14/06/2023
SANARWA
Kwalejin nazarin kimiyyar zamani , kirkire kirkire da harokin shugabanci ta Jihar Katsina( Katsina State Institute of Technology and Management) na sanar da daliban da suke neman gurbin karatu na shekarar 2022/2023 a kwasa kwasan Diploma ta kasa (National Diploma) da na Diploma ta kasa akan kirkire kirkire na zamani ( National Innovation Diploma) cewa za' a fara aikin tantance su karo na biyu tun daga ranar Litinin 19 ga wata zuwa Jumu'a 23 ga watan Yunin shekarar 2023.
Ana bukatar daliban dasu zo da takardun su na asali (original credentials) da takardar shaidar biyan kudin sayan fom( payment slip) da kuma katin gaiyata domin zuwa tantancewar (post UTME admission screening invitation card).
Haka kuma wadan da ke da sha'awar karatu a wannan kwaleji har yanzu kofa bude take, za su ziyarci shafin yanar gizo na JAMB domin zabar KSITM a matsayin zabin su na farko (first choice).
Ana shawartar daliban da su tabbatar da sanya dukkanin bayanan sakamakon jarabawar su ta sakandare (O' level results) a shafin su na JAMB.
Sanarwa daga:
Shamsudden Ahmed, MNIM
Mukaddashin Magatakardar kwalejin