17/06/2022
Ba raina ATIKU nayi ba, amma kafin karfe 12 rana TINUBU ya ci zabe an gama. - Inji EL-RUFAI.
Gwamnan Jihar KADUNA Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce, tsohon Gwamnan Jihar Lagos Sanata Bola Ahmed TINUBU, shine wanda zai samu nasara a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023.
A zantawa da gidan talabijin na Channels, tsohon mimistan birnin tarayyar Nigeria Abuja din, ya ce, ba wai ya raina ATIKU bane a siyasance amma batu na gaskiya TINUBU babanshi ne idan ana Maganar siyasa.
"Lissafi da wasu Jama'a musamman 'yan PDP ke yi cewa TINUBU zai samu nasara ne kawai a jihohin Yarbawa, sun manta cewa mune fa sojojinsa a arewa kuma zamu yi duk me yiwuwa ganin ya kai ga nasara"
"ATIKU ba ko shakka zai samu galaba a wasu jihohin na Arewa yayin da Kwankwaso zai lalata kuri'un jihar Kano shi kuma Peter Obi zai hana Atiku rawar gaban hantsi a yankin kudu maso gabas" Inji El-rufai.