Abu muh'd

Abu muh'd إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

04/03/2023

𝗔𝗧𝗧𝗔𝗕𝗦𝗜𝗥𝗔𝗧𝗨 𝗙𝗜 𝗨𝗟𝗨𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗟𝗤𝗨𝗥'𝗔𝗡, 𝓷𝓪 𝓫𝓪𝓫𝓫𝓪𝓷 𝓶𝓪𝓵𝓪𝓶𝓲 ( ᴀʙᴜʟ ʜᴀꜱꜱᴀɴ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ ꜱᴀʏʏɪᴅɪʏ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ ᴀᴍɪɴ ).

𝐃𝐀𝐑𝐀𝐒𝐈 𝐍𝐀, 17.

ℍ𝕀𝕂𝕀𝕄𝕆𝕄𝕀ℕ 𝔻𝔸𝕂𝔼 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝕊𝔸𝕌𝕂𝔸ℝ 𝔻𝔸 𝔸𝕃ℚ𝕌ℝ'𝔸ℕ𝕀 𝔸 ℝ𝔸ℝℝ𝔸𝔹𝔼/𝕂𝔸𝕂𝕂𝔸𝕋𝕊𝔼.

𝑪𝒊𝒈𝒂𝒃𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝒊𝒏𝒅𝒂 𝒂𝒌𝒂 𝒕𝒔𝒂𝒚𝒂.

Akwai Kuma wasu hikimomin daban wadanda suke fa'idantar da saukar alqur'ani a rarrabe. daga ciki akwai.
* Gudanar sababbin abubuwa da Ababen da kan fado ko halaye ko afkuwar wasu mas'aloli, Wannan hikumar itace wadda Allah ya fada a Suratul Furqan:
ولا يأتونك بمثل إلا جئناك بالحق وأحسن تفسيرا.
Qarqashin wannan akwai wasu hikimomi kamar haka:
1. Bayanin hukuncin Allah madaukakin sarki kan hukunce-hukunce, da abubuwan da suke fadowa tsakanin musulmi, haqiqa rahamar sa ga bayin sa ta hukunta duk lokacin da wani Abu ya faru Kuma hukuncin sa ba sananne bane ga musulmai, sai a saukar da wata aya ko ayoyi masu bayanin hukuncin Allah kan wannan mas'alar, Misali:- Abinda ya faru game da qirqirar qarya ga Nana Aishah yardar Allah ta Kara tabbata agareta, haqiqa ayoyi sun sauka daga saman bakwai wadanda suke nuni akan barrantar Nana Aishah, da Kuma hukunci ga wadanda s**a jefe ta da hakan ba tare da shaidu ba, da Kuma bayanin hukuncin Allah game da su, shine fadar Allah:
إن الذين جاءوا بالإفك عصبة منكم لا تحسبوه شرا لكم بل هو خير لكم لكل امرىء منهم ما اكتسب من الإثم.......، ولولا فضل الله عليكم ورحمته وأن الله رؤوف الرحيم. سورة النور.
Alhamdulillah Masha Allah, mu hadu a darasi na gaba.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/.

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

01/03/2023

𝗔𝗧𝗧𝗔𝗕𝗦𝗜𝗥𝗔𝗧𝗨 𝗙𝗜 𝗨𝗟𝗨𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗟𝗤𝗨𝗥'𝗔𝗡, 𝓷𝓪 𝓫𝓪𝓫𝓫𝓪𝓷 𝓶𝓪𝓵𝓪𝓶𝓲 ( ᴀʙᴜʟ ʜᴀꜱꜱᴀɴ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ ꜱᴀʏʏɪᴅɪʏ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ ᴀᴍɪɴ ).

𝐃𝐀𝐑𝐀𝐒𝐈 𝐍𝐀, 16.

ℍ𝕀𝕂𝕀𝕄𝕆𝕄𝕀ℕ 𝔻𝔸𝕂𝔼 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝕊𝔸𝕌𝕂𝔸ℝ 𝔻𝔸 𝔸𝕃ℚ𝕌ℝ'𝔸ℕ𝕀 𝔸 ℝ𝔸ℝℝ𝔸𝔹𝔼/𝕂𝔸𝕂𝕂𝔸𝕋𝕊𝔼.

𝑪𝒊𝒈𝒂𝒃𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝒊𝒏𝒅𝒂 𝒂𝒌𝒂 𝒕𝒔𝒂𝒚𝒂.

