Muso juna a musulunci

Muso juna a musulunci Daura

05/09/2022

"Sallar Nafila Lokacin Da Liman Ya Hau Minbari Ranar Jumu'ah.

1) Idan mutum ya shiga masallaci ranar Jumu'ah liman yana akan minbari, zaiyi sallah raka'ah biyu, amma ya gajarta. (Bukhari da Muslim)

2) Idan mutum ya taradda ana kiran sallah kafin a fara khutbah, zaiyi sallah lokacin da ake kira bazai jira a gama kiran sallah ba, saboda sauraron khutbah wajibi ne amma sauraron maikiran sallah Sunna ne. ( Ibn Uthaimeen)

3) Idan mutum bai samu shiga masallaci ba ya tsaya a harabar masallaci, bazaiyi sallah ba lokacin da liman ke khutbah, saboda sallar ta Tahiyyatul masjid ce, bata wajaba sai ga wanda ya shiga masallaci.

4) Mutane da yawa sukanyi kuskure sai su zata akwai wasu raka'ah biyu da akeyi kafin Jumu'ah, sai kaga mutum yazo yana wajen masallaci ya kabbarta sallah alhali liman yana khutbah. Wannan kuskure ne, matsayin sa kamar wanda ya tashi a cikin masallaci ya kabbarta sallah alhalin liman yana khutbah.

5) Duk wanda ya shiga masallaci wajibi ne (a kan zance mafi inganci) yayi sallah raka'ah biyu kafin ya zauna. Wannan hukuncin da ranar Jumu'ah da Assabar da sau ran ranaku duka daya ne. Dalili akan hakan shine, cewar da Manzon Allah S.A.W. yayi: Idan dayanku ya shiga masallaci kada ya zauna sai yayi sallah raka'a biyu. ( Bukhari da Muslim)

Ya kamata ayi fadakarwa da mutane akan wannan hukuncin, saboda da yawa akan saɓa."

Sheikh Jabir Sani Maihula

27/08/2022

ASSALAMU ALAIKUM
Yan uwana musulmi da fatan kun tashi lapiya

25/08/2022

ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAHI WABARAKATUHU
Barkanku da rana yan uwana

08/08/2022

BARKANKU YAN UWANA MUSULMAI BAKI DAYA

Address

Community
Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muso juna a musulunci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share