22/03/2026
MATSATSUBI CIGABAN KUNDIN TSATSTUBA 12
Abdulaziz Sani M Gini
A baya mun tsaya ne a inda ake zayyana bayani akan gimbiya Luzaiya😏😏:-
Tana da ƙwala-ƙwalan idanu a ƙarƙashin gira mai ƙyallin baƙi kuma sun kasance masu haske sosai, hancinta dogone siriri k**ar alƙalami a ƙasansa an dasa mata ƙaramin baki mai ban sha'awa.(🙄🙄🙄🙄 wannan bayani haka 🙄🙄).
ldan tayi murmushi sai kaga k**ar kyawun nata ya linka kansa.(Wata sabuwa😝😝😂).
# # # # #
Tana tafe a hankali cikin izza ta iso gaban mahaifinta shi kuwa sai ya miƙe ya tare ta sannan ya k**a hannunta na dama ya sumbaci kan yatsunta sannan ya zaunar da ita kusa dashi suna masu duban juna cikin murmushi da nuna zunzurutun ƙauna.
Luzaiya tace "Ya kai Abbana ina can gidana yanzu ina shirin fita rangadi bayan gari sai ga saƙonka ya riskeni cewar na dakatar da fita shin lafiya kuwa?"
Sarki Fahalul Bahafus yace "E, to lafiyar kenan amma ba ƙalau ba. Abin da yasa nace ki fasa fita shine labari yazo mini cewa rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari kuma ba'a san me ya kawo suba.
Don haka yanzu na tura aje aji dalilin zuwansu ƙasata."
Koda jin haka sai Luzaiya tayi murmushi tace "Ai koma dame s**a zo dai dai muke dasu, ya kai Abbana ni kam nasan cewa a halin yanzu yadda kake da tarin gwarzaye mayaƙa babu wata runduna da zata iya cin mu da yaƙi."
Sarki ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Tabbás haka zancenki yake 'yata domin inda na kasance azzalumi da tuni yanzu na mallaki duk ƙasashen dake maƙwabtataka damu." Sarki na gama faydin haka kenan sai ga Jambu ya dawo ɗauke da wasiƙa,da zuwa sai ya miƙa takardar ga sarki shi kuma ya baiwa magatakarda ya umarceshi daya karanta ta.
Take magatakarda ya warware ya fara bayani k**ar haka:-
"DAGA JARUMI NAZMIR BIN HALUFA ZUWA GA SARKI FAHALUL BAHAFUS NA BIRNIN MAHAZÜS.
GAISUWA TARE DA BIYAYYA A GAREKA YAKAI WANNAN SARKI, KAYI SANI CEWA NI MANZO NE DAGA SARKI BASHAKUR NA BIRNIN DAHAMUL KUMA BAI TURONI GARE KA DAN KOMAI BA SAI DON NA YANKE KANKA NA KAI MASA KUMA NA TAFI DA KYAKKYAWAR 'YARKA GIMBIYA