05/05/2022
Kira Zuwa Gurin Ƙungiyoyin Dalibai Na Jami'a , Gwamnati , Da Yan Kasuwa , Dangane da Yajin Aikin ASUU , NASU, SSANU .
Assalamu Alaikum .
Bai Kamata Ace Strike din da ake a Zuba Idanu Ana Kallon Gwamnati Da Kungiyoyin Malaman Jami'a .
Idan ku ka yi La'akari da Cewa shi kanshi Yajin Aikin Ba yanzu aka fara shi ba an dauki shekaru ma su Tsawo Ana yi
Amma har yanzu a abu daya ake Gwamnati Ta Gaza Biyan Bukatun Malaman Jami'a .
Su kuma Bukata tana tasowa su Tsunduma Yajin Aikin .
To shin su daliban ba su da Kungiyoyin Kare Hakkin Sune ? .
Yakamata Kungiyar Daliban Jami'o'i Ta Ƙasa NAUS Ta Tashi Tsaye Don Tabbatar da Bin Kadin Hakkin Mambobinta Itama Haka Kungiyar Dalibai Ta Kasa NANS Itama Su Tashi Tsaye Idan Zai Yiwu Har Zanga Zangar Lumana Su yi
Don Gwamnati ta duba ta biya Malaman da Kungiyar Alkawarin Da Tai Musu .
Idan Ba Haka Ba Su ma Sun Cire Hannunsu Daga Lamarin Zaɓe Da Za a Gabatar .
Idan Kuma Ba Haka ba a Ware Adadin Wasu kudi da kowanne Dalibin Jami'a Zai ba Makarantar Shi a Hada Ko Za su Tashi Kudin Da ASUU NASU da SSANU Ke Bukata , Domin Kawo Karshen Yajin Aikin .
Ko Kuma Manyan Yan Kasuwar Mu Su Saka Hannu Cikin Lamarin Su Hada Karfi Da Karfe Su Biya Domin Jin dadin Dalibai .
Idan Aka ci gaba da Haka ba a dauki daya daga cikin wannan Matakan Ba Tsarin Ilimin Kasar Nan na Dab Da Karasa Lalacewa .
Yan uwa Dalibai Ku yi liking, comments, da share .
MS Kutama
Students Activist