29/09/2021
MU KULA DA FACEBOOK ACCOUNT DINMU
Pls share
Idan aka kwace account dinka ba kai kadai matsalar za ta shafa ba, idan kai ba ka damu da kanka ba to kayi tunanin wasu da matsalar za ta shafa. Sanin kanmu ne cewa kwanakin nan an faye yawan datse accounts na mutane musamman na Facebook, har da asusunsu na banki, to kayi hattara!
Ga shawarwari guda biyar kacal idan za ka iya binsu sai Allah ya tseratar da mu baki daya.
1. Ka da rika amfani da password mai sauki, kayi amfani da "strong password" kamar yadda masana s**a umarta. Ka da ka sa date of birth, lambar waya ko wani sunanka ko sunan budurwarka. Akwai dalili mai karfi da ya saka masana s**ace hakan, kai dai ka kiyaye kawai.
Misali na strong password:
MoH&i)D(deEn%20+20*jp.J&a
2. Ka da ka ajiye lambar wayar da aka sanka da ita a matsayin phone number ka da ka saita account naka da ita. Idan so samu ne ka da ka bari wani ya taba sanin lambar ma bale kayi rajista da ita a wani wuri.
3. Ka da ka kasance mai amfani da password daya a ko ina, misali password dinka na Facebook ya kasance daban da na NPOWER, SMEDAN, Gmail... sannan ka daina yawan rajista da websites ko apps din da ba ka san sahihancinsu ba, kuma ka kayi hattara da bin links!
4. Ka saita two-factor authentication da logging notification, sannan kayi verifying identity naka.
5. Ka da ka sake ka ba wa wani details naka, kuma kayi hankali da email naka sosai.
Ka turawa abokanka da 'yan uwanka don su ma sun ankara.
Allah ya tsare mu!
pls kuyi share domin wasu su amfana
HAZAKA tv