17/02/2025
TARIHIN HARUNA UJI
An haifi Alh. Haruna Uji a Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.
Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta a Gandun sarki, daga nan s**a tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.
Bayan nan s**a bar Birniwa s**a dawo Hadejia s**a ci gaba da karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara musamman wadanda s**a zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu. Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu karatu mai dama.
Hadejia A yau!
1.1, ASALIN INKIYAR HARUNA UJI..
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA, Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin Iya Kura, Mijin Iya Kura’ A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka daina ake cewa Uji.
1.11, SIFFAR HARUNA UJI.
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga magana (Idanu) haka kuma, ma’abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka ‘yar shara, musamman lokacin zafi.
Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara’a da kyauta, domin abin hannunsa bai r