18/04/2021
Allahu Akbar malam Allah yabiya malam Amin summa Amin.
ABUBUWAN DA S**A FARU A CIKIN WATAN RAMADAN A TARIHI
Allah maɗaukakin sarki ya saukar da Alqur’ani Mai Girma a cikinsa. Kamar yadda ya zo a cikin suratul Baqara inda Allah ﷻ Yake cewa:
﴿ شَهْرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلْقُرْءَانُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٍ مِّنَ ٱلْهُدَىٰ وَٱلْفُرْقَانِۚ ﴾ ()
Ma’ana: “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu na shiriya da kuma rarrabewa.” (tsakanin daidai da ba daidai ba). Lallai haƙiƙa Allah ﷻ Ya zaɓi wannan wata daga cikin watanni Ya fifita shi a tsakaninsu, Ya zabe shi Ya saukar da Alqur’ani a cikinsa.
A cikinsa ne aka saukar da sauran littattafan da Allah ﷻ Ya saukar ga sauran Annabawa عليهم السلام, k**ar yadda aka ruwaito a hadisin Wasilatu Bn Asqa'i رضي الله عنه, ya ce Manzon Allah ﷺ ya ce, “An saukar da suhufi Ibrahim a dare na farkon watan Ramadan, an saukar da Attaurah a dare na shida (6) ga watan Ramadan, an saukar da Injila a sha uku (13) ga watan Ramadan, an saukar da Alqur’ani a ashirin da huɗu (24) ga watan Ramadan.” ()
A cikin watan Ramadan ne ake buɗe ƙofofin Aljannah.
A cikin watan Ramadan ake rufe ƙofofin wuta.
A cikin watan Ramadan ne ake ɗaure kangararrun shaiɗanu macuta.
A cikin watan Ramadan ne ake buɗe ƙofofin rahama.
A cikin watan Ramadan ne ake buɗe ƙofofin sama.
A cikin watan Ramadan ne mai kira yake kira yana cewa, “Ya kai mai nufin alkhairi ka gabato, ya kai mai nufin sharri ka ja da baya.” ()
A kowane dare akwai waɗanda Allah ﷻ Yake ‘yantawa ya tseratar da su ga barin shiga wuta.
Ana amsa addu'a a cikin watan Ramadan, kuma Allah ﷻ Ya ambata a cikin suratul Baqarah inda Yake cewa:
﴿وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِى عَنِّى فَإِنِّى قَرِيبٌۖ أُجِيبُ دَعْوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِۖ فَلْيَسْتَجِيبُوا۟ لِى وَلْيُؤْمِنُوا۟ بِى لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ﴾ ()
Ma’ana: “Idan bayina sun tambaye ka game da ni ka ce ina kusa, kuma ina amsa kiran mai kira idan ya kirawo ni, don haka su amsa min su yi imani da ni, domin su sami shiriya.”
An ruwaito daga Abu Sa'id Al-Khudri da Abu Hurairahh رضي الله عنهما cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “A kowane dare Allah ﷻ Yana ‘yanta bayi daga shiga wuta, kuma kowane bawa yana da addu'a da ake amsa masa.”
Watan Ramadan wata ne na zikiri, da istigfari, da salatin Annabi ﷺ, da karatun Alqur’ani da godiya ga Allah ﷻ. Domin Allah ﷻ Yana tsaka da yin bayani a game da azumi sai Ya ce:
﴿وَلِتُكْمِلُوا۟ ٱلْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا۟ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ ﴾ ()
Ma’ana: “Domin ku girmama Allah ﷻ saboda Ya shirye ku ko kwa gode masa.”
