Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre

Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre Alhamdu Lillah😊 Mu Almajiran Ilim ne Muna Fahimtar AL-QUR'ANI MAI GIRMA da Litattafai da kuma Aiki da Koyar warsa bakin Iko. Albarkar Annabi s.a.w da Al-qur'ani

ALLAH KA ƘARA KARE TSANGAYUN MU TAREDA TABBATAR DA SU A FAƊINN DUNIYA BAKI ƊAYA.

ALHAMDU LILLAH 😊An buɗe sabuwar Tsangayar da Gwamnatin Gombe ta ginawa ƴan uwa dake Bojude Gombe State, Domin Haɓaka Kar...
27/02/2026

ALHAMDU LILLAH 😊
An buɗe sabuwar Tsangayar da Gwamnatin Gombe ta ginawa ƴan uwa dake Bojude Gombe State, Domin Haɓaka Karatun Alkur'ani mai girma, da nuna goyon bayansu ga ƴan uwa Almajirai makaranta Alqur'ani.

Mahalarta taro Manyan Alarammomi da yan uwa Almajirai da manyan sarakuna da manyan ma'aikatan Gomnati ne s**a smau halarta duk muna godiya

Duk wanda s**a bada gudumawa wajen samuwar irin wannan ayyukan Allah ya saka musu da Alheri, Allah ya bamu Albarkacin Al-Qur'ani. 🤲🏽💕

26/2/2026 Mu Koma Tsangaya ✍🏼✍🏽

30/12/2025
Shekaru 1,400 da s**a wuce a dai dai lokacin da Annabi Muhammad (S.A.W) yake raye ana kiyasi ko hasashen yawan mutanen d...
22/07/2025

Shekaru 1,400 da s**a wuce a dai dai lokacin da Annabi Muhammad (S.A.W) yake raye ana kiyasi ko hasashen yawan mutanen dake raye a duniya a lokacin basu wuce mutane miliyan 250 ba, a wancan lokacin mutanen dake raye a ban kasa basu wuce yawan mutanen Nigeria na yanzu (2025) ba.

Mutane suna rayuwa cikin wahala sosai a wancan lokaci, na matsalar abinci, ruwan sha, magani da tufafi. Amma duk da haka sai Annabi Muhammad (S.A.W) yazo da Theory din ayi aure a samu karin mutane masu tarbiyya, ayi yawa amma yawa mai tsari da lissafi. Saboda Allah ne ya aiko shi kuma shi (Ubangiji) yasan abinda ya ajiye domin rayuwar mutane a wannan duniyar.

Ba don yawan da mutane s**a yi a duniya ba da ba'a gano Mineral resources dake cikin kasa ba, da ba'a san amfanin su sosai ba. Ba don yawan da aka yi ba da ba'a gano Man fetur da amfanin sa ba. Ta dalilin Man Fetur an samu biliyoyin mutane da suke rayuwa karkashin harkar Man Fetur, tun daga ma'aikatun Man Fetur kamar NNPC, OPEC da sauran su. Wanda a zamanin da Manzon Allah yake raye babu su.

Shekaru 30 da s**a wuce babu wanda yasan sana'ar siyar da Katin waya (Recharge card) Airtime, Data da sauran su, amma a yau ta zama hanyar Abincin miliyoyin mutane, wannan budi ne da Allah yayi wa bayin sa.
~ Ada babu sana'ar gyaran waya, computer 🖥️, aikin wutar lantarki, kera motoci, da sauran aiyukan da duniya bata wuce shekaru 200 da fara yinsu ba.

Idan ka zuba Ido zaka cewa duk lokacin da mutane s**a kara yawa a duniya zaka ga Ubangiji yana kara buɗe musu kofofin da zasu samu hanyar rayuwa.
Masana suna cewa akwai abubuwan amfani a cikin kasa wadanda har yanzu duniya bata fara tono su ba, kuma ana bukatar su, kuma kayan kudi ne kayan arziki sosai, sai nan gaba.

A yau ana maganar mutanen duniya sun kai mutum biliyan 8. Wannan yana nuna maka Allah ke azurtawa kuma shi kadai yasan irin abinda ya ajiye a cikin wannan duniyar domin bayin sa.
Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Our Group:
https://chat.whatsapp.com/IiC1CrDCfHTAd0btoNscBW?mode=ac_t

13/03/2025

Abakar A, Nigerian Army 🪖 cikin Salon Murya mai Daɗi (Like Yahuza Bauchi Voice) yana karanta Alqur'ani Mai Tsarki.

30/01/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN🥺

Mutanen garin Azare sun wayi gari da ibtila'in gobara da ta faru a Tsangayar Makaranta Alƙur'ani da ke Nitel kusa da gidan Dallatun Katagum Marigayi Alh. Adamu Kuda.

