Muhammad Assalafy Gamawa

Muhammad Assalafy Gamawa Munbude wannan page ne domin wa'azantarwa da fadakarwa sunana Muhammad bura Assalafy gamawa unguwan

05/11/2024

ILimin Addini Ya Wayi Gari Ga Hannun 'Yan Sari Yau Jahilai Sunyi Dumu Dumu Cikin Rigar Malamta Sanadiyar Media😭

26/12/2020

Haka rayuwa take: Bakayiwa mutum komai ba kawai yaji baya KAUNARKA😃Yaji k**an zai mutu idan ya ganka🤔, haka kuma wani yake sonka yake kaunarka k**ar ya hadiyeka💚. Masoyana Ina kaunarku ina sonku! Allah ya bar kauna har Aljanna.

25/11/2020

"IYAKAR RASHIN DARAJA"

Mutanen akwai rashin daraja da kaunar Malaman Musulunci, kai ka ce Malaman Musulunci ne kadai su ka mayar abokan gabar su.

Maliminmu, Dr. Muhd Umar Sani Umar Rijiyar Lemo ya fid da sanarwan cewa, PDF Material da ke yawo na Tafsirin Alqur'ani Maigirma na farko a Harshen Hausa wanda shi ya wallafa, bai amince da ya'da shi ba, kuma ya na kunshe da kusakurai, don haka a daina.

A babin adalci da bokon da su ka fi gamsuwa da shi fiye da Islam, sai mutum ya dauka cewa za su girmama wannan matsayi na malam, saboda kasantuwar sa mawallafin da ke da hakkin hakan, amma da shike mutane ne marasa daraja, sai ma wasun su ke cewa za su ci gaba da ya'dawa. Shi kuwa shugaban su rankatakaf na Social Media, Dr. Abdullahi Dahiru sai ya yi wani mugun kafirin qiyasi, na hada Alqur'ani Maigirma da littafin abin koyin su Segun Adeneyi k**ar yanda za a gani a cikin hoto. Saboda sanin hali, mum san da yawan su za su lelleka Tafsirin ne ba don su fa'idanta ba, laaa, sai ma dai don neman kusakusarai da abin sukar Sunnah da Malaman Musulunci.

Saboda rashin darajar wadannan mutanen 'yan boko akida ne ya sa Shaihina Misbahu Saminu Madabo ya ce, "Su fa suna cikin takaici ne Malamin da ba sa 'kauna ya yi wani abin da Musulmai za su amfana sosai. Saboda haka yanzu sun sami topic za suci gaba da tattauna shi da kushe an ce kada aci gaba da fito da PDF".

20/11/2020

Aslm dafatan kowa yatashi lfy

14/11/2020

NEMAN YARDAR MUTANE

Kada ka damu kanka sai ka yardar da kowa da kowa, Annabawa ma ba su iya cimma haka ba.

Wanda yake kaunarka zai kalli abin da ka yi ya ga ya yi kyau, wanda ba haka ba kuwa zai ga mai kyau daga gareka ya ga ya kai karshen muni.

Idan abu mara kyau ya same ka sai mai sonka ya ce: Jarrabawa ce. Wanda ba ya sonka kuwa sai ya ce: Allah ne Ya k**a shi.

Don haka mu fahimta.

TSOHON GWAMNAN JIHAR IMO YA ZIYARCI SHUGABAN KUNGIYAR IZALAH TA KASA.A yau lahadi Tsohon Gwamna jihar imo kuma sanata Ma...
25/10/2020

TSOHON GWAMNAN JIHAR IMO YA ZIYARCI SHUGABAN KUNGIYAR IZALAH TA KASA.

A yau lahadi Tsohon Gwamna jihar imo kuma sanata Mai wakiltar imo ta yamma Sen. Rochas Okocha ya ziyarci Shugaban kungiyar IZALAH ka kasa sheikh (DR) Imam Abdullahi Bala Lau (Hafizahullah), ziyarar wanda ya gudana a hedkwatar Izalah ta kasa dake unguwar otako a babban birnin tarayya Abuja A Yau lahadi.

Address

Gamawa

Telephone

+2348032678560

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Assalafy Gamawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Muhammad Assalafy Gamawa:

Share