Watan Ramadan wata ne na haquri da juriya saboda hadisin nan na balaraben qauye wanda Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنهما yake cewa: Manzon Allah ﷺ ya ce, “Watan azumin Ramadan wata ne na haquri ne, saboda haka ake ce masa: shaharus sabari, da kuma yin azumin kwana uku a kowane wata yana tafiyar da nunkufurcin zuciya, wato suna cire tsatsar zuciya, su tsarkake ta ga barin munafirci da kafirci. Don haka babu makawa shi watan azumi wata ne na haquri, da juriya, da yarda da qaddarar da Allah ﷻ ya ɗora ma, yin haquri a kan biyayya gare shi da haqurin jin raɗaɗin yunwa da qishi da kuma qauracewa hane-hanen Allah ﷻ da bin umarninsa. Kuma Allah ﷻ Ya ce:
﴿إِنَّمَا يُوَفَّى ٱلصَّٰبِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ﴾ ()
Ma’ana: “lallai haƙiƙa ana cikawa masu haquri ladansu ba tare da lissafi ko bincike ba.
Azumin watan Ramadan yana kankare zunubai saboda hadisin Abi Hurairah رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ yana cewa; “Juma'a zuwa Juma'a, da azumi zuwa wani azumin, waɗannan suna kankare zunuban da suke tsakaninsu idan an nisanci manya-manyan zunubai.” ()
Watan Ramadan ana gafarta zunubai a cikinsa saboda hadisin Abi Hurairah رضي الله عنه wanda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.” ()
Watan Ramadan shi ne mafi girman lokaci da ake kankare zunubai a cikinsa, saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya hau kan mimbari sai ya ce amin, amin, amin, har sau uku, sai aka ce da shi, ya Manzon Allah ﷺ mun ga yanzu ka aikata wani abu wanda kafin yau ba mu ga kana aikata hakan ba? Sai ya ce, “Mala'ika Jibrilu ne ya zo ya ce da ni, a turmuza hancin duk wani bawan da watan Ramadan ya zo har ya fita bai yi aikin da zai shiga Aljannah ba, sai Jibrilu ya ce da ni ka ce amin, sai na ce amin. Sannan sai ya ce da ni a turmuza hancin duk wani bawan da aka ambace ni a gabansa amma bai yi min salati ba, sai ya ce ka ce amin, sai na ce amin. Sannan sai ya sake cewa a turmuza hancin dukkan wani bawa da ya riski rayuwar mahaifansa su biyu, ko kuma ɗaya daga cikinsu amma har s**a mutu bai yi musu biyayyar da za a sa shi a cikin Aljanna ba. Sai ya ce ka ce amin, sai na ce amin.”
Wanda duk Allah ya sa ya riski zagayowar watan Ramadan yana da ransa da lafiyarsa, haƙiƙa za a xaukaka masa darajoji saboda hadisin Ɗalhatu Bn Ubaidullahi رضي الله عنه inda yake cewa, wasu mutane sun zo wajen Manzon Allah ﷺ sai s**a musulunta gabaɗayansu, sai dai ɗaya daga ciki ya fi yawan ibada a kan ɗayan, to sai s**a fita yaqi, sai ɗaya daga cikinsu (mai yawan Ibadar) ya yi shahada, ɗayan kuma sai bayan Shekara sannan ya mutu, sai Xalha رضي الله عنه ya ce, sai aka nuna min a cikin barci ga ni a qofar Aljanna, sai na gan su duk su biyun a qofar Aljanna, sai wani ya fito daga cikin Aljannar ya yi izini ga wanda ya mutu daga ƙarshen ya fara shiga Aljannar, sannan na farkon da ya yi shahada shi ma aka yi masa izini ya shiga. Sannan sai ya dawo zuwa gare ni sai ya ce, ka koma domin kai ba ka mutu ba, ballantana a shigar da kai.
Sai Ɗalhatu رضي الله عنه ya wayi gari yana ba wa mutane wannan labarin sai mutane s**a yi mamaki da wannan mafarkin.
