20/10/2021
Ranar Salati Ga Shugaba Haɗe Da Murna Da Watan Haihuwarsa SAW.
قدْ اختار من كلِّ الخلائقِ رسلَهُ
Ubangiji Swt Yazaɓi Ma'aikansa Sunzamo Mafifita A Cikin Kowacce Halitta.
لتعريفِهِم ما كفَّ عن علمِهِ الفكرا
Da Susanar Dabayi Ilimin Ubangiji Swt Wanda Ya Zarce Tunanin Masu Tunani.
ومنهمْ قد اختار الحبيب محمدا
Acikin Waɗannan Manzaninin Ya Zaɓi Babban Masoyinsa Annabi Muhammad Saw.
نبي الهدى روح الوجود أبا الزهرا
Annabin Shiriya, Jagoran Samammu Mahaifin Sayyida Fatimatuz Zahra.
ولو جاء في أعصارهم آمنوا به
Da Shugaba Saw Yazo A Zamanin Annabawan Da S**a Gabacesa Da Sunyi Imani Dashi.
وكانوا له من خير أجناده نصرا
Da Sun Zamo Sunfi Kowa Taimakamasa A Cikin Tawagarsa.
إمام جميع الرسل جامع فضلهم
Jagoran Duk Manzanni, Wanda Ya Tattara Baye Bayen Da Allah Swt Yayi Musu.
خطيبهم في الخطب إن حشروا حشرا
Mai Musu Huɗuba A Ranar Alqiyama.
ويجمعهم في الحشر تحت لوائه
Za'a Tattarasu A Qarqashin Tutarsa Ranar Alqiyama.
وكل يقول اشفع فأنت بها أحرى
Ko Wannansu Yana Cewa Kanemamana Ceto Kai Ne Kafi Cancanta.
اللهم صل على سيدنا محمد كاشف الغمة.
Allah Swt Ka Samu Cikin Marabauta Da Ceton Manzan Allah Swt .
Algetsawy Ibrahimu.