17/10/2025
DA DUMI-DUMI: Mutum 6 sun sauya addini zuwa Kiristanci a Arewacin Najeriya — inji Fasto
Daga Jaridar Muryoyi
Jaridar Muryoyi ta ruwaito- wani Fasto da ya bayyana cewa yana yawon wa’azi a sassan Arewacin Najeriya domin jawo mutane zuwa addinin Kiristanci ya ce akalla mutum shida sun sauya addini a karkashin wa’azinsa.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Muryoyi ta ruwaito an ga Faston yana yi wa matasa wankan shiga addinin Kiristanci daya bayan daya, inda ya bayyana sunayensu da s**a hada da Sadiya, Basira Bafillatana (tare da mijinta Yusuf Aliyu daga Saminaka, Kaduna), Ansar Abdallah daga Kano, Abdullahi Umar Radda daga Katsina, Yahaya Muhammad daga Gombe, da Shamsudeen daga Kaduna.
Faston ya bayyana farin cikinsa da cewa sun “samu ceto,” tare da kiran a taimaka masu da Bible na Hausa da Fulatanci domin ci gaba da wa’azinsu.
Ya kuma gargadi sabbin masu shiga addinin da su guji karya, c**a, giya, da zina, yana mai cewa “addinin Kiristanci ba ya amincewa da wadannan abubuwa.”
Wannan bidiyon ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, musamman ganin yadda ake samun irin wannan sauyin addini a lokacin da wasu malamai Musulmai ke ta muhawara da tsine-tsine a tsakaninsu....
DAGA INA MATSALAR TAKE?