29/12/2022
Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Radda, ya jaddada kudirinsa na shigewa gaba wajen yaki da rashin tsaro a jihar Katsina.
Dr. Radda ya yi wannan ikirari ne a lokacin da yake ganawa da dimbin jama’ar da s**a tarbe shi a karamar hukumar Safana a ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zaben 2023, a yau Alhamis, 29/12/2022.
Dr. Radda ya jagoranci tawagar yakin neman zaben tun daga Katsina zuwa Zakka domin ziyartar fadar Gatarin Katsina, Hakimin Zakka, daga Zakka zuwa Kukar Samu ta garin Batsari, daga Kukar Samu zuwa Babban Duhu, Daga Babban Duhu, Dr. Radda ya jagoranci tawagar kamfen din zuwa garuruwan Baure, Ummadau, Tsakiya, R***a inda daga karshe kuma ya tsaya a filin taron gangamin kamfen a garin Safana.
A lokacin da ya isa garin Tsaskiya, ya bayyana ma al'umma cewa, sun zo ne domin ganin halin da suke ciki domin kuwa an shaida masu cewa ba zasu iya zuwa ba saboda babu tsaro, amma ya tabbatar da cewa in dai akwai alumma a garin, to babu abun da zai hana su zuwa in dai da gaske yana San shugabancin Katsina.
A duk wuraren da ya ziyarta Dr. Radda ya bayyana cewa duk wani shugaban da zai yi yaki da matsalar rashin tsaro da jihar ke fama da shi, dole ne ya kuduri aniyar shigewa sahun gaba a fagen daga. Ya bayyana yaki da rashin tsaro a matsayin wani nauyi daya rataya a wuyan kowa, don haka akwai bukatar hadin gwiwa tare da yin nuni da cewa dole ne kowa da kowa ya tashi tsaye domin samun nasara a wannan fanni.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC ya bada tabbacin inganta harkar noma tare da samar da kananan sana'o'i domin samar da ayyukan yi ga matasa da mata a fadin jihar nan.