26/05/2026
Assalamu Alaikum,
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, sannan godiya ta musamman ga daukacin al'ummar Alkaleri da Kirfi iyaye, yayyi, kanne, da abokan arziki.
Bamu da kalaman da za su bayyana adadin godiyarmu bisa yadda kuka sadaukar da lokacinku, kuka jure zafin rana, kuka ajiye uzururrukan ku domin nuna mana soyayya da goyon baya. Wannan karamci da kuka nuna mana ya tabo zukatanmu, kuma sako ne da zai zauna daram a ranmu har abada.
Muna rokon Allah Ubangiji Ya ba mu ikon sakawa al'umma da alheri. Insha Allah, idan Allah Ya bamu wannan dama, amana za ta dawo hannun masu amana. Zamuyi muku aiki na gari da adalci wanda ba zai zo da nadama ba.
Allah Ya saka muku da mafificin alheri, Ya kuma daukaka al'ummar mu baki daya.
Mungode kwarai da gaske.🙏🙏🙏