08/30/2022
RABON MOTOCIN RARARA A KATSINA YA BAR BAYA DA KURA DA TSINE-TSINE DA TONE-TONE
Daga Shuaibu Abdullahi
Mawaki Dauda Kahutu Rarara, ya shirya gangamin bayar da kyaututukan Motoci ga jaruman da s**a yi nasara a gasar wakar jagaba shine gaba Allah shine gaba.
To sai dai bayan kammala taron an hangi wata matashiyar budurwa tana yin wasu yan tsine-tsine da tone-tone kan rabon kyaututukan gasar a Kano.
Tana Mai kafa hujja da cewar an gwamutsa su a daki daya ko wane daki mutane shida, a cewar ta ita ma tana bayar da kyautar Nera dubu 100.
Tace Allah sai ya Saka musu a kan jagororin gasar baza ta taba yafewa ba, tace ga Bidiyon Sani Indomi gana Kamal Aboki ga na Raliya Yar'sarki ga Bidiyon data yi ita kanta ga Bidiyon Pato dana Lafazzi, wallahi an cuce mu baza mu taba yafewa ba; inji ta
DIMOKURADIYYA