09/09/2021
Jihohin Arewa zasu durkushe matukar... - Salihu Tanko Yakasai
Wato naga alama da wasa da wasa nan gaba dan arewa sai an wayi gari ya zama bawa a kasar nan saboda rashin kishi da sanin madafar aiki da hangen nesa na shugabannin arewa da ma mu kan mu yan arewan.
A wannan makon, gwamnan jihar Rivers wato Wike yayi nasara a wata kotu kan maganar karbar kudin haraji na VAT mai makon gwamnatin taraiya (ta hannun FIRS) ta karba a jihar sa, wannan mataki shi ma yana dab da zama doka a jihar Lagos, wanda suma jihar ce zata karbi wannan kudi ba gwamnatin taraiya ba, abinda wannan yake nufi shine idan jihohin kudu wanda su s**a fi tara kudin haraji na VAT s**a daina bari gwamnatin taraiya ta na karba, kenan za'a wayi gari kudin da jihohin arewa suke samu daga Abuja wato allocation zai yi kasa sosai, wanda mafi yawancin su kenan zasu durkushe domin a yanzu ma haka kusan kudin da suke samu ko albashi baya iya biya bare suyi aiki da shi. Wannan lamari ko da zai yi wuyar aiwatar wa, ni ina kallan sa a matsayin abinda ya k**ata ya tashi arewa daga bacci.
Idan aka zo maganar kudaden shiga, banda jihar Kaduna da kuma Kano, ba wata jiha a arewa da take tara kudi sosai wanda zai sa ta dogara da kanta ba sai ta jira kudin Abuja ba. Duk da dai a kudancin kasar nan kamfanunnika sun fi yawa idan aka hada da na arewacin kasar, amma muna da hanyoyin da zamu inganta kudaden shigar mu, domin samun damar tsayawa da kafafun mu.
Mafi karancin misali, banga dalilin da zamu dinga dibar kayan abinci haka zalla muna kaiwa kudu ba, bacin zamu iya samar da kamfanin da zai gyara su ya sa a kwalli a kai shi kudun, wanda yin hakan sai ya fi daraja. Ko kuma ace wai an dura shanu a mota an kai Kudu bacin zamu iya yin abattoir, ya zamo cewa yankakken nama za'a kai musu, idan kuma suna san saniya ko rago mai rai, toh a zabga haraji yadda sai sun gwammace su sai yankakken. Yajin aikin kai albasa Kudu kawai arewa ta yi kwanaki amma sai da Kudu ta girgiza. Yin haka zai samar da aikin yi, da kudin shiga ga arewacin Najeriya saboda abinci ne arzikin mu. Shekara da shekaru an gagara yin kamfanin tumatirin gwangwani kwaya daya tak a Kano, wanda da anyi da manoman timatir sun rage asara ba kadan ba, kuma da tattalin arzikin su ya inganta.
Duk bankunan da suke Kano, ko arewa ma gaba daya, da kuma rassan manyan kamfanunnika zaka ga motocin su lambobin Lagos ne da su, su zo Kano mu tara musu kudi amma duk kudin harajin su Lagos yake komawa. Akan me?
Shekara shida dan arewa na shugabancin kasar nan amma har yanzu arewa bata samu wutar lantarki ba wanda zai farfado da masana'antu a yankin mu, bare tattalin arzikin mu ya bunkasa, gashi wankin hula ya kai mu dare. Mun ci sa'a ma ana aikin bututun iskar gas wato AKK, wanda hakan zai sa a samu farfadowar kamfanunnika musamman a Kano da Kaduna, amma shi ma akwai sauran aiki a gaba.
Toh gaskiya ina kira da babbar murya manyan mu da shugabannin mu da mu kan mu magoya baya, da a tashi tsaye, tsayin daka. Ya zama wajibi mu nemi hanyoyin da zamu inganta tattalin arzikin arewa yadda zamu iya tsayawa da kafafun mu, ko kuma mu zama bayi a kasar nan. Kowanne gwamna ya tabbatar kujera mafi kusanci da shi, da kuma wadda tafi kowacce muhimmanci ita ce kujerar kwamishina ko mai bada shawara akan fannin tattalin arziki. Sannan shugabannin arewa su dinga haduwa suna hada karfi da karfe wajen ganin sun ciyar da yankin mu gaba, ba suyi ta fada a tsakanin su ba, wannan baya shiri da wancan, wancan baya ga miciji da wannan. A duba halin da muke ciki, a cece mu tun kafin mu azabta.
Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.