Dandalin Adabi Na Kabawa -Kebbi Literary Club

Dandalin Adabi Na Kabawa -Kebbi Literary Club Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dandalin Adabi Na Kabawa -Kebbi Literary Club, College & University, Birnin-Kebbi.

13/10/2021

This is Africa spoke to Sada Malumfashi, the director of the Hausa International Book and Arts Festival (HIBAF) which will be hosting its first edition.

HABBAKO DA ADABI (LITERATURE) A MATSAYIN HANYAR SAMUN CI GABA MAI DOREWA GA ALUMMABincike ya tabbatarda cewa ba wata alu...
11/10/2021

HABBAKO DA ADABI (LITERATURE) A MATSAYIN HANYAR SAMUN CI GABA MAI DOREWA GA ALUMMA

Bincike ya tabbatarda cewa ba wata alumma wadda ta taba ci gaba fiye da iliminta da wayewarta. Shi kuma iliminta da wayewarta ana gane su ne kuma suna ingantuwa ne ta hanyar adabin (Literature) din ta.
Masana suna fassara adabi a matsayin wani fannin ilimi wanda ya ƙunshi labarai da waƙoƙin baka da rubutattu da wasannin kwaikwayo da al'adu da abubuwan fasaha da na hikima (hadi da kuma karatunsu).

Da wannan adabi kasashen Larabawa da Turawa s**ayi amfani wajen fadakarwa da hankaltarda yanuwansu ga irin duhun jahilci da rudani na rashin shugabanci na gari da suke ciki (A zamanin turawa ana kiranshi Age of Enlightenment a fakaice).
A nan kasar Hausa, da wannan adabi ne su Mujaddadi Shehu Danfodiyo (Allah ya jikansa da rahama) tare da kanensa Abdullahi, da 'yayansa Muhammadu Bello da Nana Asmau dama sauran dalibansu s**ayi amfani wurin kira ga alumma ta hanyar wakoki, kasidu da rubuta litattafai har aka samu s**a fahimta.

To idan munyi laakari da wannan zamani namu, zamu ga lallai anyi wasa da wannan adabi sosai. Sannan duk da akwai wasu aikace aikace na hikima da akayi, amma bamu karatun su. Ga wadanda suke yunkurin yin adabin ko karatun kuma, to mafi yawa suna yinsa ne da yaren turanci.
Wannan yasa muka yanke shawarar mu buda wannan kafa domin ciyar da wannan adabi gaba a yarukanmu na gida, (duk da a shi adabi ana so mutum ya iya fahimtar yaruka da dama -wato ya zamto "multilingual" domin amfana da hikimomi daga wurin marubuta na aladu daban daban.)
Ta wancan din, marubutan litattafai da mawakan gargajiya da ma masana masu hikima da masu kasidu zasu rika duba zuwa ga matsaloli na alumma sannan suna rubutu kuma suna isar dashi cikin yaren da alumma suke fahimta cikin sauki domin samun cigaban Alumma.

Address

Birnin-Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandalin Adabi Na Kabawa -Kebbi Literary Club posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share