GSS Sumaila. Class of 2004

GSS Sumaila. Class of 2004 Munkirkiri wanna gidane don sada zumunci ga tsofaffin dalibai na GSSS Sumaila Kano state.

02/11/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Kabir Magaji, Musa Aliyu Magajin

12/07/2019

The family of
Alh.Ibrahim Sabo Csp (rtd)
Sardauna gumli
And
Alh.Adamu Y.Haruna CSC
Cordially invite
------------------------------------------
to the
Wedding fatiha
Of their children
Shafi'u ibrahim sabo gumli
(Majidadi sardauna)
&
Karimatu Adamu Haruna
Which will take place as follows:
Date:saturday 03/08/2019
Time: 2:00pm
Venue: Inkil juma'a masjid along gombe road Bauchi state
RSVP08060016809,07069012749,08085996031,08143720860,08148630802

16/04/2019

A yayin da arewacin Najeriya ke fama da kalubale daban-daban da s**a hada da na tsaro, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tattalin arziki, Legit.ng tayi waiwaye domin kawo maku kalaman fasihin mawaki, Marigayi Sa'adu Zungur, a cikin daya daga cikin waken sa mai taken: 'Arewa Jamhuriyya Ko Mulukiyya? ".(1914-- 1958):
Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?
“Matukar a arewa da karuwai,
‘Yan daudu da su da Magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar ’ya’yan mu suna bara,
T**i da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai taryonsu da dukiya.
Babu shakka’ yan kudu za su hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
In ko ’yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,
Malaman karya ’yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai za ta yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
Ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
Ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.

14/02/2019

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci 'yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Omar, wacce Musulma ce 'yar asalin kasar Somaliya, da ta yi murabus bayan da ta wallafa wasu sakonni a shafinta na Twitter.
Sakonnin da ta wallafa dai na zargin cewa 'yan majalisar dokokin Amurkan na goyon bayan Isra'ila ne kawai saboda kamun kafa da kudi.
Shugaba Trump ya bayyana cewa ''ko dai ta yi murabus a matsayinta na 'yar majalisa ko kuma ta fita daga kwamitin majalisar a kan harkokin kasashen waje.''
'Yar majalisar mai wakiltar jihar Minnesota ita ce 'yar Somaliya ta farko da aka fara zaba a majalisar.
Misis Omar dai ta ba da hakuri bayan ta sha s**a daga mutane daban-daban a kan wannan lamari.
'Yan jam'iyyar Democrat da kuma Republican a kasar sun bayyana cewa sakonnin da ta aika a shafin Twitter ya jawo ce-ce-ku-cen kan batun kin jinin Yahudawa.
Shugaba Trump ya bayyana kalaman da Misis Omar ta yi na ba da hakuri a matsayin kalamai marasa gamsarwa.

14/02/2019

Rarraba
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna, ta koka da k**a wasu manyan jam'iyyar da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi saboda wasu kalamai da s**a yi da ake zargin za su iya ta da fitina a ranar zabe.
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna, Mr. Felix Hassan Hyat, ya fadawa taron manema labarai cewa, an k**a jigajigan jam’iyyar a jihar tare da hadin bakin jam’iyya mai mulki ta APC, inda aka tafi da su Abuja.
Ya kuma kara da cewa suna zargin za’ayi amfani da sojoji da kuma 'yan kato da gora domin a haddasa rigima saboda mutane su ji tsoro, yana mai cewa, wadannan ba hanyoyin dimocradiyya ba ne.
Amma a nata bangaren jam’iyya mai mulki ta APC a jihar, ta mayar da martani ta hannun mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar APC, Alhaji Salisu Tanko Solo, wanda ya ce, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya kasa fadawa jama’a dalilin da ya sa aka k**a su.
Inda ya kara da cewa ko shi ya yi irin wadannan kalaman batanci to yana gayyatar jami’an tsaro su k**a shi, saboda kalaman da su ka yi hankali ba zai dauka ba.

Batun yatsan da mutane ya k**ata su yi amfani da shi domin dangwala kuri'arsu a lokacin zabe na neman ya kawo rudani a N...
14/02/2019

Batun yatsan da mutane ya k**ata su yi amfani da shi domin dangwala kuri'arsu a lokacin zabe na neman ya kawo rudani a Najeriya.
Wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta musamman WhatsApp ya bayyana cewa hukumar zabe ta canza tsarin yadda mutane za su jefa kuri'a.
Cikin bayanin da ake yada wa har da yatsan da hukumar ta ce za a yi amfani da shi.
Amma Hukumar INEC ta karyata labarin inda ta ce masu zabe za su iya amfani da kowane yatsa yayin dangwala kuri'arsu.
A wani bayani da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar zabe ta bayyana cewa masu zabe za su iya amfani da kowane irin yatsa su dangwala kuri'arsu.
"Mai kada kuri'a zai iya amfani da kowanne yatsa domin kada kuri'arsa. Amma ya tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam'iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam'iyyar daban," in ji INEC.

