Dahiriyya media news

Dahiriyya media news Muna godiya masoya shehu

RAMADAN TAFSEER 2023!!! MAULANMU SAUTUL ISLAM Sheikh Dahiru Usman Bauchi ,OFR (LISANUL FAIDHA) Yana farin cikin gayyatar...
15/03/2023

RAMADAN TAFSEER 2023!!!

MAULANMU SAUTUL ISLAM Sheikh Dahiru Usman Bauchi ,OFR (LISANUL FAIDHA)

Yana farin cikin gayyatar Yan'uwa Musulmi Zuwa Buɗe Tafsirin Alqur'ani Mai Girma.

Wanda Maulana Sheikh,Yake gabatar wa duk shekara a Jihar Kaduna.

Insha Allahu za'ayi Na Bana kamar haka:-
Rana:- LARABA 22-03-2023

Lokaci: karfe 4:00 na yamma
Wuri:- Masallacin Juma'a Na T/Wada Kaduna

Sanarwa daga:-
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi
(Chairman Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation)

Allah yakaimu lafiya ya kuma bada Ikon zuwa
Ameen thumma Ameen.

27/12/2022

Muna son chanjawa wannan shafi suna,sbd wasu dalilai.Ku bamu sunan da kuke so musaka ajiki.🙏

• Shehu Dahiru Usman Bauchi (RTA) Yana Cewa: • “Wallahi Jama'a Su Dinga Girmama Annabi Duk Abinda Ya Shafi Annabi A Girm...
23/09/2022

• Shehu Dahiru Usman Bauchi (RTA) Yana Cewa:

• “Wallahi Jama'a Su Dinga Girmama Annabi Duk Abinda Ya Shafi Annabi A Girmama Shi, Kowa Ya Fadi Maganar Da Zata Raba Ka Da Annabi Ka Rabu Da Shi Ka K**a Annabi Ƙam-ƙam.

• Duk Abinda Allah Ya Ba Mutane Ba Abinda Ya Ba Su Fiye Da Abinda Ya Bai Wa Masoya Annabi Muhammad (Salawatullahi Wasalamuhu Alaihi Wa'alihi Wasallam).

• Idan Mutane Sun Fi Ka Ilimi Kai Ƙoƙari Ka Fi Su Son Annabi In Mutane Sun Fi Ka Kudi Kai Ƙoƙari Ka Fi Su Son Annabi In Mutane Sun Fi Ka Mulki Kai Ƙoƙari Ka Fi Su Son Annabi...”

• Allah Ya Ƙara Wa Shehu Lafiya Da Tsawon Kwana Mai Albarka Alfarmar Annabi (Salãmullah Alaihi Wa'alihi Wasallam)

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A DuniyaDaga Aminiya 2/9/2022 ✍️.Fitaccen ...
02/09/2022

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

Daga Aminiya 2/9/2022 ✍️.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.

Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 98 a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da s**a haddace Alkur’ani.

A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda s**a karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.

Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne s**a haddace Alkur’anin

Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass

Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.

A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.

To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.

“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.

Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe.

“An haife ni ne a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira, a ranar Laraba.”

Yadda na mayar da karatun Alkur’ani sana’ata’
Ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a rayuwarsa shi ne irin yadda ya mayar da Alkur’ani sana’arsa da kuma yadda ya rungumi Darikar Tijjaniya ta zama rayuwarsa.

“A duk lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karatun Alkur’ani da karanta Salatul Fatihi da tasbihi da istigfari da salatin Annabi (SAW) da sauran zikirori,” in ji shi.

Kwarewar Sheikh Dahiru Bauchi

Da aka tambaye shi kan fannonin ilimin da ya fi kwarewa, shehin malamin ya ce, “Na yi dukkan karatuna na addini a karkashin kulawar mahaifina, har na haddace Alkur’ani kuma ta hannunsa ne na karbi Darikar Tijjaniya.

“Shi mahaifina ya karbi Darikar Tijjaniya ne ta hannun wani mutum mai suna Alhaji Gwani Abba, daga baya sai mahaifina ya ba ni izinin na tafi duk inda nake so domin zurfafa ilimina na addini da haddar Alkur’ani mai girma.