Gobarar ta cinye kusan dukkanin wani abu mai amfani a Tsangayar, babban abin alhinin shi ne na rashin wasu daga cikin Almajirai mutum 2 da gobarar ta cinyesu. Da wannan muke addu'ar Allah ya amshi shahadarsu, yasa Alƙur'ani ya cece su Amin.

Ƴan uwa muna muku fatan Alkairi, Godiya ta musamman a gare ku.Malaman mu da s**a rasu Allah ya jiƙan su da Rahmah Don Is...
20/12/2024

Ƴan uwa muna muku fatan Alkairi,
Godiya ta musamman a gare ku.
Malaman mu da s**a rasu Allah ya jiƙan su da Rahmah Don Isar Annabi ﷺ da Alqur'ani ♥️

Abdurrahaman DantineGubuchi, Onya Tochukwu, Mustapha Sulaiman, Abubakar Sani, Usman Abdulbasir, Abdullah Hamxa, Ys Yk, Musa Abdullahi, Malan Harouna, Rabiu Sunusi, Shafiu Boss, Mohammed Buba, Dahiru Umar, Abdulrazaq S Yusuf, Alkasim Alkasim, Princess Last Born Abubakar, Badamasi Muhammad K-t, Mustafa Yakuba, Abdulahi Amiru, YUSUF MUHAMMAD, Razak Ibrahim, Abdulmudallif Muhammed Aliyu Gwarabjawa

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN.😭😭Yanzu muke samun labarin rasuwar Baba Gwani Lawi Gwani Ɗan zarga, ya rasu ne bayan f...
17/12/2024

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN.😭😭

Yanzu muke samun labarin rasuwar Baba Gwani Lawi Gwani Ɗan zarga, ya rasu ne bayan fama da jinya.

Haƙiƙa duniyar makaranta Alƙu'rani mun yi babban rashi, domin Gwani ya ƙarar da rayuwar sa wajan karatun Alƙur'ani da karantar da shi da gwagwarmayar a kan Alƙur'ani.

muna addu'a Allah Subhanahu wata'ala ya ji kansa da rahma ya kyauta namu zuwan, hidimar da ya yi wa Alƙur'ani Allah ya sa ya ɗauka acan.

Za a sanar da lokacin Jana'izar sa nan bada jimawa ba in sha Allahu.

Muna miƙa sakon Ta'aziyya ga ƴaƴa jikoki iyalai yan'uwa Almajirai na rashin wannan bawan Allah, Allah ya bada haƙuri. 😭

Yasir Gwani Badamasi

15/11/2024

Daga wajen Addu'ar Uku

📍 Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre

ALLAHU AKBAR 😭😭😭An gabatar da Jana'izar Gangaran Baba Gwani Sani Gombe a yau Laraba (Jumada auwal 12/1445_hijra) = Novem...
14/11/2024

ALLAHU AKBAR 😭😭😭
An gabatar da Jana'izar Gangaran Baba Gwani Sani Gombe a yau Laraba (Jumada auwal 12/1445_hijra) = November 14/2024 Kamar yadda Addinin Islama ya tanadar da Misalin ƙarfe 11:00am.
Amma Ranar Talata Allah yayi mai Rasuwa
Shi ne Mamallakin Fitacciyar Tsangayar nan (TSANGAYAR GWANI SANI GOMBE)

Wadda daga baya Mai Girma Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya. ya sabunta Ginin da Kuma Sunan Makarantar Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre
Wallahi Duniya tayi babban rashi na Jigo a Fannin Alqur'ani... Muna yiwa mutanen ƙasar Gombe da Ƴan uwa na ƙasa Nigeria da Ƙetare ta'aziyya.

Baba Gwani ya sha fama da Rashin Lafiya kafin Rasuwar sa, Allah ya Jiƙansa da Rahmah, Allah ya Gafarta masa, Allah ya Haskaka Makwancin sa ya sada shi da Annabin Rahmah don Matsayin Annabi ﷺ da Alqur'ani.

Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raji'un 😢

Malamin Bahaushe:Jinka yafi Ganin ka Malami bafaden Allah,da Fankama aka fiku ba Tarin Ilimi ba, ka musuluntar da Bayahu...
21/09/2024

Malamin Bahaushe:
Jinka yafi Ganin ka Malami bafaden Allah,
da Fankama aka fiku ba Tarin Ilimi ba, ka musuluntar da Bayahude ka Shiryar da Bamaguje ka Shayar da Bayerabe ka Ilmantar da Balarabe.

Ka kaɗai ne mai bada Ilimin da ke ratsa Zuciya Idaniya ta zubar da Hawaye, Duk mai hasken zuciya sai so haɗuwa da kai, kuma yaso yaji Muryar ka mai Amon Gwala-gwalai da Lu'ulu'un Kalmomi masu tafiyar da Zuƙata...

Prof Sheikh Umar Sani Fagge
Mu Koma Tsangaya
Ahmad Khamis Alhasand

Address

Army Barracks Road, Yelenguruza
Gombe
760233

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Gombe Almajiri Integrated Qur'anic Education Centre:

Share