IDRIS BOYI FANS

IDRIS BOYI FANS Education

05/06/2020

BARKANMU DA ASUBA

Labaran Safiyar Jumma'a 05/06/2020CE - 13/10/1441AH. Cikakkun labaran

An samu karin mutane 350 da s**a kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 11,516.

Gwamnatin tarayya za ta gina wa 'yan gudun hijra 500 a jihohi 4 na Arewacin Najeriya.

Gwamnatin jihar Katsina ta sake bude kasuwanni ta umurci ma'aikata su koma bakin aiki.

'Yan jam'iyyar APC 10,000 sun sauya sheƙa sun koma PDP a jihar Kwara.

Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da cewa duk masu dauke da Coronavirus a jihar sun warke.

'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a wani fito-na-fito da s**a yi a jihar Zamfara.

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta k**a wata mota makare da giya a jihar.

Gwamnatin Tarayya za ta biya naira bilyan 1.7, ladar zanen taswirar sabon titin saukar jirage a filin Abuja.

Majalisar Dattawa na binciken yadda dala bilyan 3.3 da s**a bace a CBN.

Kasashen duniya sun caccaki Amurka kan kashe George Floyd.

Mutum 7,000 sun tsere daga sansanin 'yan gudun hijira a Nijar.

04/06/2020

Labaran Safiyar Alhamis 04/06/2020CE - 12/10/1441AH. Cikakkun labaran

An samu karin mutum 348 da s**a harbu da cutar Coronavirus. Jimillar masu cutar a Najeriya ya kai 11,166

An saki Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari.

Boko Haram sun yi garkuwa da mutane 4 da s**a hada da jami'an jin kai 3 da soja daya.

Kungiyar SERAP ta kai karar Shugaba Buhari gaban majalisar dinkin duniya kan rage kasafin kudin ilimi da na lafiya.

'Yan bindiga sun kashe mutane 9, sun raunata wasu da dama a sabon harin da su ka kai a Kaduna.

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta bude filayen jiragen sama guda 5 a Najeriya.

Sojoji sun k**a mutane 24 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Ondo.

Coronavirus: An sallami karin mutane 17 da s**a warke daga cutar a jihar Edo.

An kai hari sansanin sojojin sama na kasar Amurka da ke jihar North Dakota, inda aka kashe sojoji 2.

Kasar Qatar ta ce ba za ta yarda Isra'ila ta mamaye Zirrin Gaza ba.

Mutane 5 sun rasa rayukansu sak**akon kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

03/06/2020

BARKANMU DA ASUBA

Labaran Yammacin Talata 02/06/2020CE - 10/10/1441AH. Cikakkun labaran

Majalisar wakilai ta amince Shugab Buhari ya karbo bashin $22.7bn daga kasar waje.

CBN ya umarci bankuna su gaggauta mayar wa mutane kudin da s**a makale a ATM.

Covid-19: An yi wa mutane sama da 4,500 gwajin cutar a jihar Kano.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bukaci a rika yankewa masu fyade tsattsauran hukunci.

Kotu ta bayar da umurnin a saki Sanata Orji Uzor Kalu daga gidan yari.

Kungiyar IPMAN ta ce ba za ta iya sayar da litar man fetur a kan Naira 121.5 ba.

Kungiyar Boko Haram sun kashe fararen hula 5 a yayin da 9 s**a bace a Borno.

Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar girke sojoji a tarzomar da ake yi a kasar.

Dakarun Isra'ila sun k**a Falasdinawa 23 a Gabashin Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce adadin mutanen da cutar korona ta harba a nahiyyar Afirka ya zarta 150,000.

Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta zabi 'yan aikin sa kai don gwajin rigakafin cutar corona na kasar.

Let's join together to promote the level of education in our respective communities
21/02/2020

Let's join together to promote the level of education in our respective communities

11/02/2020
23/06/2017

Hi to you all

Address

Jahun

Telephone

+2347038133773

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IDRIS BOYI FANS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share