05/07/2019
JAM’A MU KULA DA WANNAN.
Wani yaro yazo wajen baban sa yace masa: "Baba ni bazan kara zuwa masallaci ba.!”
Sai Baban yace: "Ko meye dalilin ka.?”
Sai yaron yace: "Na ga mutane da dama suna latsa wayoyin su alhali ana huduba, wasu kuma suna gulma, wasu suna games, wasu suna zaman da bai dace ba, kai da yawan su munafukai ne"
Sai Baban yayi shiru yace: "OK! Naji, ko zan sanya ka wani abu kafin ka yanke wannan hukunci na ka na karshe?".
Yaron yace: "To Baba babu matsala mene ne?"
Sai Baban yace: "Dauki wannan plate din ka cika shi da ruwa ka zagaye cikin masallacin nan sau uku kada kabari ruwan ko digo daya ya zuba".
Shikenan yaro ya aminta da abinda Baban sa ya sanya shi yayi, bayan wani lokacin sai yaron ya dawo yace ya kammala.
Sai Baban ya sake tambayar yaron wasu tambayoyi guda uku:
"1. Ko kaga wani yana dannan wayar 📱 shi?
2. Ko kaga wasu suna gulma?
3. Ko kaga wasu suna abinda bai dace ba?".
Sai yaron yace: "Banga wani yana danna wayar 📱 shi ba, ban kuma ga wasu suna gulma ba, b***e kuma ace naga wasu suna abinda bai dace ba, saboda na maida hankali na akan plate din ruwan kada ya zuba".
Sai Baban na shi yace da shi: "Toh duk lokacin da kaje masallaci, ka maida hankalin ka ga Ubangijin ka ba abinda Ubangijin ka ya halitta ba, ta hakanne zaka samu falalar zamewa a dakin Ubangijin ka".
Idan zaka shagaltu da neman yardar Ubangijin ka, mene ne zaisa har kana hango laifin wasu?
Ya Ubangiji Ka datar damu. Ameen.