Wani lokacin da qarfafa/tabbatar da zuciyar sa wajen saukar da ayoyin lallashi da hanishi akan fushi wajen bijirowa mutanen sa shiriya, kamar inda Allah yake cewa: لعلك باخع نفسك ألا يكونوا مؤمنين --- (شعراء)
Da fadar Allah: ---فلا تذهب نفسك عليهم حشرات. (فاطر)
Kuma sau dayawa tabbatar da zuciyar sa kan kasance da saukar da ayoyin azaba irin wadanda aka gargadi masu qaryata shi da su daga cikin mutanen sa, domin tsoron kada wata uquba ta same su, kamar yanda ta shafi wadanda s**a gabace su daga al'ummomin da s**ayi zalumci, kamar inda Allah yake cewa:
فإن أعرضوا فقل أنذرتكم صاعقة مثل صاعقة عاد وثمود * إذ جاءتهم الرسل من بين أيديهم ومن خلفهم ألا تعبدوا إلا الله قالوا لو شاء ربنا
لأنزل ملائكة فإنا بما أرسلتم به كافرين. ( فصلت)

Wani lokacin tabbatar da zuciyar sa kan kasance da saukar da ayoyin kafa hujja wadda zata buce qarerayin masu qirqirar qarya, kamar ayar da ta sauka domin bata shirka, da yin kuka akan mutawar mushrikai, da raddi/inkari game da masu inkarin/musun tashi alqiyama da ta taruwa bayan mutuwa, da qarar da shubuhohin masu inkarin wahayi da Kuma annabta.

Alhamdulillah Masha Allah, mu hadu a darasi na gaba in Sha Allah.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

28/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 97.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝔹𝔸𝕐𝔸ℕ𝕀ℕ 𝕎𝔸𝕊𝕀𝕐𝕐𝔸 𝔾𝔸 𝕄𝔸𝕋𝔸.(ᴋʏᴀᴜᴛᴀᴛᴀ ᴍᴀsᴜ).

Daga Abi Hurairata yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yace Lallai Sa'ad Dan Ubaidatu al'ansari yace ya Rasulallah shin ya kake gani ace mutum ya iske wani mutum tare da Matar sa shin zai kashe shi ne? Sai Manzon Allah ﷺ yace: A'A. Sai Sa'ad yace: A'a na rantse da Wanda ya aiko ka da gaskiya. Sai Manzon Allah ﷺ yace: KU SAURARI ABINDA SHUGABAN KU KE FADA (SA'AD).
Daga dai shi Abi Hurairata yace Sa'ad yace ya Rasulallah shin ya kake gani ace na iske wani tare da Matar ta, bazan taba shi ba sai nazo da shaidu guda hudu? Sai Manzon Allah ﷺ yace: NA'AM. Sai Sa'ad yace: Kai!!! Na rantse da Wanda ya aiko ka da Gaskiya, zan gaggauta takobi a kansa kafin shaidun nan kuwa.sai Manzon Allah ﷺ yace: KU SAURARI ABINDA SHUGABAN KU KE FADA (SA'AD). LALLAI SHI MAI KISHI NE, AMMA NI NA FISHI KISHI, ALLAH KUMA YA FINI KISHI.
رواه مسلم.
Ya ubangijin ka kare Mana kawunan mu da iyalan mu daga fadawa cikin fitina ta rayuwa.
Alhamdulillah, Wa sallallahu Ala Nabiyi nal karim.
Wannan shine qarshen karatun littafin (HAQQUL MUBIN). A yau 08/08/1444, 28/2/2023.
Allah nake roqo daya karbi wannan karatu Kuma ya sanya shi a cikin mizani na na lada Kuma ya yafe man Abinda na fassara ba dai dai ba. Lallai shi mai iko ne bisa haka.

In Sha Allah karatun littafin 𝔸𝕋𝕋𝔸𝔹𝕊𝕀ℝ𝔸𝕋𝕌 𝔽𝕀 𝕌𝕃𝕌𝕄𝕀𝕃 ℚ𝕌ℝ'𝔸ℕ zai cigaba da zuwa daga inda muka tsaya.
Dan Uwanku Abu Muh'd.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

27/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 96.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝔹𝔸𝕐𝔸ℕ𝕀ℕ 𝕄𝕌𝕊𝕋𝔸ℍ𝔸𝔹𝔹𝔸ℕℂ𝕀ℕ 𝔸𝕌ℝ𝔼ℕ 𝔹𝕌𝔻𝕌ℝ𝕎𝔸.