“Bangaren da na fi kwarewa sosai shi ne Alkur’ani, daga nan kuma sai bangaren Tafsiri, a nan malaman Tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri inji su.

“Sai kuma bangaren Ma’arifa, ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin (gyaran) zuciya wanda ake kiran sa Tlimin Tarbiyya.

“A nan ma masu irin ilimin kan ce ina da sani a fannin. Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangare.

“Sauran ilimomi kuma ina tattabawa, su Hadisi da Lugga da Li’irabi da Tasrifi da Fikihu, duk ina tattabawa,” inji shi.

‘Dalilin da nake buga misali kan duk tambayar da aka yi min’
Da aka tambayarsa cewa jama’a na mamakin yadda idan aka yi masa tambaya sai ya ba da misali kafin ya bayar da gundarin amsar, sai ya ce, “Wato shi buga misali wata runduna ce ta Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane.

“Idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su.

“Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da matukar muhimmaci wajen ba da amsa.”

Shehin malamin ya zama masanin Tafsirin Alkur’ani Mai Girma wanda ya samu lambobin yabo a wannan bangaren.

Ya kuma samu digirin girmamawa a bangarori daban-daban a Najeriya da ma kasashen waje.

Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi lambar yabo ta Digirin girmamawa, sannan Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR.

Nasarorin Sheikh Dahiru Bauchi

Ga wasu daga cikin nasarorin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya samu a tsawon shekarunsa:

1, Ya musuluntar da dubban mutane

2, A duk lokaci bayan lokaci yakan karanta Alkur’ani kuma yana yin saukar Alkur’ani a kwana biyu

3, Ya ba da lazumin Darikar Tijjaniyya wa dubban mutane da dama a fadin duniya

4, Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1500 a Najeriya da sassan Afirka

5, Sama da mutum 140,924 sun haddace Alkur’ani a makarantunsa a fadin Najeriya

6, Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya

7, Mutum ne mai kishin kasarsa Najeriya wanda aduk lokacin da ya bude baki zai yi addu’a sai ya roki Allah Ya ba kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali

Bugu da kari, malamin yana cikin wadanda s**a fi kowa dadewa suna tafisirin Alkur’ani da watan azumin Ramadan.

Masallacin da yake tafsirin da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna, na daya daga cikin manyan masallatan da ke cikin garin, kuma za a iya cewa a tsawon shekaru, malamin yakan zauna a garin kusan fiye da a ko ina.

Wani bincike da wani wanda yayi Nazari kan rayuwar malamin ya kuma rubuta littafi a kansa mai suna Shehu Dahiru Bauchi Ginin Allah, shekaru uku da s**a wuce, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, ya ce

Daya daga cikin almajiran shehin, Mallam Ahmad Tijjani Kolo, ya ce a yanzu an sami karin mahaddata a cikin zuri’arsa, inda yanzu s**a doshi 300. Ya ce da wahala a sami mai irin wannan a tarihi.

Shugaban Kungiyar Daliban Sheikh Dahiru Bauchi, Mallam Ibrahim Imam Ismaila, ya ce a tarihi babu wanda ya taba samun irin baiwarsa.

‘Rayuwarsa gaba daya makaranta ce’

Shi kuwa Daraktan Wakafi a Hukumar Shari’a na Jihar Bauchi, Mallam Ahmad Tijjani Sa’id, ya ce rayuwar shehun malamin gaba dayanta makaranta ce.

Ya ce rayuwar malamin ta raya ilimi da kuma tarbiyyantar da al’umma, saboda a yau a raye a cikin malamai da ya yi tafiya daga Fataskum zuwa Filato a kafa don yada addinin Musulunci.

Ya kuma ce malamin ya yi tafiya daga Arewa har kasashen Kudu a kan jaki da doki don yada addinin.

Sannan ya yi tafiya a kan keke zuwa kauyuka da dama kamar Tafawa Balewa da yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma don yada addinin Musulunci.

‘Gidajensa 1,000 da ake zama kyauta’

Malam Ahmad Tijjani Sa’id ya ci gaba da cewa babu abin mamaki cikin sha’anin malamin kamar yadda yake daukar nauyi ba tare da jin tsoron hidima ba.