Daga nan sai labarin ya jewa Manzon Allah ﷺ, sai ya ce, “Mamakin me kuke yi? Wannan na farkon ya fi tsananin ibada, a kan na biyun, sannan kuma ya yi shahada, amma shi wancan na ƙarshen shi ya fara shiga Aljannah, shin ba ya rayu a bayansa Shekara ɗaya ba? Sai s**a ce eh, shin ba ya riski watan Ramadana ba? S**a ce eh, ba ya yi sAllah iri kaza da iri kaza har na tsawon Shekara xaya ba? Sai s**a ce haka ne ya Manzon Allah ﷺ, sai ya ce, abin da yake tsakaninsu na daraja k**ar nisan sama ne da kasa, tun da shi Allah ya yi masa tsawon rai har ya riski Ramadan.” ()
Yin umara a cikin watan Ramadan daidai yake da k**ar ka yi hajji tare da Manzon Allah ﷺ saboda hadisin Abdullahi Ɗan Abbas رضي الله عنه da ya ce, haƙiƙa Manzon Allah ﷺ ya cewa wata mace daga cikin mutanen Madina da ake ce mata Ummu Sinanin “Me ya sa ba ki yi aikin hajji tare da mu ba? Sai ta ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ muna da raquma (taguwoyi) guda biyu a gidanmu, ɗaya mai gidan namu ne ya tafi aikin hajji a kanta shi da ɗansa, ɗayar kuma ita s**a bar mana a gida muke ban ruwa da ita. Sai Manzon Allah ﷺ ya ce mata, yin umara a watan azumi daidai yake da yin aikin hajji tare da ni.”
A wata ruwayar ta Muslim ya ce mata, “Ki je ki yi umara a watan Ramadan domin yin umara a watan Ramadan daidai yake da yin hajji tare da ni.”
Haka kuma a wata ruwayar ta Bukhari sai ya ce mata, “Idan watan Ramadan ya zo ki je ki yi umara a cikinsa, domin umara a cikin Ramadan k**ar hajji ce.” Amma fa ladan hajjin ake samu ba wai farillar hajjin ce take sauka daga kan wanda bai yi ta ba.
Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana daga cikin siddiqai da shahidai, saboda hadisin Amru Bn Murra Al-Juhani ya ce, wani mutum ya zo wajen Ma’aikin Allah ﷺ daga qabilar Qudha'a, sai ya ce, ya Manzon Allah ﷺ ka bani labari idan na shaida babu abin bautatawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammadu ﷺ Ma’aikin Allah ne, na yi salloli biyar, na ba da zakkah, sannan na yi azumin watan Ramadan ni waye? Sai Ma’aiki ﷺ ya ce, “Kana cikin siddiqai da shahidai.” ()
Haka kuma yin azumin watan Ramadan yana jawo wa mutum shiga Aljannah saboda hadisin Jabir رضي الله عنه.
Yin qiyamul laili a cikin watan Ramadan da imani da neman lada ana gafarta zunubi da shi, saboda hadisin Abu Hurairah رضي الله عنه da ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya yi tsayuwar Ramadan da imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na daga zunubansa.” ()
Watan Ramadan wata ne na sallar tarawihi, ita kuma sallar tarawihi sallah ce wadda ba a yin ta sai a cikin watan Ramadan, saboda hadisin Ummina A’ishah رضي الله عنها ta ce, Manzon Allah ﷺ ya fito a cikin tsakiyar dare sai ya yi salla a masallaci sai mutane s**a bi shi wannan sallar sai aka wayi gari ana ba da labarin wannan sallar da Ma’aiki ﷺ ya yi a cikin dare, da dare na gaba ya zo sai mutane s**a taru fiye da dare na farko, sai ya yi sallah da mutanen sai aka wayi gari labari ya ci gaba da yaxuwa, sai dare na gaba ya zo mutane s**a sake taruwa a wannan daren fiye da na baya sai Manzon Allah ﷺ ya yi musu sallah, a dare na huɗu sai masallaci ya cika da jama'a sai Ma’aiki ﷺ bai fito ba, har mutane s**a ce lokacin sAllah ya yi, Manzon Allah ﷺ bai fito ba, har sai da lokacin sallar asubah ya yi.
