Essangi Blog

Essangi Blog Mission of this page is to Educate peoples

04/03/2024

04/03/2024

Before I die,
I want may last words

"La ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah {ﷺ}"

Zulum a Jamhuriyar Nijar, ya ziyarci 'yan gudun hijirar Borno na garin Malam-FatoriGwamna Babagana Umara Zulum ya kai zi...
05/12/2022

Zulum a Jamhuriyar Nijar, ya ziyarci 'yan gudun hijirar Borno na garin Malam-Fatori

Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara garin Bosso da ke kan iyaka a Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadin da ta gabata, domin ziyartar 'yan jihar Borno da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu.

Mutanen dai mazauna garin Malam-Fatori ne, hedikwatar karamar hukumar Abadam da ke arewacin jihar Borno a gabar tafkin Chadi.

Malam-Fatori yana kusa da Bosso a Jamhuriyar Nijar.

Shekaru da dama, 'yan Najeriya da 'yan Nijar daga yankunan kan iyaka suna shiga da fita daga garuruwan kan iyaka don harkokin zamantakewa, kasuwanci da cinikayya.

A tsakanin shekarun 2013 da 2014, ‘yan Najeriya da dama daga Abadam, Monguno da wasu da yawa daga cikin kananan hukumomin 10 da ke arewacin Borno, sun fake a Bosso kuma s**a zauna a can tsawon shekaru bakwai, suna gudun hijira daga hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa kan iyakar Najeriya.

Tun lokacin da Zulum ya zama Gwamna a shekarar 2019 ya yi balaguro zuwa sassa daban-daban na jamhuriyar Nijar kusan sau 10, kuma duk ziyarar ta yi ne domin tantance ayyukan jin kai da kuma daukar matakai.

Sak**akon ziyarce-ziyarcen Zulum, dubban ‘yan gudun hijira sun dawo daga Bosso aka tsugunar da su a garuruwan kakanninsu galibi a arewacin Borno.

Da dama daga cikinsu an sake tsugunar da su a garin Malam-Fatori a farkon wannan shekarar (2022).

Tun a shekarar 2014 ne Boko Haram s**a mamaye Malam-Fatori tsawon shekaru bakwai kafin sojoji su kwato su.

Zulum ya kasance a garin Malam-Fatori a lokuta daban-daban yana kula da ayyukan sake ginawa, yayin da ‘yan kasar da s**a dawo sannu a hankali suke ta diban abubuwan rayuwarsu har zuwa lokacin da aka samu ambaliyar ruwa a baya-bayan nan da aka ce an yi ta yin cajin da ya wuce kima a tafkin Chadi, a bana.

04/12/2022

Thank you for this opportunity.


I'm by name IBRAHIM UMAR
From Niger State
Thank you

01/12/2022

Idan ka bawa abokinka bashin N50,000 ba tare da shedu ba. Bayan wani lokaci ka ce, wane ina son k dawo mini da kuɗina domin ina da buƙatu.

Shi kuma sai ya ce, baka bina ko sisi!

In ka garzaya zuwa kotu, abu na farko da Alƙali zai fara tambayarka shi ne, kana da shedu? A wannan lokacin da bakinka zaka ce, A'a!

Alƙali zai nemi abokinka y yi rantsuwa. Babu kunya babu tsoron Allah ya yi rantsuwa akan baka binsa ko sisi.

Alƙali zai ce tabbas haka maganar take, baka binsa ko sisi tun da ya rantse. Wannan shi ake kira ADALCI.

Amma haƙiƙanin zance kana bin abokinka N50,000 wannan ita ake kira 'GASKIYA''

Idan haka ne, ko da dalili ko babu dalili ita gaskiya ɗaya ce bata canzawa. Amma Adalci yana canzaw da canzawar shedu da dalilai.

Duk in da gaskiya take akwai adalci a wurin amma ba duk in da adalci yake bane gaskiya take.

Gaskiya Allah ne kaɗai ya santa sai wasu tsirarin mutane amma Adalci yana da fuskoki da dama, zai iya canzawa daga hagu zuwa dama a cikin mas'ala ɗaya.

A dede lokacin da ake neman kuri'u mu, a dede lokacin ake tura yan uwan mu talakawa gidan kurkuku, mungode da sakayya, d...
01/12/2022

A dede lokacin da ake neman kuri'u mu, a dede lokacin ake tura yan uwan mu talakawa gidan kurkuku, mungode da sakayya,

daga: Fitaccen Dan Jarida a Najeriya Barrah Almadany Journalist

30/11/2022

❝Wallahi duk wanda kaga ba ya tsoran RANAR AL-QIYAMAH, wallahi bai san Allah bane!❞

- Sheikh Albaniy Zaria Rahimahullah

Kungiyar Kare Hakkin bil adama ta yi Allah-wadai da k**a Aminu AdamuKungiyar kare haƙƙin bil adama ta Northern Nigeria H...
29/11/2022

Kungiyar Kare Hakkin bil adama ta yi Allah-wadai da k**a Aminu Adamu

Kungiyar kare haƙƙin bil adama ta Northern Nigeria Human Rights Advocates ta yi Allah wadai da k**a Aminu Adamu Muhammad wanda ake zargin cewa uwar gidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ta bayar da umarnin k**a shi.