“Yana da gidaje fiye da dubu daya a fadin kasar nan, amma ba inda ake haya, bayin Allah masu neman ilimi yake zubawa a ciki kyauta.

“Jama’ar da yake ciyarwa Allah kadai Ya san adadinsu. A kullum idan Shehi zai fito zai sallami baki fiye da 3,000 da s**a zo ziyarar sa daga ciki da wajen Najeriya, kuma za ka samu dalibansa ya yi musu auren fari ya musu suna kuma bai gaji ba.

“Ya maka mace ta biyu ya dauki nauyinku. Ire-iren wadannan halaye na Shehi da wuya ka samu wanda zai iya yin haka.”

01/09/2022

Alhamdullah ta tabbata mauludin Shehu Tijjani Na qasa ajaharmu ta Gombe
24-9-2022
Muna godiya wa allah

GAYYATAR TARON ZIKIRIN JUMA'A A GARIN ABUJAMaulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi Tare da Maulanmu Sheikh Sharif Ibrahim Sa...
24/08/2022

GAYYATAR TARON ZIKIRIN JUMA'A A GARIN ABUJA

Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi Tare da Maulanmu Sheikh Sharif Ibrahim Sale Alhusain Maiduguri

Suna Gayyatar Yan'uwa Musulmai Ahhalullahi Shehunai Muqaddamai Zakirai Zuwa Gagggarumin Taron Zikirin Juma'a Na Sabuwar Shekara Hadi da Addu'a ta Musamman Don Neman Zaman Lafiya a Kasar mu Nigeria Baki

Wannan Gagggarumin Taron Zai Gudanane A Babban Birnin Tarayya Abuja

Ranar Juma'a 28/Muharram/1444 -- 26/Aug/2022

Lokaci:-- 04:30pm Na Yamma

Wurin Taro:-- Babban Masallacin Juma'a na Qasa Wato (Central Mosque Abuja)

Allah Ya Bada Ikon Halarta Ameen

Sanarwa Daga:-- Mu'assatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi

✍🏽 Khadimul Faidha Media Team Of Nigeria

-Istigfari (ƙafa 100)- Salatin Annabi (ƙafa 100)- Hailala (ƙafa 100)Wannan shine wuridin da ake karantawa a tijjaniyya k...
21/08/2022

-Istigfari (ƙafa 100)
- Salatin Annabi (ƙafa 100)
- Hailala (ƙafa 100)

Wannan shine wuridin da ake karantawa a tijjaniyya kullum safe da yamma. Annabi saw ne asalin wanda yayi umurni a rinƙa karanta su, kuma suna daga cikin azkaran da yake karantawa safe da yamma.

Kaima Kayi ƙoƙari ka rinƙa karantawa ko baka ɗariƙa, ka dai ji zikirori ne daga Manzon Allah saw ba Shehu Tijjani ya ƙirƙiro su ba, shi dai iyaka ya ƙarfafa sunnar ce ga mabiyansa.

Lokacin wautar da tunani ya wuce da cewa Shehu Tijjani ya ƙirƙiri sabuwar ibada.

GAREKU BAREBARIN SHEIHU!!!Halarar MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana farin Cikin Gayyatar Al'ummar Musulmi(Mu...
18/08/2022

GAREKU BAREBARIN SHEIHU!!!

Halarar MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana farin Cikin Gayyatar Al'ummar Musulmi(Musamman Malamai, Limamai, Khalifofi, Muridai, Zakirai, Zuwa Wajen Taron Zikirin Sabuwar Shekarar 1444Ah.

WANDA ZA'A GABATAR DA

*. Zikirin Juma'a,
*. Saukokin Al-Qur'ani.
*. Addu'o'i Na Musamman Wa 'Kasa Akan Lafiya Da Zaman Lafiya,

WANDA ZA'A GABATAR KAMAR HAKA

*. Juma'a(21-Ga Muharram 1444Ah) - 19-8-2022).

*. Lokaci: 'Karfe 04:30 Na Yamma.