Daga Jabir Dan Abdullahi yardar Allah ta Kara tabbata agaresu yace: Lallai Abdullahi ya Rasu Kuma ya bar 'yan Mata guda tara ko Kuma bakwai, Sai Nayi Aure, na auro bazawara, Sai Manzon Allah ﷺ yace: YA KAI JABIR KAYI AURE? sai nace eh. Sai yace: TO BUDURWA KO BAZAWARA? sai nace masa bazawara ce ya Rasulallah. Sai Manzon Allah ﷺ yace: INAMA ACE BUDURWA CE, KAYI WASA DA ITA, ITAMA TAYI WASA DA KAI. Ko Kuma cewa yayi: KA SATA DARIYA TA SAKA DARIYA. Sai nace masa: Lallai Abdullahi ya Rasu Kuma ya bar'yan Mata guda tara ko Kuma bakwai, shiyasa na qyamaci in auro tsarar su agaresu, sai dai na auro macen da zata iya tsayawa game da sha'anin su Kuma ta kimtsa su. Sai Manzon Allah ﷺ yace: ALLAH YAYI MAKA ALBARKA.
رواه مسلم.

Ya ubangiji ka bamu ikon bin sunnar Annabin mu game da dukkan ayyukan mu. Kuma ka aurar da marasa aure daga cikin mu. Kuma ka aura Mana budurwa domin muyi wasa da ita, itama ta yi wasa damu, Kuma mu sata dariya itama ta samu dariya.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

26/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 95.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ ℍ𝕌𝕂𝕌ℕℂ𝕀ℕ 𝕋𝕊𝕆𝕋𝕊𝔸 𝔻𝔸𝕐𝔸 𝕂𝕆 𝕋𝕊𝕆𝕋𝕊𝔸 𝔹𝕀𝕐𝕌.

Daga Ummul Fadhli tace Wani balaraben Qauye ya shigo gurin Manzon Allah ﷺ alhalin yana cikin gida na, sai yace ya Annabin Allah lallai ni ya kasance ina da Mata, Sai na auro Wata Matar, Sai Matar tawa ta farkon tace ta shayar da Matar nan tawa ta biyu Nono sau daya ko sau biyu. Sai Manzon Allah ﷺ yace: AI TSOTSA DAYA KO TSOTSA BIYU BATA CUTARWA.
رواه مسلم.

Wannan sai ya nuna cewar hukuncin shayarwa ga yaro yanada tasiri wajen dangantaka, Kuma hukuncin shayarwa kamar hukuncin jini ne wajen Abinda yake haramtawa kamar dai wajen shayarwar nan,
Sannan wannan ya bayyana Mana cewar tsotsa daya na nono ko biyu baya tabbatar da wadannan hukunce hukuncen har sai shayarwar da ta haifar da qoshi, wadda ta kawar da yunwa, itace ake kira da shayarwa Kuma mai haramta aure ko aurowa. Allah ne mafi sani.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

25/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 94.

** 𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝕌𝕄𝕌ℝℕ𝕀 𝔻𝔸 𝔸𝕄𝕊𝔸𝕎𝔸 𝕄𝔸𝕀 𝕂𝕀ℝ𝔸 ℤ𝕌𝕎𝔸 𝕎𝔸𝕃𝕀𝕄𝔸.

Daga Nafi'u yace Naji Abdullahi Dan Umar yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yana cewa: Manzon Allah ﷺ yace: KU AMSA WANNAN KIRAN IDAN AN KIRAKU ZUWA GARETA, Nafi'u yace Abdullahi Dan Umar ya kasance yana zuwa walimar aure ko wadda ba ta aure ba, ya kasance yana zuwa walimar alhalin yana azumi.
رواه مسلم.

** 𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ ℍ𝕌𝕂𝕌ℕℂ𝕀ℕ 𝕊ℍ𝔸𝕐𝔸ℝ𝕎𝔸.

Daga Nana Aishah yardar Allah ta Kara tabbata agareta tace: baffa na Wanda aka shayar damu tare yazo ya nemi izini na, sai naqi yi masa izini har sai na nemi umarnin Manzon Allah ﷺ, Nace masa baffa na Wanda aka shayar damu tare yazo yana neman izini na ban bashi ba, sai Manzon Allah ﷺ yace: BAFFAN KI YA SHIGO GURIN KI. Sai Ummuna Aisha tace: nifa mace ta shayar Dani ba namiji ba. Sai Manzon Allah ﷺ yace: SHI FA BAFFAN KI NE YA SHIGO GURIN KI.
رواه مسلم.

