08/09/2022
LABARI MAI KAYATARWA!!!!!
Wani mutum ne yashirya yin wata tafiya. Ya dauki matarsa da ’ya’yansa cikin motarsa s**a k**a hanya.
Ba su yi nisa ba s**a hadu da wani mutum tsaye a bakin hanya.
Ya daga musu hannu s**a tsaya, ya nemi su dauke shi.
Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?”
Ya ce, “Ni ne dukiya.” Nan take iyalin s**a dau shewar cewa ga abokin tafiya, maganin takaicin duniya.
S**a ce lallai a dauke shi su tafi tare. Dama motar irin babbar Jif din nan ce mai yalwar mazaunai wato (family car), sai s**a dauke shi
s**a tafi.
Suna yin gaba kadan sai s**a tarar dawani mutumin, shi ma a bakin hanya yana dagamusu hannu, sai
maigida ya tsaya.
Ya tambaye shi: “Wane ne kai?”
Ya ce: “Ni ne sarauta da matsayi.
Iyalan na jin haka s**a ce a dauko shi. Domin babu abin da yin sa zai
gagarimutum a duniya, muddin yana da sarauta da matsayi.
Shi ma s**a dauke shi s**a wuce.
Suna kara gaba kadan sai ga wani mutumin tsaye a gefen hanya, shi ma ya daga musu hannu s**a tsaya.
Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?”
Ya ce: “Ni ne Addini.” Maigida ya waiwayi iyalansa, sai ya ga sun yi jugun-jugun cike da damuwa.
Tun kafin ya nemi shawararsu s**a ce: “Wannan ba abokin
tafiya ba ne. Takura mana zai yi da hukunce- hukuncensa na halal da haram,ya hana mu more rayuwarmu. Ya dai jira nan gaba ma dawo mu
dauke shi bayan mun gama more jin dadin rayuwarmu.”
Maigida ya yarda da shawarar iyalansa, s**a wuce s**a bar
Addini nan tsaye, suna taQama da wadatar dukiya da alfarmar sarauta da matsayi, har s**a ci karfin tafiyar daza su yi.
Suna cikin tafiya sai s**a iso wani wurin binciken ababen hawa,
( cheking Point ). S**a tsaya don suma a duba su. Sojan da ke bincike yace da maigida: “Kai fito mu tafi, tafiyarka ta kare daga nan!” Maigida ya ce: “Kai
kuwa wane ne kai?”
Yace: “Ni ne mala’ikan mutuwa.Ina bincike ne a kan addini. Kai kuwa
ba ka da shi.” Maigida ya ce: “Affff", ai na baro shi a hanya. Bari na koma na dauko shi.”
Mala’ikan mutuwa ya ce: “Ai wannan damar ta wuce ka har abada!” Mai