*. Wuri: Fadar Mai Martaba Sarkin Lafia.

(Sanarwa Daga: Mua'ssasatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi)

ALLAH Ya Bada Ikon Halarta, Ka Zaunar Da 'Kasarmu Nigeria Lafiya, Ameeeeen

MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa:"...Idan Aka Sa Lura Siffar/Halittar 'DAN ADAM Surarsa Aka Kwaikwaya A...
18/08/2022

MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa:

"...Idan Aka Sa Lura Siffar/Halittar 'DAN ADAM Surarsa Aka Kwaikwaya Aka Ajiye Shi Ya Zama GWAMNATI(A Duk Fadin Duniya),

MISALI👇

KWANYARSA(Kwakwalwarsa) Nanne 'HEAD QUARTER' Na Kowacce Gwamnati, Head-Quarter Ita Take Da Iko Da Duk Jiki(Gwamnati) Gaba 'Daya,

Aikinta Ne Ya Sauko Zuwa ZUCIYA Nanne 'OFISHIN SAKATAREN GWAMNATI' Idan Huhu Ya Sheqo Numfashi Sai Zuciya Ta Tace,

Ta Fitar Da Mai Muni Ya Sake Shaqar Sabo, Jini Ya Biyo Ta Kwakwalwa Ya Bama Zuciya, Zuciya Ta Fesa Ma Jiki Gaba 'Daya,

Sai CIKI(Tumbi) Nanne 'CENTRAL BANK', Idan Ya Kar6a Sai Ya Tace Sai Ya Rabama Sauran Rassan Ga6o6i Sai Su Ci Gaba Da Aiki,

Sai FARJI/AL'AURA Nanne MA'AIKATAN ASIRI 'NATIONAL SECURITY',

Sai IDO Yana Sa Ido Akan Abinda Zai Cuci Gwamnati 'INTELLEGENT' Kenan,

Sai KUNNUWA Suna Saurara Su Ji Abin Da Zai Cuci Gwamnati Su Sanar Da Ma'aikatan Asiri(Intellegent),

Sai HANNUWA Da 'KAFAFU Nanne 'Karfin Gwamnati Yake Wato K**ar Su; Sojoji 'Yan Sanda, Alkalai, Gandurobobi, Immigration, Da Custom, Da Sauransu.

Mun Gode SHEHU(R.A)❤️🙏🙏🙏

ALLAH Ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA(R.A)🙏🙏🙏

Dahiriyyah media News
Othman Muhammad ✍

TA'AZIYYA!    TA'AZIYYA!!     TA'AZIYYA!!!Inna'lillahi Wa'ina'ilaihin Raji'un Thumma Ilaina Turja'u Astagfirullah Allah ...
17/08/2022

TA'AZIYYA! TA'AZIYYA!! TA'AZIYYA!!!

Inna'lillahi Wa'ina'ilaihin Raji'un Thumma Ilaina Turja'u Astagfirullah Allah Mun Tuba Daman Gare Ka Muke Baga Waninka Ba Ya Allahu Ya Haiyu Ya Kaiyimu Ya Gafaru Ya Zuljalali Wal'ikram Subhanaka Rabbana Ya Mallalahu Waladu

Oh Allah Maulaya Modibbo Ibrahim Jarkasa Babbar Gaba Cikin Mazan Failah Daya Diga Cikin Zaqaquran Haziqan Mazan Aiki Tafiya Ba Waige Cikin Allah Da Manzon Allah Da Shehu Na Tijjani Kudubul Wara Tijjani Da Sahibul Faidah Alhaji Ibrahim Niass R t a

Shehu Mutum Ne Wanda Baya Son Tashin Hankali Ko Cinzalin Wani Mutum Cikin Harka Shehu Mutum Ne Mai Matukar Haquri Da Aikin Bayi Shehu Mutum Ne Mai Tsantsene Cikin Cikin Dukkan Af'alnashi Shehu Mutum Ne Wanda Saidai Muce Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Samun K**arsa Gaskiya Abune Mai Matuqar Wahala Shehu Madallah Da Kai Aikin Garemu Wlh Bazai Fadu Ba Shehu Mungode Mungode Mungode Jazakallahu Bikairan