Allah ya bamu ikon amsawa yan uwan mu musulmi Kiran da zasuyi Mana domin tayasu farin ciki, Kuma ka bamu ikon bin sunnar Annabin mu Muhammad ﷺ.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

24/02/2023

📜 صحيح البخاري 📜

24- بَابُ إِذَا حَاضَتْ فِي شَهْرٍ ثَلاَثَ حِيَضٍ.

وَمَا يُصَدَّقُ النِّسَاءُ فِي الحَيْضِ وَالحَمْلِ فِيمَا يُمْكِنُ مِنَ الحَيْضِ.
لِقَوْلِ اللهِ تَعَالَى: {وَلاَ يَحِلُّ لَهُنَّ أَنْ يَكْتُمْنَ مَا خَلَقَ اللهُ فِي أَرْحَامِهِنَّ}.

وَيُذْكَرُ عَنْ عَلِيٍّ، وَشُرَيْحٍ: إِنِ امْرَأَةٌ جَاءَتْ بِبَيِّنَةٍ مِنْ بِطَانَةِ أَهْلِهَا مِمَّنْ يُرْضَى دِينُهُ، أَنَّهَا حَاضَتْ ثَلاَثًا فِي شَهْرٍ صُدِّقَتْ.
وَقَالَ عَطَاءٌ: أَقْرَاؤُهَا مَا كَانَتْ.
وَبِهِ قَالَ إِبْرَاهِيمُ.
وَقَالَ عَطَاءٌ: الحَيْضُ يَوْمٌ إِلَى خَمْسَ عَشْرَةَ.

وَقَالَ مُعْتَمِرٌ: عَنْ أَبِيهِ: سَأَلْتُ ابْنَ سِيرِينَ عَنِ المَرْأَةِ تَرَى الدَّمَ بَعْدَ قُرْئِهَا بِخَمْسَةِ أَيَّامٍ؟ قَالَ: النِّسَاءُ أَعْلَمُ بِذَلِكَ.

📝حديث رقم (325):
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سَأَلَتِ النَّبِيَّ ﷺ قَالَتْ: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فَقَالَ: «لاَ، إِنَّ ذَلِكِ عِرْقٌ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ الأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلِّي».

📌 شرح المفردات:
(أَقْرَاؤُهَا مَا كَانَتْ): جمع قرء أي في زمان العدة، ما كانت: أي قبل الطلاق.
(فَلاَ أَطْهُرُ): لا ينقطع عني الدم.
(أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟): هو سؤال عن استمرار حكم الحيض حالة دوام الدم وعدمه ممن تقرر عنده أن الحائض ممنوعة من الصلاة.

📌 الفوائد:
1) اختلف العلماء في تقدير أقل الحيض وأكثره، والصحيح أنه لا حد فيه وإنما التعويل على مسمى الحيض الذي علقت عليه الأحكام، ويرجع ذلك إلى المعروف من حيض النساء، ويرجع أيضا إلى أمانة المرأة وعادتها وقدر الأيام قد يقل وقد يكثر، على قدر أحوال النساء في أسنانهن وبلدانهن.

2) إذا أشكل على مسلم انقضاء عدة امرأة ردها إلى الكتاب والسنة، فتعد الأقراء بالشهور، كَما في حق الآيسة والصغيرة.

3) فيه دلالة على أن المرأة مؤتمنة على الإخبار بما في رحمها، ومصدقة فيهِ إذا ادعت مِن ذَلِكَ ممكناً.

4) فيه دليل على الرد إلى العادة، فإن كانت مميزة وثبت ما يدل على التمييز فذاك، وإلا ردت إلى العادة.

5) قيل: فيه دليل لأبي حنيفة في الرجوع إلى العادة سواء كانت مميزة أم لا.

6) المستحاضة تصلي أبدا، إلا في الزمن المحكوم بأنه حيض، وهذا إجماع.

7) لا يترك الصلاة من عليه الدم كما فعل عمر حيث صلى وجرحه يثعب دما.

