nan sai Allah ya sake kai su wani Ramadan din,sai mijin ya nuna wa matar,falalar yafiya,da kuma mantawa da komai da ya faru tsakaninsu da liman,kuma ma ya kamata su gayyato shi Dan ya zo yayi buda baki a gurinsu,Dan su sami cikakkiyar lada.
Sai matar tace ta yadda,amma da sharadin idan limamin ya gama buda baki,su nuna masa rashin kyautawar abinda yayi,sai mijin ya amince da sharadin.
Bayan sun gayyato liman,kuma ya gama buda baki zai tafi,sai matar ta yiwa liman magana,kan cewa a waccan shekara,sun ajiye kudin,kuma sun tabbatar shi ya dauka,sabida haka wannan abu ne da bai dace ba.
Sai wannan limamin ya sunkuyar da kai,da ya d**o kai,sai ga idanuwansa cike da hawaye.
Yace tabbas ni na dau kudin.
Sai s**a ce to shikenan ya dena kuka,
Sai yace masu ba yana kuka bane dan ya dauki kudin,yana kuka ne sabida sunyi kwana dari uku da sittin da biyar (365) basu karanta alqurani ba.ya ce a lokacin da ya dau ki kudin,ya saka shi ne a shafin farko na alqurani,a inda suratul fatiha take.
Sai matar ta tashi taje ta bude alqurani, sai ta ga kudin a ciki.
Sai s**a fashe da kuka,sai s**a durkusa a gaban liman suna neman yafiya akan abinda s**a masa..
Sai yace masu:ni din me? Ai ba ni kuka yiwa laifi ba,Allah kuka yi mawa, sai Ku koma Ku nemi gafarar sa.
Mafi yawancin mu haka muke yanzun,mun kauracewa alqurani Al