Hmm Rayuwace Daman Haka Ta Gada Babu Makawa Kowa Lokaci Na Jiran Shi Allah Sa Musamu Cikar Sa'a Irinta Shehu Modibbo Ibrahim Jarkasa Shehu Hakane Rabuwa Da Jasadinsa Wlh Baya Nufin Mun Rabu Da Kai Shehu Muna Nan Cikin Fadarka Wlh Bazamu Juya Baya Ba Da Himmarka Ya Maulaya Shehu Ibrahim Jarkasa R t a

Muna Mika Sakon Ta'aziyya Zuwaga Maulanmu Sayyadi Rasulullahi S a w Da Maulanmu Shehu Ahmadu Attijjaniyu R t a Da Maulanmu Sahibul Faidah Sahibul Waqqty Niass R t a Gamida Musulman Duniya Baki Daya Musamman Yan Uwa Tijjanawa Yan Faidah Allah Karawa Shehu Kusanci Bijahi Shugaba s a w

Amadadin Hadarar Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi R t a Qarqashin Jagorancin Maulana Shehu Mustapha Salihu R t a El-gombawiyu R t a

M Taheer Bayee
DAHIRIYYA MEDIA NEWS

Ƙungiyan Rabida Ta Malaman Musulunci Na Duniya Wanda Keda Cibiya A Kasar Saudiyya Zata Ƙulla Yarjejeniyar Aiki Tare Da K...
17/08/2022

Ƙungiyan Rabida Ta Malaman Musulunci Na Duniya Wanda Keda Cibiya A Kasar Saudiyya Zata Ƙulla Yarjejeniyar Aiki Tare Da Khalifa Sheikh Mahi Inyass RTA

A yau mataimakin shugaban ƙungiyar rabidatu alamil Islam, ƙololuwar ƙungiyar Malaman musulunci na duniya ya sauka ƙasar Senegal domin taron ƙulla yarjejeniyar aiki tare da ƙungiyar haɗin kan musulmai ta Afrika wanda Khalifa Sheikh Mahi Inyass RTA ke jagoranta.

Cikin waɗanda s**a tarbi babban baƙo daga filin jirgi a madadin Khalifa Mahi Inyass akwai Khadimul Faidha, Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA.

Ana sa ran gobe 17 ga watan Agusta za'a yi taron ƙulla yarjejeniyar a ɗakin taro na gidan Abdullahi Bayero dake Madinatu Kaulakh.

ABBAN BALKISU BAZA'A SANYA YA KAKE BABabban Goro Sai Magogin Karfi Cikakken Masani Mazan Faira Ance Damu Shehu Dahiru Na...
15/08/2022

ABBAN BALKISU BAZA'A SANYA YA KAKE BA

Babban Goro Sai Magogin Karfi Cikakken Masani Mazan Faira Ance Damu Shehu Dahiru Na Bauchi Amma Gaskiya Zance Ba Haka Yake Maulana Koda Inuwarsa Bata Sauka Ga Duniya Ba B***e Ayi Zance Jasadinsa Lissafin Baya Buga Rilajai Sun Sallama Masa Bayee Dahirul Madahuru Shehu Anata Zagaye Wai Ko Za'a Sanka Hmm Naga 'Yan Maza Sun Bar Takubai Sun Zo Niman Tuba Karatun Kurma Gane Shi Akwai Matukar Wahala Gaya Kudai Ce Shehu Dahiru

Anbuga Da Kai Anbarka Likkafani Mayafin Dole Kaike Raba Abunda Baya Rabuwa Maulaya Kowa Kagani Zacensa Yake Anyi Batun Anyi Batun Kowa Yayi Zugum Sai Saurara Ake Babu Ankasa Fadinsa Yaya Yake Agama Zagaye Zagaye Lamarin Saishiru Sanin Shehu Saidai Shehu Maulal Axeemu Haqiqaty Barhama Sautul Islam

M Taheer Bayee
DAHIRIYYA MEDIA NEWS

Address

Gombe

Telephone

+2347087655455

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dahiriyya media news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share