20/12/2022
Sheíkh Abduljabbar Sheíkh Nasíru Kabara A Karní Na Ashirín Da Dayá
DÁGA Hussaini Fata
Duniya ba ta shedi wani mutum a dunìya hausa Fulani ba wanda kungiyoyin addinin Musulunchi s**a hadu domin yaki dashi kamar Sheíkh Abdúljabbar Nasíru Kabara ba, domìn kowannen su yana da matsala da shi saboda wasu dalilai, kodai akan shehin su ko aqidar su ko kungiyar su
An fara jin muryar Sheíkh Abduljabbar Nasíru Kabara né a karshen 1990s, inda shehin Malamín ya fara kai harî janibin masu da'awar iyayen Annabí suna wuta, Manzón Allah yana fitsari a tsayé, ba'a tawassulí da Annabí, da sauransu, inda shehin malamin ya shahara da martani mai gauní akan masu irin wannan aqidar da dalilai na Ilmi, har yana cewa; "Wadaran Addini in har ba zai tsayu ba sai an ta6a kimar Annabin da yazo da addinin"
Sheíkh Abdúljabbar Nasíru Kabara Mútum ne kafaffe akan abinda yakai yakini akan sa, wanda baya yin shiru akan duk wata tawaya da aké jinginawa a janibin Allah (T) da Manzonsa, da sunan nassi ko ruwaya, hakan yasa ya samu matsala da wasu masu kiran shehin su da Allah da kuma masu cewa Allah yana da nauyi musamman idan yayi fúshí, har al'arshí ma tana qara idan yayi fushi, ko kuma su ce Allah yana sakkowa daga wani waje zuwa wani waje, ko kuma s**e wutar jahannama ba zata cika ba sai Allah ya sanya kafarsa a cikin ta sannan zata ce da ubangijin ta na cika yanzu, da sauran kurafat da aka cusa a aqidun Musulunchi kuma ake inganta su. Akwai wata ibarar sa da yake cewa; "Idan an ce muslim ne ya inganta sai muce ai ana yin Musulunchi tun kafin Muslim ya inganta wannan tatsunniyoyin"
A matsayin sa na wanda ake ganinsa sufi kuma bakadire a tashin farkó, yayi kokari wajen tsaftace wasu al'adu a tafiyar gidan su na darika, inda ya nuna wasu tasarrufofi da akeyi a gidan su da sunan dariqa, ya nuna ba su da inganchi a addini, don haka ya chanchanchi a daina su, hakan yasa anan ma ya samu matsala da wasu daga cikin 'yan'uwan sa na jini, har wasun su s**a rinqa barazanar kashe shi t