21/05/2017
MADUBIN DUBAWA
**************************
Turawan Yamma sun chanza tunanin
Al'ummah. Sun dauki mace
amatsayin Wata "Na'ura" wacce aka
halicceta kawai domin Jima'i! (S*X
DEVICE).
Su kuma matan sun yarda da hakan,
Kuma wannan tunanin yayi tasiri
sosai azukatansu. Shi yasa kowanne
lokaci Mafi yawan Qokarinsu ko
yunkurinsu duk akan Harkar Jima'in
ne. ko dai don suja hankalin namiji,
ko kuma don Namiji yaji da'din
saduwa dasu, Ko kuma yadda zasu
asirce Namiji su mallake zuciyarsa.
Idan sun hadu da junansu sun
kebance agidajen Biki ko wuraren
ayyuka, Ko gidajen gaisuwa, duk dai
zancen kenan. Daga gulma sai
wannan.
A kafafen sadarwa kuwa, wasu har
groups suke Qirkira ko shafuka a
facebook ko Whatsapp don koyar da
jima'i ko sayar da Maganin Mata
domin jima'i!
Har da wasu Qarti samari wadanda
ko auren fari basuyi ba, wai su zasu
koya ma matan aure yadda ake
jima'i!. Su kuma Matan suna kwashe
sirrin Mazajensu suna gaya ma
Qartin (SUBHANALLAH).
Wannan shi ake kira "WANKIN
KWAKWALWA". Domin kuwa a
addinin Musulunci Mata su aka fi
sani da kunya, tausayi, Ladabi, da
kuma biyayyar Allah da biyayyar
Mazajensu.
Amma ayanzu an wanke musu
wancan Kyakkyawan tunanin neman
yardar Allah da yardar Mazajensu.
An chusa musu tsananin son shagala
da burgewa da neman biyar bukatar
sha'awa ta kowanne hali.
Acikin Matayen Farko an samu irin
su Nana Khadijah, Nana Fatimah,
Nana A'ishah, Nana Hafsah, Nana
Juwairiyyah, Nana Ummu Salamah,
Ummu Waraqah, Ummu Kulsum,
Ummu Sulaym, Ummu Hiram da
sauransu (Allah shi yarda dasu).
Daga bayansu an samu Manyan
Waliyyai acikin Mata irin su Sayyidah
Nafeesah, Fatimah Bintul Husayn,
Rabi'atul Adawiyyah, Zubaidah, da
sauransu.
Maimakon Matan zamanin nan su
nemi sanin tarihin wadannan domin
suyi koyi dasu, A'a kullum sunfi son
karanta Labaran Batsa, Maganin
Mallakar Miji, ko kuma Gulmace-
Gulmace..
Sun dena kokarin gyaran zukatansu
sai dai gyaran Jiki. Basu damu da
neman yardar Allah da Manzonsa
(saww) ba, Sai dai neman yardar
Mazaje... Ko ba Mazajen aurensu ba.
Idan kaga Matar aure ta cha'ba ado
ta fesa turare mai Qarfi, ta sanya
Atampa mai tsada to gidan Biki zata
je. Ko kuma wurin aiki, Ko Jami'ah
(University).
Su turawan da kuke koyi dasu, yanzu
acikinsu 'Ya'yan Zina sunfi 'Ya'yan
aure yawa.. Matan auren dake harkar
Kwartanci da wasu Mazajen sunfi
yawa fiye da wadanda basu yi.. A
kasashen Turai.. To menene abin
sha'awa acikin irin wannan rayuwar?.
Wannan kira ne daga Zauren Fiqhu,
domin mu gyara mu gudu tare mu
tsira tare..
*GYARA KAYANKA BAI ZAMA SAUKE
MU RABA BA...*
ALLAH KA SHIRYAR DAMU .