12/06/2019
WANE NE HASSAN TEHRANI?
-Gudummawarsa Ga Gwagwarmaya
Daga Nura Kurma Kano
Kwanaki ne dai aka jiyo Kwamandan dakarun kare juyin Musulunci na Iran (IRGC), Janar Hussain Salami yana yiwa Amurka shaguben cewa, duk jiragen yaqin ruwan da ta jibge a tekunan dake gabas ta tsakiya, Iran zata iya raga raga da su.
A cewar sa, tun shekaru sha biyu da s**a wuce, Jamhuriyar Musuluncin ta gama tanadar makaman da zasu iya nutsar da jiragen yaqin Amurkan, sakamakon abinda Janar Hasan Tehrani ya qera.
mutane da yawa sun ji sunan Birgediya Janar Shaheed Hasan Tehrani, amma basu San shi ba, ballantana su san wace rawa ya taka wajen bada gudummawar sa ga kare wannan juyin.
Shi dai Hasan Tehrani, sunansa ya fara fitowa fili ne ko a cikin Iran lokacin da Imam Khomeini (Q.S) ya nada shi shugaban wata tawaga da marigayi Hafez Assad ya nemi Iran ta tura Syria domin samun horon yadda ake qera Mizayil lokacin yaqin da Saddam Hussein al Tikrity da goyon bayan qasashe sama da 40 s**a afkawa Jamhuriyar Musuluncin da shi. Duk duniya Syria ce kadai ta goyi bayan Iran.
Wannan tawaga ta je Syria, kuma ta dawo gida da fasahar qera Mizayil wanda a lokacin Janar Hasan ya duqufa wajen aikin. Kuma cikin qanqanin lokaci labari ya canja, domin sai ga Iran na iya jefa mizayil har cikin Iraqi su ma,
Lokacin da kisan da ake yiwa Musulmin Bosniya ya tsananta, Janar Hasan Tehrani yana cikin tawagar da IRGC s**a tura domin horar da Musulmin Bosniya yadda zasu kare kansu daga kisan kiyashin da duniya ta zura ido ake yi musu.
Tawagar, wadda ta hada da Janar Qassem Sulaimani, Janar Hasan Shateri da Shaheed Imad Mughniyah, har yau dinnan masana harkar leqen asiri na duniya, suna cike da al'ajabin yadda ta iya shiga Bosniya da Hercegovina duk kuwa da yadda Amurka da qawayenta s**a dauki matakin ganin cewa wani taimakon kare kai bai isa ga Musulmin Bosniya ba.
YADDA HASAN TEHRANI YA QERA MAKAMAN DA S**A GAGARI DUNIYA GABA DAYA.
S-300, wani makami ne na tsaron sararin samaniya, wanda Rasha ta qera shi. Kuma kusan ita kadai ce take da tsaron samaniya irin sa, tana matuqar kishin wata qasa ta san sirrin yanda ake qera shi. makamin yafi duk wani tsaron samaniya da sauran qasashen s**a mallaka a wancan lokacin.
Wata rana, Janar Tehrani ya kai ziyara zuwa Moscow, ziyara ce ta aiki. suna cikin tattaunawa da jamian tsaron Rasha, sai Janar din yace musu, da zaku bamu zanen yadda kuka qera S-300 da muma mun je mun yi reverse engineering din sa, mun qera namu. A lokacin Iran ta biya Rasha kudin siyan S-300 din, amma matsin lamba daga Amurka da Isra'ila ya hana ta bata makamin. shi ne ya nemi su bashi blueprint din makamin shi ya koma ya qera.
Ance jamian tsaron Rashan sai s**a yi masa dariya, kuma s**a nuna masa cewa, ai lallai ba zai taba iya qera S-300 ko irin sa ba ko sun bashi blueprint din.
Lokacin da ya dawo daga Rasha, abin ya dame shi matuqa, sai yayi shiri ya tafi Mashhad, ziyarar Halattaccen Halifan Manzo na 8, Imam Ali Al Ridha A.S.
Lokacin da yaje, yayi adduar samun taimakon Allah akan yadda zai qera makamin da yayi daidai da S-300.
A take a wajen Allah Ya kimsa masa yadda zai yi. Yana dawo wa gida ya samu takarda ya dinga rubuta abubuwan da ya gani a cikin ilhamin da Allah Azza wa Jalla Yayi masa a hurumin Imam din.
Wannan ya haifar da qera wasu Mizayaloli kala-kala masu ban al'ajabi.
Tun daga kan tsaron sararin samaniya wanda ya fi S-300 nesa ba kusa ba, har zuwa kan wasu makamai masu tarwatsa jiragen ruwan yaqi, wadanda ita kanta Amurkar ta kasa qera wani makami da zai iya kare jiragen yaqin ta daga gare su, samar da fasahar harba tauraron dan adam sararin samaniya, da kuma fasahar jirage marasa matuqi duk daga ilhamin da Janar Hasan Tehrani ya samu ne.
Malamqn kimiyya suna yi masa laqabi da Baban makamai masu linzami na Iran, wannan kuwa ba qarin gishiri ba ne, domin shi ya fara tsara wa Jamhuriyar Musulunci shirin ta na makamai masu linzami, Ilhamin da ya samu, shi ya mai da Iran gagarabadau a harkar Aerospace gaba daya a yau a duniya.
Yadda Iran ke cafke jirage marasa matuqi da Amurka ke taqama babu mai iya ko ganin su idan s**a tashi sama, da yadda makaman da Iran ta qera suke fin qarfin tsarin tsaron da Amurka take taqama da shi na Patriots defense system, ko David sling, wanda haramtacciyar qasar Isra'ila ke taqama da shi, babban misali ne akan hakan.
Wannan shi ne Hasan Tehrani a taqice.
-DAGA NURA KURMA KANO