Bayan an yi sallar asuba sai Ma’aiki ﷺ ya fuskanci mutane ya yi godiya ga Allah ﷻ ya yi kirari a gare Shi, sai ya ce, bayan haka ya ku mutane al'amarinku bai vuya gare ni ba, sai dai na ji tsoron kada a wajabta muku wannan sallah ne ku kasa yin ta shi ya sa ban fito ba.” Wannan kuwa ya faru ne a cikin watan Ramadan. ()
Wanda ya yi sallar tarawihi tare da liman sannan kuma ya lazimci wannan jam'in har sai da liman ya qare sallar, za a rubuta masa lada k**ar ya yi tsayuwar daren ne gaba ɗayansa.
Saboda hadisin Abu Zarrin رضي الله عنه da yake yin bayani game da tsayuwar watan Ramdan, sai ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Wanda ya tsaya tare da liman s**a yi sallar tarawihi har aka gama, to za a rubuta masa k**ar ya tsaya a gaba ɗayan wannan daren ne yana sAllah.”
A wata ruwayar kuma ya ce, “Za a rubuta masa ya tsaya da sAllah a wannan daren dukkansa.” ()
Watan Ramadan wata ne na samun nasara a kan maqiya saboda addu'o'in da ake yi domin samun nasara, domin a zamanin Ma’aiki ﷺ, musulmai sun fita yaqi su ɗari uku da 'yan kai, mutum biyu ne a kan doki; saba'in kuma suna kan raquma, amma duk da haka Allah ﷻ ya ba su nasara, a kan mushrikai wanda adadin su ya kai kimanin mutum (1,000), wasu suna kan dawakai, guda ɗari bakwai kuma (700) suna kan raquma.
Wannan shi ne yaqin Badar, kuma ya faru ne a cikin watan Ramadan a Shekara ta biyu bayan hijrah.
Haka nan Allah ya taimaki muminai a cikin yaqin Fatahu Makkah, shi ma da aka yi shi a cikin watan Ramadan a Shekara ta takwas (8) bayan hijrah, domin Manzon Allah ﷺ ya shiga garin Makkah ba tare da yaqi ba, ya yi kuma nasara. ()
Sannan ana ninninka lada da kuma ninninka sak**akon duk wani abin alkhairi da aka aikata a cikinsa, Manzon Allah ﷺ ya fi kowa alkhairi ya fi kuma ninka alkhairin da yake yi a cikin watan Ramadan a ya yin da ya haɗu da Mala'ika Jibril. Manzon Allah ﷺ ya fi kowa alkhairi da kyauta fiye da iska ko tatacciyar iska mai wucewa.” () Ma’ana, saboda yawan kyautarsa da alkhairinsa.
Watan Ramadan wata ne na karanta Alqur’ani, Jibrilu yakan zo wajen Ma’aiki ﷺ a cikin kowacce Shekara a cikin watan Ramadan suna yin bitar karatun Alqur’ani tare. Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyautar mutane, kuma ya fi yin wannan kyautar tasa ne a cikin watan Ramadan a yayin da ya haɗu da Jibrilu, lallai haƙiƙa Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyauta fiye da iska wadda ta taso. ()
Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci, wanda Musulunci ba ya cika sai da shi, haka kuma imanin bawa ba ya cika sai da shi, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Umar رضي الله عنه inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce, “An gina Musulunci a bisa abubuwa biyar;
Na farko: Shaidawa babu abin bautatawa da gaskiya sai Allah ﷻ, sannan kuma Annabi Muhammadu ﷺ Manzon Allah ne.
Na biyu: Tsayar da sAllah.
Na uku: Bayar da zakkah.
Na huxu: Azumin watan Ramadan.
Na biyar: Aikin hajji ga wanda ya sami iko.” ()
Shi watan Ramadan wata ne na i’itiƙafi da lazumtar masallaci da niyyar neman kusanci ga Allah ﷻ, dalilin yin nafilfili da karatun Alqur’ani da ambaton Allah ﷻ da salati ga Annabi ﷺ da yin tasbihi da istigfari a cikinsa, shi ne hadisin Nana A’ishah رضي الله عنها inda take cewa, “Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin i’itikafin goman ƙarshe na Ramadan.”
