Katafare Tv

Katafare Tv Domin samun ingantatun labarain cikin gida da ketare. Stay informed with the latest news, updates, and insights from around the world

we sell portable water at this factory in better price.

"An kafa Tijjaniyya ne a karkashin Kitabu Wassunah Don haka Bin Shari'a Da Sunna Wajibi Ne Ga Tijjanawa"~Nigerian M***i ...
18/06/2025

"An kafa Tijjaniyya ne a karkashin Kitabu Wassunah Don haka Bin Shari'a Da Sunna Wajibi Ne Ga Tijjanawa"~Nigerian M***i Sherif Ibrahim Saleh Al-Hussaini.

DA DUMI DUMI:|•Rahotanni daga Jahar  Filato na nuni da cewa Gwamnatin jahar ta kwace akalla Babura 142 a wani sabon yunk...
17/06/2025

DA DUMI DUMI:|•Rahotanni daga Jahar Filato na nuni da cewa Gwamnatin jahar ta kwace akalla Babura 142 a wani sabon yunkuri na sake aiwatar da dokar hana zirga-zirgar babur a cikin babban birnin Jos-Bukuru.

Jami’ai sun ce an dauki matakin ne da nufin dakile karuwar barazanar tsaro da kuma inganta lafiyar al’umma a yankin babban birnin Jihar.

Kufadamana ra'ayoyinku a comment section.
13/06/2025

Kufadamana ra'ayoyinku a comment section.

Wata mace mai suna Damilola Adekunle ta ce binciken da tayi ya tabbatar mata cewa matashin nan da aka dade ana nema wand...
11/06/2025

Wata mace mai suna Damilola Adekunle ta ce binciken da tayi ya tabbatar mata cewa matashin nan da aka dade ana nema wanda ake yiwa lakabi da Dadiyata ba shi da rai, wato ya rasu.

Mai bi ciken a farkon watan da ya gabata ta fitar da sanarwar cewa zata bada tukwicin naira miliyan goma ga duk wanda zai bata bayani akan Dadiyata, inda ta nemi jami'an tsaro da 'yan jarida su sayar mata da bayanai koda kuwa nawa ne zata biya, ita kuma zata ɓoye sunansu.

A wani rubutu fa tayi a jiya a shafinta na Facebook ta mika ta'aziyyar rasuwar matashin inda ta bayyana bakin ciki da kaduwa game da lamarin.

SUPPORT THE CREATION OF DARAZO DISTRICTAna kira wa dukkan masu ruwa da tsaki dadukkan al'umma dasu bada goyon baya wajen...
10/06/2025

SUPPORT THE CREATION OF DARAZO DISTRICT

Ana kira wa dukkan masu ruwa da tsaki dadukkan al'umma dasu bada goyon baya wajen kira da kuma neman Sandan Girmamawa wa masarautar Darazo saboda jimawa dakuma tarihinta.

Samaila Muhammed bcj
CEO Samir Technology Ltd

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN🔥 Rashin Imani  Ango Ya Yanka Matarsa Bayan Watanni Biyu da AureA yau al'umma ta sake ...
10/06/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

🔥 Rashin Imani Ango Ya Yanka Matarsa Bayan Watanni Biyu da Aure

A yau al'umma ta sake girgiza da wani mummunan lamari da ya faru a layin Minister, cikin karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano. Wani matashi da aka ce sabuwar amaryarsa ce, ya aikata abin da ya girgiza zukatan mutane—ya yanka matarsa har lahira!

Lamarin ya auku ne da rana tsaka, bayan sallar Azahar. Rahotanni daga wurin da lamarin ya faru sun tabbatar cewa an samu mamaciyar da raunuka masu tsanani a wuya da cinyarta. Abin takaici da ban al'ajabi, ana zargin mijinta da aikata wannan kisan gilla, inda shi kansa aka same shi da raunuka a hannunsa – alamar yankan wuka.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

> "Wallahi, wannan abu ya girgiza Gwarzo! Auren su bai wuce wata daya da sati guda ba, amma gashi sun kai ga kisa.

Mutane da dama sun taru a kofar gidan suna kuka, wasu kuma cikin firgici da fargaba, suna tambaya: Shin me ke haddasa irin wannan mummunar dabi’a tsakanin ma’aurata a wannan zamani?

Wasu na cewa soyayya ce ta jirkice, wasu kuma suna kallon hakan a matsayin sakacin da ke yawaita a tsakanin sabbin ma’aurata, tare da faduwar tarbiyya da rashin kulawar iyaye da malamai.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamaciyar, Ya kuma sa ta huta cikin rahamarsa. Allah Ya hana faruwar irin wannan abu a gaba. Amin.

Zakakurin dan wasan Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya ci gaba da buga wa ƙungiyar Al Nassr, wanda hakan...
09/06/2025

Zakakurin dan wasan Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya ci gaba da buga wa ƙungiyar Al Nassr, wanda hakan na zuwa ne bayan lashe kofin Nations League da ya yi a ranar Lahadi.

A baya-bayan nan ne Ronaldo ya nuna alamun cewa zai bar kulob ɗin da ya fara buga wa wasa a Janairun 2023.

Iran ta gargaɗi ƙasashen Turai kan shirin tozarta ta dangane da makamashin nukiliya
09/06/2025

Iran ta gargaɗi ƙasashen Turai kan shirin tozarta ta dangane da makamashin nukiliya

Tsohon Hafsan Sojin Najeriya Tukur Burutai Ya Sha Da Ƙyar Daga Harin Ƴán BíndígaTsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laf...
09/06/2025

Tsohon Hafsan Sojin Najeriya Tukur Burutai Ya Sha Da Ƙyar Daga Harin Ƴán Bíndíga

Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya sha da kyar daga harin da wasu 'yan bíndíga s**a kai wa tawagarsa a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Jumma’a, yayin da Buratai ke tafiya a cikin gundumar ƙasar Kanuri, inda gungun 'yan bíndíga s**a bude musu wuta a cikin daji.

Kamar yadda wasu majiyoyi daga rundunar tsaro s**a tabbatar, motar da tsohon hafsan ke ciki ta sha bíndíga sosai, amma babu wanda ya mutu ko ji rauni mai tsanani.

Wani jami’in tsaro ya ce, “Lamarin ya faru da gaggawa, amma tawagar sojoji da ke rakiyar Buratai sun mayar da martani, s**a fatattaki maharan.”

Har yanzu ba a tantance ko Bókó Hárám ne ko ISWAP ne ke da alhakin harin ba.

Yanda ma’aurata  s**a je kotu dan a raba aurensu! Idan kaine alkalin wacce shawara ko hukunci za ka yanke?
09/06/2025

Yanda ma’aurata s**a je kotu dan a raba aurensu! Idan kaine alkalin wacce shawara ko hukunci za ka yanke?

Address

Eagle Sino Plaza
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katafare Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share