Iafa7959

Iafa7959 Masha Allah alani I'ma tillah

21/04/2025
14/10/2024

Ban amince in goyawa kowa baya ba a zaben 2027 mai zuwa ba- Inji tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.

Sanarwar ta biyo bayan wani cece-kuce a shafin sada zumunta na X dake bayyana cewa Atikun ya amince ya goyawa gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir baya a matsayin dan takarar shugaban kasa daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Sai dai wannan martani yazo ne a dai-dai lokacin da waccar wuta ke ruruwa, inda Atiku ya bayyana cewar babu wanda ya marawa baya hard zuwa yanzu.

Shin ya dace Atiku ya marawa wani dan takarar baya kokuwa ya sake nema?

14/10/2024
14/10/2024

Fadar shugaban kasa ta gargadi 'yan Najeriya masu kiran shugaban kasa Bola Tinubu da T-PAIN, don haka kowa ya kiyaye.

14/10/2024

Give Them Movie Name😂😂😂

13/10/2024
11/10/2024

WATA SABUWA: Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin hana kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP korar Umar Damagum daga mukaminsa na shugaban riko na jam’iyyar PDP

A yau Juma'a ne Jaridar ATP Hausa ta rawaito cewa, Masu ruwa da tsaki na jihar Ribas sun dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa da sakataren jam'iyyar na kasa bayan zarginsu da raba kafa.

An yanke wannan huluncin ne a wata tattaunawa da mambobin su gudanar a babban birnin tarayya Abuja a safiyar yau Juma’a.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ne ya tabbatar da hakan. Ya fitar da sanarwar da ke isar da hukuncin NWC da karfe 3:18 na safiyar yau Juma’a.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Kwamitin ayyuka na kasa, NWC, na jam’iyyar PDP ya yi nazari sosai kan jerin korafe-korafen da aka yi wa shugaban riko na kasa, Amb. Illiya Damagum da Sakatare na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, musamman dangane da wasikar da s**a aike wa kotun daukaka kara a kan matsayin jam’iyyar a shari’ar da ta shafi tsaffin ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su 27, wadanda s**a bar kujerunsu. Bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Sai dai babban Kotun Tarayya dake Abuja ta hana cire Shugaban rikon Iliya Damagum akan mukaminsa na shugaban riko.

11/10/2024

Tinubu zai yi amfani da makonni biyun ne a matsayin hutun aiki, don yin tunani a kan sauye-sauyen da ya samar a Gwamnatinsa don samo mafita ga yan Najeriya - inji fadar shugaban kasar.

Tinubu dai ya gudanar da wasu jerin tafiye-tafiye zuwa Birtaniya da Faransa tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a watan Maris din 2023.

A ranar 29 ga watan Agusta, Tinubu ya bar Abuja zuwa China amma ya tsaya a Dubai kafin ya isa birnin Beijing ranar 1 ga Satumba.

A ranar 16 ga Satumba, Shugaban ya koma Abuja bayan ziyarar da ya yi ta tsawon mako biyu mai albarka' a China da Birtaniya.

A yayin ziyarar wanchan lokacin na zuwansa
Burtaniya, shugaban ya gana da Sarki Charles III a Landan, inda aka tattauna kan sauyin yanayi.

A wannan karon Shugaba Bola Tinubu na shirin zuwa birnin Paris na kasar Faransa daga birnin Landan na kasar Birtaniya, a kowane lokaci daga yau ka iya barin birnin Landan don yin wani muhimmin sha'ani wanda ba'a bayyana ba.

Wani makusancin siyasa na Tinubu ne kuma tsohon abokin takararsa, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Juma’a.

Address

Abuja

Telephone

+2348119964820

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Iafa7959 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Iafa7959:

Share