Ummu Ahmad

Ummu Ahmad Am nothing am Zero behind decimal point

25/12/2021

*ADDINI NASIHA NE*

Mutane suna so su yi arziki amma suna manta zunubai suna hana arziki.

Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: *"Lallai ana haramta ma bawa arziki saboda wani zunubi da yake aikatawa"*.

12/12/2021

"Abinda yafi komai takaici a Alkiyama shine, ga ladanka baka iya bawa iyayenka da 'ya'yanka da masoyanka ba amma kana kallo za'a dauka a ba makiyanka don kaci namansu ko ka zalunce su wajan yin munarfurcinsu ko cin dukiyarsu bada izni bah".

*Ya Allah ka tsaremu da fadawa tarkon Shedan

01/12/2021

HANYOYI DA ZASU AMFANEMU DON CIN MORIYAR SAURAN KWANAKIN DA S**A RAGEMANA MASU MATUKAR TSADA:
1. Yawaita Istighifari
2. Yawaita Karatun AlQur'ani Ladan bai misaltuwa.
3. Yawaita Sadaka - Hanyar samun tsira ce.
4. Dauki Waya ka Kira 'Yan uwa - Sadar da zumunci ne.
5. Kame bakin ka - Zaka kubuta daga gulma ko alfasha.
6. Yi Addu'a wa danuwa - Malaa'iku za su maka.
7. Taimaka Wa mabuqaci - Allaah zai baka mafita.
8.Ciyar da mai Azumi - Zaka samu ladar Azumi a sauqaqe.
9. Kwanta da wuri - Hakan zai baka daman tashi da dare.
10. Yawaita yin zikiri - Wannan zai baka daman kusantar mahaliccin ka.
11. Rage Shiga Social Media - Hakan zai Baka damar Ibadah.
12. Yafe ma Wanda Ya Maka Laifi, Hakan zai Sa Allaah Ya Yafe Maka.

13. Tura Wannan Saqon Wa Wani - Hakan Zai Sa Ka Samu Ladan Wanda Yayi Aiki Da Shi.
✍🏼✍🏼Ummu Ahmad

30/11/2021

Da GASKE Ka KE KO YAUDARAR KANKA Ka KE??

Imam Ibnul Jauzi Allah ya masa rahama yana cewa, "Sau tari akan samu mutum yana ikrarin yana da tauhidi alhali mushrikine wa Ubangijinsa, dayawa akan samu mai cewa shi bawan Allah ne alhali kuma bawan cikinsa ne, yana saɓawa Ubangijinsa wurin yiwa kansa biyayya, ya sayar da yardar Allah dan neman yardar abun halitta irinsa.
Sau nawa aka samu mai bin son zuciyarsa wanda ya riki zuciyarsa a matsayin abun bautarsa, sau nawa kuma aka samu wanda yayi riko da umarnin Ubangijinsa wanda yake sayar da kansa wurin neman yardar Ubangijinsa".

28/11/2021

Mace ta gari ita ce wadda ta san Abinda ya dace ta yi idan mijinta yana cikin fushi ko yunwa ko gajiya. Sakarai ita ce wadda ake jin sirrin mijinta daga wurin ta.

Namiji sadauki shine idan ya samu alheri sai ya nufo gida wurin iyalansa. Sakarai
shi ne mai dukan matarsa.

A lahira Munafukai sune a ƙasan wuta. Amma a duniya sunayensu ne a saman Jarida.

Mutum biyu ba a gaskata maganarsu: Mai neman aure da mai neman aure

Mutum uku kana iya biyan su: Wanda ya fara yi maka sallama, da wanda ya ba ka wurin zama, da wanda ya yo tafiyayya zuwa wurin ka. Na huɗu sai dai ka roƙi Allah ya biya shi: Shine, wanda yake da buƙata bai ga inda ya dace ya nemi taimako ba sai a
wurinka.

Address

Sumaila
Abuja
NO

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ummu Ahmad posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Ummu Ahmad:

Share