25/05/2025
Yana Kofar Gida a zaune sai wasu Mata s**a ce suna neman Gidan Rabiāatu. Sai yace su miki hanya su sake tambaya za'a nuna musu.
Bayan 'yan mintuna s**a dawo s**a ce ai Kofar Gidan da yake zaune nan ne aka musu kwatance.
Sai ya sake ce musu gaskia ba nan bane su kara mikewa su tambaya.
Bayan lokaci s**a sake dawowa s**a ce lallai fa nan Gidan da yake zaune nan aka sake nuna musu.
Sai yace nan dai Gidana ne, ba Gidan Rabi ba, idan Gidan su kuke so shine na nuna muku inda zaku je. Amma nan Gidan Shehu ne ba na Rabi ba.
Sai suke ce to ayi hakuri Gidan Shehu, yace ku shiga Rabin na ciki.