ILIMI KOGI NE

ILIMI KOGI NE Bamu yarda wani ya mana post na wani abu da baidaceba

Yakamata mu saba da ambaton ahlin annabi idan muna yimasa salati (allahumma salli ala sayyidina muhammadin wa'ala ahlihi...
21/08/2023

Yakamata mu saba da ambaton ahlin annabi idan muna yimasa salati (allahumma salli ala sayyidina muhammadin wa'ala ahlihi wasalim) 🙏🙏🙏

ABUBUWA 5 DA SUKE JANYO BALA'I ACIKIN AL'UMMAHadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)Yace Wa...
19/08/2023

ABUBUWA 5 DA SUKE JANYO BALA'I ACIKIN AL'UMMA

Hadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)

Yace Watarana muna zaune sai ga Manzon Allah (S.A.W) yazo wucewa, Yace " ya ku taron muhajirai! Akwai wasu abubuwa guda 5 idan al'umma s**a Jarabtu dasu!

Ina Roƙon Allah kada ku riske wannan Lokaci.

1⃣ Duk Al'ummar da s**a bayyana Alfasha! Tabbas zasu samu kansu cikin Annoba da yaduwar sabbin cututtukan da ba'a taɓa ganin su ba!

2⃣ Duk Al'ummar da suke tauye modu da sikeli! Tabbas zasu samu kansu cikin yanayi na fari (rashin ruwan sama), Tsadar Rayuwa da cutarwa daga azzaluman Shuwagabanni.

3⃣ Duk Al'ummar da s**a hana zakkar dukiyoyinsu! Tabbas Allah zai hanasu ruwan sama! Idan kaga Ruwa, an yine kawai saboda yara da dabbobi da suke rayuwa a cikinsu.

4⃣ Duk Al'ummar da s**a saɓa alkawarin Allah da Manzon sa! Tabbas Allah zai ƙasƙantar dasu a gaban abokan gabansu.

5⃣ Duk Al'ummar da Shuwagabaninsu basu hukunci da Littafin Allah, kuma suke chanza Abinda Allah ya sauƙar! Tabbas Allah zai sanya gaba, yaƙi da ganin Aibin Junansu a tsakaninsu.

Ibn Majah ne ya Rawaito Wannan Hadisin.

Dan Girman Allah acikin Waɗannan Abubuwa 5 wanne ne ba'a aikatawa a Nigeria? A hakan kuma muke jiran ganin dai dai

Allah kashiryemu ka gyara mana zukatanmu

~ Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Allah yasa mudace amen
Maryama Muhammad Abdullahi 😘

" Ya Ubangiji Ka Sauƙaƙawa Kowa akan Hanyar Neman Abincin Shi."
11/06/2023

" Ya Ubangiji Ka Sauƙaƙawa Kowa akan Hanyar Neman Abincin Shi."

21/05/2023

Duk sunan da za'a kira ka da shi, kimar sunan bai kai a ce ma MUSULMI ba.

-Sheikh Guruntum
© Ibrahim Usman

30/04/2023

Acikin surorin Alqur'ani
114
Rubuta sunan Surah daya
saboda Girman Allah🙏

 Wakee'u bin Jarrah Allah ya masa rahama yake cewa "Zakkar fidda kai ga watan Ramadhan kamar Sujudus sahwi ne ga sallah,...
29/04/2023



Wakee'u bin Jarrah Allah ya masa rahama yake cewa "Zakkar fidda kai ga watan Ramadhan kamar Sujudus sahwi ne ga sallah, tana cikace tawayan Azumi kamar yadda sujudus sahwi take cikace tawayan sallah"

تاريخ بغداد (٥٧٦/١١)

Muraja'armu ta yau: 06/10/1444 = 26/04/2023Surah: 2- Baqarah. Ayah: 135 - 141Allah ya bada ikon karantawa Mahaddacin Alq...
29/04/2023

Muraja'armu ta yau: 06/10/1444 = 26/04/2023
Surah: 2- Baqarah.
Ayah: 135 - 141

Allah ya bada ikon karantawa

Mahaddacin Alqur'ani

Address

Sabon Gari
Jalingo

Telephone

+2348101004527

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ILIMI KOGI NE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to ILIMI KOGI NE:

Share