8) أن الدم السائل من الجسد من فصد وغيره لا ينقض الطهارة، لقوله ﷺ: "إن ذلك عرق".

9) فيه رد على من قال: إنه يلزمها الغسل لكل صلاة لأنه ليس في الحديث ما يقتضي تكرار الغسل، فلا يجب الغسل إلا مرة واحدة للحيض عند الانقطاع.

📕أكاديمة علوم الحديث رواية ودراية (القناة العامة):📕
https://t.me/hadith_sciences_ahmedbakry

24/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 93.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝕄𝕌𝕊𝕋𝔸ℍ𝔸𝔹𝔹𝔸ℕℂ𝕀ℕ 𝕂𝔸𝕃𝕃𝕆 ℤ𝕌𝕎𝔸 𝔾𝔸 𝔽𝕌𝕊𝕂𝔸ℝ 𝕄𝔸ℂ𝔼 𝔸 𝕋𝔸𝔽𝕌𝕂𝔸ℕ ℍ𝔸ℕℕ𝔸𝕐𝔼ℕ 𝕋𝔸 𝔾𝔸 𝕎𝔸ℕ𝔻𝔸 𝕂𝔼 𝕊𝕆ℕ 𝔸𝕌ℝ𝔼ℕ 𝕋𝔸.

Daga Abi Hurairata yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yace: Na kasance agurin Manzon Allah ﷺ sai wani mutum yazo gurin sa ya bashi labarin ya auri wata mace daga mutanen Madina. Sai Manzon Allah ﷺ yace masa: KAYI KALLO ZUWA GARETA ? Sai yace a'a. Sai yace masa: JEKA KA KALLE TA, DOMIN ACIKIN IDANUN MUTANEN MADINA AKWAI WANI ABU.
رواه مسلم.
Daga Sahlu Dan sa'adus sa'idiyyi yace: wata mata tazo gurin Manzon Allah ﷺ Tace nazo ina Mai kyautar kaina gareka. Sai Manzon Allah ﷺ ya kalle ta, ya daga kallo gareta sannan ya dai dai ta shi, sannan yayi qasa da kansa. lokacin da matar nan taga baice komai ba game da ita, sai ta zauna. Sai wani mutum cikin Sahabban sa ya tashi yace: idan baka da buqatar ta, ka aura man da ita. Sai Manzon Allah ﷺ yace SHIN AKWAI WANI ABU A GURIN KA ? Sai yace a'a ya rasulullah, sai yace masa: JEKA GURIN IYALINKA KAGA ZAKA SAMO WANI ABU. Sai ya tashi ya tafi yaje ya dawo yace: wallahi ba'a samu komai ba. Sai Manzon Allah ﷺ yace: NEMO KO ZOBEN BAKIN QARFE NE. Sai yaje ya dawo yace ko zoben ma na qarfen babu. Amma ga gyauto na nan tanada rabin sa, 'sahlu yace bashida wani qyauton banda wannan'. Sai Manzon Allah ﷺ yace: ME ZA TAYI DA QYAUTON KA? IDAN KA DAURA SHI ITA KUMA BA TA DA KOMAI, IDAN KUMA ITA TA DAURA SHI TO KAI BA KA DA KOMAI. Sai mutumin ya samu guri ya zauna, bayan ya dade a zaune sai ya tashi ya tafi, sai Manzon Allah ﷺ ya ganshi ya tafi, sai yace akirashi. Lokacin da yazo sai yace masa: ME KA HADDACE NA ALQUR'ANI ? Sai yace: Na haddace sura kaza da sura kaza ya lissafo su. sai yace: KANA IYA KARANTA SU A HADDACE ? Sai yace Na'am, sai Manzon Allah ﷺ yace: JEKA NA MALLAKA MAKA ITA SABODA ABUNDA KE TARE DA KAI NA ALQUR'ANI.

رواه مسلم.
Ya ubangiji ka datar damu.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

21/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 92.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ ℍ𝔸ℝ𝔸𝕄ℂ𝕀ℕ 𝔸𝕌ℝ𝔼ℕ 𝕄𝕌𝕊𝔸𝕐𝔸 (sʜɪɢᴀʀ), 𝔻𝔸 𝕂𝕌𝕄𝔸 𝔹𝔸ℂ𝕀ℕ 𝕊ℍ𝕀.