14/02/2019

Allah kasa ayi xabennan lafiya k bamu shugabanni nagari .amin

25/11/2018

YABON MACEN KIRKI
Mai irin wannan halin...
Shin ko ka samu dacewa da cikakkiyar mace ta kirki ?!
MISALINTA
Itace wadda MIJINTA yakan amince da ita, ba kuma hakan ne zai zame ma ta yin hasara ba.
Takan yi masa alheri ba mugunta ba, a duk halin da ya samu kansa.
Takan yi asubanci ta shirya wa mijinta abinci, ta kuma shirya wa ƴan matan gidanta aike-aiken da za su yi. Takan lura da gona sosai kafin ta saya, da ribar da ta ci ne, sai take dasa gonar biyayya ga mijinta (wato lura da duk abinda mijinta ke da bukata shine uzurinta), takan himmantu don ta yi aiki tukuru. Ba ta jin tsoron lokacin sanyi...gama ƴaƴanta duka suna da tufafi masu kauri. Mijinta sananne ne har a dandali, yayin da yake zaune tare da dattawan garin...ma'ana dai (Mutumin kirki abin ƙauna ga mutane).
Wadata da mutunci su ne suturarta, (hali nagari kenan).
Tana magana da HIKIMA kuma koyarwarta ta ALHERI ce.
Tana lura da al'amuran ƴaƴanta da kyau, ba ruwanta da ƙyuya ko lalaci. Ƴa'ƴanta s**an tashi su gode mata, MIJINTA kuma yana yabonta. Zai ce mata, "Mata da yawa sun yi abin yabo, amma ke kin fi su duka."
Hanyar sharri da taɓewa (Bin bokaye) duk shirme ne. Amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo. A yi mata cikakken yabo saboda ayyukanta, za a yabi ayyukanta har ma a dandali.
NASIHA CE...!!!

02/11/2018

Yau laffuzan sai a hankali..,
Suna da nauyi marar misali..,
Kwatanta su da buhun kwalli..,
Wasu Shugabannin ba hankali..,
In suna da Ilmi kirashi da kalili..,
Sun sace kudin mu na Baitulmali..,
Sannan ga RASHAWA Kiri-kiri a fili..,
Ta dalilin sanya mu cikin wani hali..!
Hmm.. Bari kuji rashin hankali..,
Da EFCC ta kira su gaban Alkali..,
Ace a yi masu Shari'a Alal a Kalli..,
Akarbi HARAM din a barsu da halali..,
Ah ah! gwara a kiyama mu gansu a fili..,
A gaban mu Allah yayi masu tonon silili..,
A takaice dai anan sun fi jin tsoron Alkali..,
A Maimakon ALLAH wanda ya Halicci Alkali..!
TIR! Da Shugaba mai kwakwalwar DANKALI..!
ALLAH ka canza mana Shi da mai HANKALI..!
Aammmeenn Thumma Aammeenn.

27/09/2018

Mutum mai nawa (saiɗi ko marar kuzari) ba ya iya himma don cimma nasara akan lokaci.
Mai himma kuwa da ya samu...sai a maimaiye shi da ƙyashi ko nuna hasada.
Halin Ɗan'Adam kenan.
NASIHA CE...!!!

31/07/2018

30/07/2018
GATAN MULKI DA MAI MULKIN DUK LOKACI NE
Dadin mulki ne yake saka wasu daga cikin
shugabanni masu mum munan xuciya mantawa da lokaci.
Saboda jin iko da kuma samun 'daukaka da isa da Allah ya Ara masa.
Duk abinda zai mantar da mai mulki yin tunani da
kuma kulawa akan muhimmancin lokaci, to,
wannan mutum kawai kana masa kallon mai
biyayyane shi akan abu mai rudi (Duniya)!
Bari na tunatar da kai mana.
Mai yiwuwa kasan da haka.Idan kuma baka
sani ba, to, yau kasan da haka din.
Wato ita kujerar mulki daka gantan nan, ai ba
mai mallakinta na din-din-din, muddin kuwa akwai mai ita, to, bai wuce LOKACI ba. Saboda
haka, duk wadda ka ga yazo gareta har ya zauna,
to, shima lokaci ne ya kawo shi kanta.Sa'an
nan kuma; shine kuma dai zai sake raba shi da
ita din.
Domin haka yasa ta kasance a waje guda take
zaune a koda wanne lokaci. Sai dai kai din ka je
gareta, har ka samu daman hawanta.Da ka
samu ka zauna kuma sai ka manta da cewa;
Kafin kai din ka zo, ai wasu ne da dama s**a
tashi a kanta.
Saboda haka, ina so ka sani cewa; ita...
kujerar mulki k**ar kujerar aski ta ke.
Idan ka zauna, kai ma din za ka tashi wani ma
ya hau.
NASIHA CE...!!!

Address

Sumaila Postal Codes Interstate. This Local Government Area Is Located In Kano State, North West Geopolitical Zone Of Nigeria. For More Details On The List . .
Sumaila
712102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GSS Sumaila. Class of 2004 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share