12/09/2025
FALALAR KARATUN SURATUL KAHFI
1. Kariyar daga Dajjal
Annabi ﷺ ya ce:
“Duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahfi, zai sami kariya daga Dajjal.”
(Muslim ne ya rawaito).
A wani riwayar kuma:
“Duk wanda ya karanta farkon Suratul Kahfi zai sami kariya daga Dajjal.”
(Muslim).
2. Haske a tsakanin sati biyu
Annabi ﷺ ya ce:
“Duk wanda ya karanta Suratul Kahfi a ranar Juma’a, zai sami haske tsakanin shi da Ka’aba.”
(al-Bayhaqi da al-Hakim s**a rawaito, s**a ce sahihi).
A wani riwayar:
“Duk wanda ya karanta Suratul Kahfi a ranar Juma’a, haske zai haska masa daga ƙasa zuwa sama, kuma zai haskaka masa tsakanin Juma’a biyu.”
(al-Hakim).
3. Kariyar daga fitintinu
Saboda surar ta ƙunshi labaran fitintinu da hanyoyin tsira daga gare su (fitinar addini, dukiya, ilimi, da mulki), wanda ya karanta ta da nazari Allah zai tsare shi daga irin waɗannan fitintinu.
4. Haske a kabari da ranar kiyama
An ce karatun Suratul Kahfi yana kawo haske a kabari, sannan kuma yana zama haske ga mai karatu a ranar kiyama.
Saboda haka, musulmi yana da kyau ya riƙa karanta Suratul Kahfi musamman a ranar Juma’a, ko da ya karanta cikakkiyar surar ko kuma ayoyi goma na farko
(ko na ƙarshe).
Kuyi sharing zuwa ga yan uwa su amfana
Abu Ja'afar Assunny ✍️