A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar wato Barrista Abba Hikima ya saka wa hannu, ƙungiyar ta ce dole ne yan siyasa su bar yan ƙasa su tofa albarkacin bakinsu ba tare da yi musu barazana ba.

Ƙunigiyar ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda aka k**a yaron da kuma riƙe shi ba bisa ƙa'ida ba inda ta ce hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Haka kuma ƙungiyar ta yi kira ga duk wasu masu ruwa da tsaki da waɗanda suke da alhakin riƙe da Aminu Adamu da su sake shi nan take su ba shi haƙuri sa'annan kuma su biya shi diyya.

Batun k**a wannan matashi dai na daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta a Najeriya inda jama'a da dama ke bayyana mabambantan ra'ayoyi kan hakan.

Idan babba baiji kunyar hawa jaki ba......😂😂
24/11/2022

Idan babba baiji kunyar hawa jaki ba......😂😂

ALLAHU AKBAR: Nijeriya Ce Ƙasa Ta Ɗaya A Duniya Da Tafi Yawan Mahaddata Al-Qur’aniGa jadawalin ƙasashen da s**a fi yawan...
23/11/2022

ALLAHU AKBAR: Nijeriya Ce Ƙasa Ta Ɗaya A Duniya Da Tafi Yawan Mahaddata Al-Qur’ani

Ga jadawalin ƙasashen da s**a fi yawan mahaddata Al-Qur’ani Mai Girma k**ar haka:

1. Nijeriya

2. Indonesia

3. Saudi Arabia

4. Somalia

5. Pakistan

This is 20-year-old Qatari, Ghanim Al-Muftah. He starred alongside Morgan Freeman and recited the   in the   opening cer...
22/11/2022

This is 20-year-old Qatari, Ghanim Al-Muftah. He starred alongside Morgan Freeman and recited the in the opening ceremony.

Ghanim was born with a rare condition known as Caudal Regression Syndrome, affecting the development of the lower half of the body.

Many suggested his mother abort Ghanim but she decided to have him: “I will be his left leg and you will be his right leg”.

Ghanim became Qatar's youngest entrepreneur, having founded an ice-cream business. He plays multiple sports despite physical disabilities. At school, Ghanim used to play football wearing shoes on his hands and would chase after the ball with his "normal-sized" friends.

Rather than allowing the condition to stunt his life, Ghanim has learned to overcome obstacles with positivity. He is currently pursuing his university degree, majoring in political sciences with a goal of becoming a diplomat.

______________________________________

#Палестина #فلسطين #2022

Sama da shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur yayi wannan wa'azin a sigar Wake~ Matukar a arewa da karuwai,~ yan daudu dasu...
21/11/2022

Sama da shekaru 50, Marigayi Sa'adu Zungur yayi wannan wa'azin a sigar Wake

~ Matukar a arewa da karuwai,
~ yan daudu dasu da magajiya.
~ Da samari masu ruwan kudi,
~ Ga mashaya can a gidan giya.
~ Matukar yayan mu suna bara,
~ T**i da Loko-lokon Nijeriya.
~ Hanyar birni da na kauyuka,
~ Allah baku mu samu abin miya.
~ Sun yafu da fatar bunsuru,
~ Babu mai tanyonsu da dukiya.
~ Babu shakka yan kudu zasu hau,
~ Dokin mulkin Nijeriya.
~ In ko yan kudu sunka hau,
~ Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
~ A Arewa zumunta ta mutu,
~ Sai karya sai sharholiya.
~ Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
~ Malaman karya yan damfara.
~ Sai karya sai kwambon tsiya,
~ Sai hula mai annakiya.
~ Ga gorin asali da na dukiya,
~ Sai kace dan annabi fariya.
~ Jahilci ya ci lakar mu duk,
~ Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
~ Ya daure kafarmu da tsarkiya.
~ Bakunan mu ya sa takunkumi,
~ Ba zalaka sai sharholiya.
~ Wagga al’umma mai zata yo,
~ A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
~ Zaya sha kunya nan duniya “.
~ “Mu dai hakkin mu gaya muku,
~ Ko ku karba ko kuyi dariya.
~ Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
~ Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
~ Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
~ Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
~ Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
~ waken sa mai suna “Arewa
~ Jamhuriya ko Mulukiya”
Allah Yajikan Malam Saadu Zungur
Allah kayimasa Rahama amin amin

Address

Madaka Road
Kagara

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Essangi Blog posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share