21/09/2024
KADAURE KAKARANTA WANNAN SAKO YANADA AMFANI GAREKA
JAN HANKALI DA TUNA TARWA GA YAN UWANA MATASA MAZA DA MATA WANNAN SHINE AKEKIRA NEMAN INCI MUFALKA MUSAN ABINDA MUKEYI.
Yan uwana matasa yakamata kusan abinda kukeyi wallahi wadannan mutanen basuda mu da mu ba sannan basuda alkawali yaudai komai rashin ganewar mu yakamata mugane anaso dole sai angurbata muna tunanin ta hanyar bamu abubuwa kamar haka:-
1. Kwayoyi domin gushewar hankali kutambaya Ina diyansu suke.
2. Makamai domin yakar juna akan banbancin ra'ayin siyasa kutambaya Ina diyansu suke.
3. Ansamu kyamar neman ilimin addini da zaman saboda mu bakowa bane illa diyan talakawa kutambaya Ina diyansu suke.
4. Ana amfani damu wajen yake zumunci tare da kiyayya ga Dan uwanka akan party siyasa kutambaya Ina diyansu suke.
5. Mukanyi karatu Amma basu San yanda muke yinsa ba Amma saboda Babu tausayi azukatansu sai ahana mu offer wadda zamu ci abinci da ita kuma Babu sana'a agaremu ko kudin jari to su kasan inda diyansu suke.
Wannan abin dubawa ne musamman yadda muka tsinci kammu ahannun su yadace mutashi mufalka mu haka muke fitowa wajen za6e musaida incin mu akan wayar salula(cellphone), ko shinkafa kwano 2---4, kokuma akan naira N2,000.
To wallahi kada kayi alfahari da kudin da ake baka tun daga N1000 zuwa N1, million kana canyewa wallahi ba'a taimake kaba indai harya kasance taimakon ka akeso ayi to asamo maka aki wata ma'aikata inda zaka samu albashin N20k zuwa N50k wallahi yafi duk abinda zabaka Wanda ko lalurar kwana Daya(1) bazatayi maka ba
✍️ Nasir Ladan kokuma Nasir Bello
21/September 09/2024