Ma'ana: ya kasance yakan tare a masallaci yana ibada a goman ƙarshe har Allah ﷻ ya karvi ransa. Daga nan kuma matansa sun cigaba da yin hakan a bayansa. ()
Akwai kuma hadisin da ya zo daga Abu Hurairah رضي الله عنه cewa, Manzon Allah ﷺ yana yin I’itikafi a cikin watan Ramadan na kwana goma, amma a Shekarar da Allah ﷻ ya karɓi ransa ya yi I’itikafin kwana ashirin (20). ()
Don haka, ya k**ata 'yanuwa musulmai a riqa qoqari a zage dantse idan watan Ramadan ya zo a qara qoqari fiye da wanda ake yi kafin zuwan watan Ramadan wajen yawaita karatun Alqur’ani da sAllah da salati ga Annabi ﷺ da istigfari da yawaita kyauta da sadaka da sa da zumunci da mak**antansu.
Watan Ramadan wata ne na ijtihadi, wata ne na qoqari, wata ne na zage ɗantse a wajen qara yawaita ibadu, domin Manzon Allah ﷺ ya kasance idan goman ƙarshe na Ramadan ya zo yana raya darensa, ya tashi iyalansa su ma su raya darensu, sannan ya qara xaura gyautonsa, wato ya ci xamara ya dage wajen yawaita ibada.
Watan Ramadan wata ne na ijtihadi da zage ɗantse, domin neman dacewa da daren lailatul qadari, wanda wannan dare shi kaxai ya fi dare dubu (1000) wanda ba na lailatil qadari ba. Wata dubu shi ne Shekara tamanin da uku (83) da 'yan kai. Wanda in mutum ya dace aka karvi ibadarsa zai sami wannan ladan. Ma’aiki ﷺ ya ce “Ku nemi daren lailatil qadari a cikin goman ƙarshe na Ramadan.”
A wata ruwayar yake cewa, “Ku nemi lailatil qadari a dare na ashirin da huɗu.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Shi lailatil qadari ana iya samunsa a daren ƙarshe ko a bakwai na ƙarshe.” Don haka sahabbai suke dagewa wajen qoqarin nemansa.
Ummina A’ishah رضي الله عنها ta ce, na tambayi Manzon Allah ﷺ sai na ce, ya Ma’aikin Allah ﷺ idan na san wannan shi ne daren lailatil qadari me ya k**ata na roqa? Sai Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ki ce ya Allah kai ne mai afuwa kana son yin afuwa kayi min afuwa.” ()
Karya azumin Ramadan da gangan ba tare da wani uzuri ba, yana daga cikin manyan laifuka, saboda hadisin Abu Umamah رضي الله عنه wanda ya ce, Manzon Allah ﷺ ya ce, “Ina barci sai wasu mutane biyu s**a zo s**a tashe ni, s**a k**a dantsena s**a tafi da ni wani dutse mai nisa, sai s**a ce da ni in hau sai na ce musu ai ba zan iya hawa ba, sai s**a ce za mu sauqaqa maka hawan, sai na hau, ina tsakiyar dutsen nan sai na jiyo wata murya mai tsanani, sai na ce waɗannan muryoyinsu waye? Sai s**a ce wannan ihu ne da kururuwar 'yan wuta. Sannan s**a tafi da ni sai muka tarar da wasu mutane an rataye su, a kan agarorinsu, an tsattsaga kumatunsu, ga shi kuma jini yana fita ta wajen, sai na ce, su waye waɗannan? Sai aka ce su ne masu karya azuminsu kafin lokacin azumin ya qare.”
Waɗannan su ne darajoji da mutum zai samu idan ya tsaya ya kula da azumin watan Ramadan da kyautatawa da kuma kyakkyawar niyyah.
Allah ya amsa mana dukkan buƙatu na alkhairi ya tsare dukkan sharri da abin ƘI