Daga Dan Umar yardar Allah ta Kara tabbata agaresu yace: Lallai Manzon Allah ﷺ yayi hani akan auren musaya. Abinda ake cewa auren musaya: shine mutum ya aurar da diyar sa akan shima Wanda ya aurar mawa ya aura masa shima diyar sa, Amma babu sadaqi atsakanin su.

Wannan auren yana daga cikin auren da Manzon Allah ﷺ ya haramta ga al'ummar sa, kasancewar aure ne da babu wani sadaqi acikin sa. ya zama kamar musayar kayayyaki tsananin mutane wanda shi aure bai zamo irin hakan ba.
Ya ubangiji ka bamu ikon bin sunnar Annabin mu.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

18/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 91.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ ℍ𝕌𝕂𝕌ℕℂ𝕀ℕ 𝕎𝔸ℕ𝔻𝔸 𝕐𝔸𝔾𝔸 𝕎𝔸𝕋𝔸 𝕄𝔸ℂ𝔼 𝕊𝔸𝕀 𝕋𝔸 𝔽𝔸𝔻𝔸 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ ℝ𝔸ℕ𝕊𝔸.

Daga Jabir yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yace Lallai Manzon Allah ﷺ yaga wata mata, sai ya nufi matar sa Zainab alokacin tana jeme wata fatar ta, sai ya biya buqatar sa. sannan ya dawo gurin Sahabban sa yace: LALLAI ITA MACE TAKAN FUSKAN TO DA SURAR SHAIDAN, KUMA TAKAN JUYA BAYA DA SURAR SHAIDAN, IDAN DAYANKU YAGA WATA MACE(sai ta fada a ransa) TO YAJEWA MATAR SA, DOMIN WANNAN ZAI MAYAR DA ABINDA KE A RANSA.

رواه مسلم.

Daga dai shi Jabir yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yace Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa: IDAN DAYANKU MACE TA BURGE SHI HAR TA FADA A RANSA, TO YA NUFACI MATAR SA, YA TAKE TA, DOMIN WANNAN ZAI MAYAR DA ABINDA KE CIKIN RANSA.

Ya ubangiji ka bamu ikon bin sunnar Annabin mu Kuma ka bamu mata na kwarai, Kuma ka aurar da mu.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

إن الله مع الذين اتقو والذين هم محسنون

16/02/2023

𝗞𝗔𝗥𝗔𝗧𝗨𝗡 𝗟𝗜𝗧𝗧𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗛𝗔𝗞𝗞𝗨𝗟 𝗠𝗨𝗕𝗜𝗡.

𝖣𝖠𝖱𝖠𝖲𝖨 𝖭𝖠, 90.

𝔹𝔸𝔹𝕀 𝔸 ℂ𝕀𝕂𝕀ℕ 𝔸𝕌ℝ𝔼.

Daga Anas yardar Allah ta Kara tabbata agareshi yace: Wasu daga cikin Sahabban Annabi ﷺ, Sun tambayi matan Annabi ﷺ game da ayyukan sa a sirrance( a gida ). Sai wani daga cikin su yace: Bazan auri mata ba, Wani Kuma yace: Ni ba zan ci Nama ba, Wani Kuma yace: Ni ba zan qara barci ba akan shimfida ba. Da Manzon Allah ﷺ yaji haka, sai yayi godiya ga Allah yayi yabo gareshi sannan yace: MEYA SAMU WASU MUTANE SUKE CEWA KAZA DA KAZA, SAI DAI NI INA YIN SALLAH KUMA INA YIN BARCI KUMA INA YIN AZUMI KUMA INA SHAN RUWA, KUMA INA AUREN MATA, DUK WANDA YA GUJI SUNNAH TA TO BAI TARE DA NI.
رواه مسلم.

Ya ubangiji ka bamu ikon yin koyi da Manzon Allah ﷺ bisa koyarwar sa, ba bisa son zuciya ba ko ganin ya kamata.

Wanda ke buqatar farkon wadannan Darussan saiya tuntubi wadannan links din na qasa.

Page, Abu Muh'd.
👇👇👇 https://www.facebook.com/profile.php?id=100072291571591.

Group, NASIHA.
👇👇👇
https://facebook.com/groups/144877520331129/

Address

Rafin Dinya Bcga
Katsina

Telephone

+2348107515354

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abu muh'd posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Abu muh'd:

Share